Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 10/15 pp. 5-7
  • Bari Mu Yi Farin Ciki Tare!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bari Mu Yi Farin Ciki Tare!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Farin Ciki da ’Yan’uwa Masu Bi
  • Ku Yi Murna Tare da Waɗanda Suke Fuskantar Gwaje-Gwaje
  • Ka Riƙe Farin Cikinka Cikin Hidimar Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Yi Farin Ciki Tare Da Allah Mai Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 10/15 pp. 5-7

Bari Mu Yi Farin Ciki Tare!

YANA daɗa wuya a yi farin ciki da kuma murna. Yana wa mutane da yawa wuya su yi tunanin abubuwa masu kyau da za su gaya wa wasu. A wasu lokatai, rayuwa a manyan birane tana sa mutane su kaɗaita kuma su yi tunani cewa ba sa son su kasance tare da mutane.

Farfesa Alberto Oliverio ya ce “mutane suna kaɗaitawa a ko’ina a yau kuma rayuwa a manyan birane tana iya sa wasu su ji sun kaɗaita. A yanayi da yawa, zai sa ba za mu damu da abokan aikinmu da maƙwabtanmu ko kuma waɗanda suke aiki a kantuna inda muke sayayya ba.” Sau da yawa irin wannan kaɗaitawa tana sa baƙin ciki.

Amma yanayi da kuma halin ’yan’uwanmu sun yi dabam. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi murna kullum.” (1 Tas. 5:16) Da akwai dalilai da yawa da za su sa mu yi murna da kuma farin ciki tare. Muna bauta wa Jehobah Maɗaukaki Duka, kuma mun fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki. Muna da begen samun ceto da kuma yin rayuwa har abada, kuma za mu iya taimaka wa mutane su samu wannan albarkar.—Zab. 106:4, 5; Irm. 15:16; Rom. 12:12.

Kiristoci na gaskiya suna murna da farin ciki tare da juna. Shi ya sa Bulus ya rubuta wasiƙa ga Filibiyawa: “Na yi murna na yi farinciki kuma tare da ku duka: haka nan ku kuma sai ku yi murna, ku yi farinciki kuwa tare da ni.” (Filib. 2:17, 18) A nan, cikin ayoyi biyu kaɗai, Bulus ya yi magana game da yin murna da farin ciki da juna sau biyu.

Kiristoci suna bukatar su mai da hankali don kada su ware kansu. Duk wanda ya ware kansa daga ’yan’uwansa ba zai yi farin ciki da su a cikin ikilisiya ba. Saboda haka, ta yaya za mu iya bin gargaɗin Bulus na mu “yi farin ciki cikin Ubangiji” tare da ’yan’uwanmu?—Filib. 3:1.

Ka Yi Farin Ciki da ’Yan’uwa Masu Bi

Wataƙila Bulus yana cikin kurkuku a Roma domin ayyukansa na wa’azi, sa’ad da ya rubuta wasiƙarsa ga Filibiyawa. (Filib. 1:7; 4:22) Duk da haka, saka shi a kurkuku bai rage ƙwazonsa a hidima ba. Akasin haka, ya yi farin ciki cewa yana bauta wa Jehobah iya gwargwadonsa kuma ‘ana tsiyaye shi bisa hadaya.’ (Filib. 2:17) Halin Bulus ya nuna cewa farin cikinmu bai dangana ga yanayinmu ba. Ko da yana cikin kurkuku, ya ce: “Zan yi murna kuma.”—Filib. 1:18.

Bulus ya kafa ikilisiya a Filibi, saboda haka, yana ƙaunar ’yan’uwa da ke wajen sosai. Ya san cewa zai ƙarfafa su ta wajen gaya musu game da farin cikin da ya yi don bauta wa Jehobah. Shi ya sa ya rubuta: “Ina so ku sani, ’yan’uwa, al’amuran da suka same ni, sun dai kasance ga yaɗuwar bishara: har sarƙoƙina suka zama bayanannu cikin Kristi ga matsara na Firatariyum duka, har ga saura duka kuma.” (Filib. 1:12, 13) Filibiyawa sun ƙarfafa sa’ad da Bulus ya gaya musu wannan labarin, da hakan ya yi farin ciki da ’yan’uwansa a Filibi, su kuma sun yi farin ciki tare da shi. Amma, ta yin hakan, ba sa bukatar su yi sanyin gwiwa don abin da Bulus yake fuskanta. Maimakon haka, suna bukatar su yi koyi da misalinsa. (Filib. 1:14; 3:17) Bugu da ƙari, Filibiyawa za su iya ci gaba da ambata Bulus cikin addu’o’insu da kuma taimaka da tallafa masa iya gwargwadonsu.—Filib. 1:19; 4:14-16.

