Abin Da Ke Ciki
15 Ga Oktoba, 2011
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA MAKONNIN:
28 ga Nuwamba, 2011–4 ga Disamba, 2011
Nishaɗin da Kake Yi Yana Amfane Ka Kuwa?
SHAFI NA 8
WAƘOƘI: 70, 74
5-11 ga Disamba, 2011
Shawara Mai Kyau Game da Kasancewa Marar Aure da Kuma Mai Aure
SHAFI NA 13
WAƘOƘI: 85, 36
12-18 ga Disamba, 2011
Ka Dogara ga Jehobah, “Allah na Dukan Ta’aziyya”
SHAFI NA 23
WAƘOƘI: 75, 115
19-25 ga Disamba, 2011
Ka “Yi wa Dukan Masu-Makoki Ta’aziyya”
SHAFI NA 27
WAƘOƘI: 68, 42
Manufar Talifofin Nazari
TALIFIN NAZARI NA 1 SHAFUFFUKA NA 8-12
Ko da a ina ne muke da zama, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu zaɓi nishaɗi mai kyau. Wannan talifin zai tattauna yadda za mu iya zaɓan nishaɗi mai kyau.
TALIFIN NAZARI NA 2 SHAFUFFUKA NA 13-17
Zaɓin da mutum ya yi game da ko zai kasance marar aure ko kuma zai yi aure yana shafan rayuwarsa baki ɗaya da kuma dangantakarsa da Jehobah. Wannan talifin zai nuna yadda shawarar da ke 1 Korintiyawa sura ta 7 za ta iya amfane bayin Allah da ba su yi aure ba da kuma ma’aurata a wannan sashe mafi muhimmanci na rayuwa.
TALIFOFIN NAZARI NA 3, 4 SHAFUFFUKA NA 23-31
Bayin Jehobah da kuma wasu mutane suna fuskantar mawuyacin yanayi a wannan kwanaki na ƙarshe. Mene ne wasu cikin waɗannan yanayin? A ina ne za mu iya samun ƙarfafa da muke bukata? Waɗannan talifofi biyu sun nuna yadda Jehobah da kuma Shaidunsa suke ƙarfafa mutane a waɗannan mawuyacin lokatai.
A FITOWAR NAN
3 Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Mu ‘Yi Tsaro’?
18 Bauta wa Jehobah ne Yake Sa Ni Farin Ciki
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 2]
Kwallon duniya: Courtesy of Replogle Globes