Shin muna da halin yin murna kamar na Bulus? Shin muna iya yin tunanin abubuwa masu kyau da muka shaida a rayuwarmu da kuma hidimarmu ta Kirista? Sa’ad da muke cuɗanya da ’yan’uwanmu, yana da kyau mu yi murna game da aikin hidima. Ba za mu jira har sai mun samu labari na musamman kafin mu yi hakan ba. Alal misali, wataƙila wani ya saurari saƙon Mulki domin gabatarwa mai kyau da muka yi amfani da shi ko kuma domin yadda muka tattauna da shi. Mai yiwuwa mun tattauna wata ayar Littafi Mai Tsarki da wani. Ko wataƙila sa’ad da muke hidima, mutane sun san mu a matsayin Shaidun Jehobah kuma hakan shaida ce mai kyau a gare su. Gaya wa ’yan’uwa irin waɗannan labarai, hanya ce na yin farin ciki tare.

Mutanen Jehobah da yawa sun yi sadaukarwa don su yi aikin wa’azi kuma har ila suna hakan. Majagaba da masu kula masu ziyara da waɗanda suke hidima a Bethel da masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma bayi masu-hidima na ƙasashen waje suna farin ciki yayin da suke ci gaba da aiki tuƙuru a hidimarsu ta cikakken lokaci. Shin muna murna da kuma farin ciki tare da su? Bari mu nuna godiya ga waɗannan ƙaunatattun ‘abokan aiki zuwa mulkin Allah.’ (Kol. 4:11) Muna yin hakan ta wajen ƙarfafa su sa’ad da muke tare a tarurrukan ikilisiya ko kuma manyan tarurruka. Muna iya yin koyi da misalinsu na kasancewa da ƙwazo. Muna iya neman “zarafi” mu saurari labaransu da kalami na ƙarfafa ta wajen yi musu karimci, wataƙila cin abinci tare da su.—Filib. 4:10.

Ku Yi Murna Tare da Waɗanda Suke Fuskantar Gwaje-Gwaje

Jimre tsanantawa da kuma sha kan gwaje-gwaje sun ƙarfafa ƙudurin Bulus na kasancewa da aminci ga Jehobah. (Kol. 1:24; Yaƙ. 1:2, 3) Da yake ya sani cewa ’yan’uwa da suke Filibi ma za su fuskanci irin waɗannan gwaje-gwaje kuma za su samu ƙarfafa ta wajen nacewarsa ya sa shi yin murna da farin ciki tare da su. Saboda haka, ya rubuta: “A gare ku an bayar sabili da Kristi, ba bada gaskiya gare shi kaɗai ba, amma shan wahala kuma dominsa: kuna da wannan yaƙi wanda kuka gani a cikina, kuna kuwa ji yanzu yana gare ni.”—Filib. 1:29, 30.

Hakan yake a yau, ana yi wa Kiristoci hamayya don shaida da suke bayarwa. A wasu lokaci wannan hamayyar ta mugunta ce, amma sau da yawa mai wuyan ganewa ne. Zai iya kasance zargin ƙarya daga ’yan ridda, ƙiyayya na waɗanda suke cikin iyalinmu, ko kuwa abokan aikinmu ko abokan makaranta sun yi mana ba’a. Yesu ya ba da kashedi cewa bai kamata waɗannan gwaje-gwaje su sa mu mamaki ko sanyin gwiwa ba. Maimako, za su sa mu farin ciki. Ya ce: “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farinciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama.”—Mat. 5:11, 12.

Ba za mu ji tsoro ba sa’ad da muka ji cewa ana tsananta wa ’yan’uwanmu a wasu ƙasashe sosai. Akasin haka, ya kamata mu yi farin ciki don nacewarsu. Za mu iya yi musu addu’a muna roƙan Jehobah ya taimake su su kasance da bangaskiya mai ƙarfi kuma su jimre. (Filib. 1:3, 4) Wataƙila ta hakan ne kaɗai za mu iya taimaka wa waɗannan ’yan’uwan, amma za mu iya taimakon waɗanda suke cikin ikilisiyarmu da suke fuskantar gwaje-gwaje. Za mu iya nuna mun damu da su kuma mu tallafa musu. Za mu iya neman zarafi mu yi farin ciki tare da su ta wurin gayyatarsu jifa jifa don mu yi Bauta ta Iyali da yamma tare, ta wurin fita hidima tare da kuma yin nishaɗi tare.

Muna da dalilai da yawa na yin farin ciki tare! Bari mu ƙi halin wannan duniyar na ware kai kuma mu ci gaba da yin farin ciki tare da ’yan’uwanmu. Ta yin hakan, za mu sa ikilisiyar ta kasance da ƙauna da haɗin kai kuma za mu more ’yan’uwanci na Kirista sosai. (Filib. 2:1, 2) Hakika, bari mu “yi farinciki cikin Ubangiji kullayaumi” gama Bulus ya aririce mu: “Sai in sake cewa, Ku yi farinciki.”—Filib. 4:4.

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 6]

Kwallon duniya: Courtesy of Replogle Globes

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba