“Ku Yi Tsere Domin Ku Samu”
“Ku yi tsere, domin ku samu.”—1 KOR. 9:24.
1, 2. (a) Mene ne Bulus ya yi amfani da shi don ya ƙarfafa Kiristoci Ibraniyawa? (b) Mene ne aka ƙarfafa bayin Allah su yi?
MANZO Bulus ya yi amfani da kwatanci na yin tsere don ya ƙarfafa Kiristoci Ibraniyawa. A cikin wasiƙar da ya rubuta musu, ya ce suna kama da masu gudu a tsere. Amma ya tuna musu cewa suna yin wannan tseren tare da wasu. Da akwai ‘taron shaidu mai girma’ da sun riga sun gama tseren. Idan Kiristoci Ibraniyawa suna tuna da ayyuka na bangaskiya da ƙoƙarce-ƙoƙarce na waɗannan amintattu, za su ƙuduri aniya su gama tseren.
2 A talifin da ya gabata, mun yi magana game da tafarkin rayuwa na mutane da yawa cikin “taron shaidu.” Dukansu sun kasance da bangaskiya sosai ga Allah har ƙarshen rayuwarsu. Ta yaya mu ma za mu iya gama tseren, yadda suka yi? Bulus ya ce: “Bari mu tuɓe kowane abin nauwaitawa, da zunubin da ke manne mamu, tare da haƙuri kuma mu yi tseren da an sa gabanmu.”—Ibran. 12:1.
3. Mene ne Kiristoci za su iya koya daga abin da Bulus ya faɗa game da masu tsere a wasannin Hellanawa?
3 Littafin da ya yi magana game da Kiristoci a zamanin Bulus ya bayyana yadda masu tsere a zamaninsa suke yin gudu. (Backgrounds of Early Christianity) Ya ce: Hellanawa suna tsirara sa’ad da suke motsa jiki da kuma yin gasa.”a Yin tsere hakan ba zai yi daidai a yau ba. Amma masu tsere suna gudu ba tare da saka tufafi ba domin ba sa son kome ya hana su cin ladar. Saboda haka, sa’ad da Bulus ya gaya wa Kiristoci Ibraniyawa su tuɓe kowane abin nauwaitawa yana nufin cewa su yi ƙoƙari su kawar da kome da zai hana su cin ladar rai madawwami. Wannan shawara mai kyau ce ga Kiristoci a lokacin da kuma mu a yau. Waɗanne abubuwa ne za su iya hana mu samun lada a tsere na rai?
Ku “Tuɓe Kowane Abin Nauwaitawa”
4. Mene ne mutane na zamanin Nuhu suka shagala da yi?
4 Bulus ya ce a “tuɓe kowane abin nauwaitawa.” Wannan abin nauwaitawa ya ƙunshi kome da zai iya hana mu mai da hankali sosai ga tseren da kuma yin iya ƙoƙarinmu don mu gama shi. Waɗanne abubuwa ne za su iya zama abin nauwaitawa? Yesu ya taimaka mana mu fahimci wannan. Ya yi magana game da Nuhu, wanda yake cikin mutane masu bangaskiya da Bulus ya ambata. Yesu ya bayyana: “Kamar yadda ya faru cikin kwanakin Nuhu kuma, hakanan za shi zama a cikin kwanakin Ɗan mutum.” (Luk 17:26) Yesu ba ya magana musamman game da halaka da za a yi; yana magana ne game da yadda mutane suke rayuwa. (Karanta Matta 24:37-39.) Yawancin mutane na zamanin Nuhu ba sa son su koya game da Allah, kuma ba sa son su faranta masa rai. Mene ne suke yi? Suna ci da sha da kuma yin aure, wato abubuwa na yau da kullum. Ainihin matsalar ita ce ‘ba su lura ba,’ in ji Yesu.
5. Mene ne zai taimaka mana mu yi nasara wajen kammala tseren?
5 Kamar Nuhu da iyalinsa, muna da abubuwa da yawa da za mu yi kowacce rana. Muna bukatar mu yi aiki don mu samu kuɗi kuma mu kula da kanmu da iyalinmu. Hakan zai iya cinye lokaci da yawa da kuma kuzarinmu. Kuma idan muna da matsalar kuɗi, muna iya yin alhini game da yadda za mu samu abubuwa da muke bukata. Kuma a matsayin Kiristoci da suka keɓe kansu, muna da wasu hakkoki masu muhimmanci na tsarin Allah. Muna wa’azi da kuma shirya da halartar tarurruka da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da iyalinmu da na kanmu. Duk da abubuwa da yawa da Nuhu zai yi don ya bauta wa Allah, dukan abin da Allah ya ce ya yi “haka ya yi.” (Far. 6:22) Idan muna son mu yi kome da Jehobah ya gaya mana mu yi kuma mu gama tserenmu, yana da muhimmanci sosai kada mu ɗauki abin nauwaitawa da zai sa ya yi mana wuya mu yi tseren har ƙarshe.
6, 7. Wane gargaɗin Yesu ne ya kamata mu tuna da shi?
6 Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce mu “tuɓe kowane abin nauwaitawa”? Hakika, ba za mu iya kawar da dukan hakkokin da muke da su ba daga rayuwarmu domin wasu hakkoki suna da muhimmanci. A wannan batun, ka tuna da kalaman Yesu: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da minene za mu yi sutura? Gama waɗannan abubuwa duka Al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka.” (Mat. 6:31, 32) Yesu ya taimaka mana mu fahimci cewa abubuwa kamar abinci da tufafi suna iya zama abin nauwaitawa idan sun fi kasancewa da muhimmanci a gare mu.
7 Kada ku manta da kalaman Yesu: “Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka.” Hakan yana nufin cewa Ubanmu Jehobah zai kula da bukatunmu. Hakika “waɗannan abubuwa duka” ba sa nufin cewa za mu samu kome da muke so. Har ila, an gaya mana kada mu yi alhini game da “abubuwa duka Al’ummai suna ta biɗa.” Me ya sa? Yesu ya shawarci masu sauraronsa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko.”—Luk 21:34, 35.
8. Me ya sa za mu “tuɓe kowane abin nauwaitawa”?
8 Muna gab da gamawa. Saboda haka ba za mu so mu ƙyale kome ya sa ya yi mana wuya mu gama tseren ba. Shi ya sa za mu kawar da abubuwan nauwaitawa da ba su da muhimmanci kuma mu kasance da wadar zuci ga samun abubuwa da muke bukata. Wannan ne shawarar da manzo Bulus ya ba mu sa’ad da ya gaya mana mu kasance da “ibada tare da wadar zuci.” (1 Tim. 6:6) Tuna da kalaman Bulus zai sa ya fi mana sauƙi mu ci gaba da gudu kuma mu ci ladar.
“Zunubin da ke Manne Mamu”
9, 10. (a) Mene ne furucin nan “zunubin da ke manne mamu,” yake nufi? (b) Mene ne zai iya faru da bangaskiyar wani Kirista?
9 Ban da “abin nauwaitawa,” Bulus ya ambata kawar da “zunubin da ke manne mamu.” Mene ne wannan? Kalmar nan “da ke manne” da aka fassara a Helenanci ta bayyana sau ɗaya kawai a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma a cikin wannan ayar. Wani masanin Littafi Mai Tsarki mai suna Albert Barnes ya ce: “Mai yin tsere a wannan zamanin ba ya saka tufafin da zai riƙe ƙafarsa kuma ya hana shi gudu. Kuma ya ce a wannan hanyar, bai kamata Kirista ya ƙyale kome ya hana shi yin tsere, wato, ya raunana bangaskiyarsa ko kuma ya sa ba zai kasance da bangaskiya ba.” Ta yaya Kirista zai iya rasa bangaskiyarsa?
10 Kirista ba ya rasa amincinsa dare ɗaya kawai. Hakan yana iya faruwa a hankali, wataƙila ba zai ma san cewa bangaskiyarsa tana raunanawa da sannu-sannu ba. A wasiƙarsa ta farko zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa, Bulus ya yi musu gargaɗi a kan haɗarin ‘zakuɗawa’ da kuma kasancewa da ‘muguwar zuciya ta rashin bangaskiya.’ (Ibran. 2:1; 3:12) Idan tufar mai tsere ta kama ƙafarsa, babu shakka zai faɗi. Saboda haka, dole ne mai yin tsere ya gane cewa zai iya faɗuwa idan ya yi gudu da tufar da ba ta dace ba. Mene ne zai iya sa ya yi banza da wannan haɗarin? Wataƙila yana sakaci da yawan gaba gaɗi ko kuma hankalinsa yana a rabe. Mene ne za mu iya koya daga dukan shawarwarin da Bulus ya ba da?
11. Mene ne zai sa mu yi rashin bangaskiyarmu?
11 Ya kamata mu tuna cewa idan Kirista ya yi rashin bangaskiyarsa, hakan ya faru ne domin abubuwan da ya zaɓa ya yi. Wani masani ya yi magana game da “zunubi da ke manne mamu.” Ya bayyana cewa yanayin da muke ciki da mutane da muke tarayya da su da kuma munanan sha’awoyinmu za su iya shafanmu sosai. Waɗannan abubuwa suna iya raunana bangaskiyarmu ko kuma su sa mu yi rashin bangaskiyarmu.—Mat. 13:3-9.
12. Idan ba ma son mu yi rashin bangaskiyarmu, yana da muhimmanci mu yi biyayya ga wane gargaɗi?
12 Sau da yawa, bawan nan mai aminci mai hikima ya yi mana gargaɗi cewa mu mai da hankali wajen zaɓan abin da muke kallo da abin da muke saurarawa domin waɗannan abubuwan suna shafan yadda muke tunani da kuma sha’awoyinmu. An yi mana gargaɗi game da haɗarin son ƙarin kuɗi a ko yaushe da wasu abubuwa. Idan muna son nishaɗin wannan duniya ko kuma son kowane sabon kayayyaki, za mu shagala da waɗannan abubuwa har ba za mu samu lokacin yin abubuwa da suka fi muhimmanci ba. Domin muna ganin cewa an matsa mana ainun, zai kasance da haɗari idan muka ƙi wannan gargaɗin. Kuma bai kamata mu yi tunanin cewa wannan gargaɗin bai shafe mu ba domin muna da bangaskiya mai ƙarfi. Shaiɗan yana amfani da tunani da sha’awoyi na wannan duniyar don ya sa mu yi watsi da wannan gargaɗin. Ba ya son mu yi nasara a tseren. Wasu sun yi rashin bangaskiyarsu domin sun yi sakaci da yawan gaba gaɗi ko kuma abubuwan duniya sun janye hankalinsu. Idan hakan ya faru mana, muna cikin haɗarin rasa ladar samun rai madawwami.—1 Yoh. 2:15-17.
13. Mene ne za mu yi don mu guji yin tunani kamar mutanen duniya?
13 A kowacce rana, muna haɗuwa da mutanen da maƙasudansu da ra’ayoyinsu na duniyar Shaiɗan ne. (Karanta Afisawa 2:1, 2.) Amma muna da zaɓin tsai da shawara a kan ko za mu ƙyale tunanin wannan duniya ya shafe mu. Bulus ya ce tunanin mutanen duniya yana kama da iska mai guba da ke ko’ina. Saboda haka, yadda ba za mu so mu shaƙa iska mai guba ba, ba za mu ƙyale yadda mutane a duniya suke tunani ya shafe mu ba. Mene ne za mu iya yi don mu ci gaba da yin tseren? Yesu ya nuna misali mafi kyau na wanda ya yi tsere har ƙarshe, kuma muna iya yin koyi da shi. (Ibran. 12:2) Bulus ma ya kafa mana misali mai kyau, gama ya yi tseren kuma ya ƙarfafa ’yan’uwansa su yi koyi da shi.—1 Kor. 11:1; Filib. 3:14.
Ta Yaya ‘Za Ku Samu’ Ladar?
14. Yaya gama tseren yake da muhimmanci ga Bulus?
14 Yaya gama tseren yake da muhimmanci ga Bulus? Sa’ad da ya yi wa dattawan da ke Afisa magana a lokaci na ƙarshe, ya ce “Ban maida raina wani abu ba, kamar abin tamani a gareni, bisa ga in cika tafiyata, da hidima kuma wadda na karɓa daga wurin Ubangiji Yesu.” (A. M. 20:24) Bulus yana a shirye ya sadaukar da kome, har da ransa domin ya gama tseren. Bulus ya yi aiki tuƙuru don ya yi wa’azin bishara. Amma ya ce duk wannan ƙoƙarin zai zama banza idan bai gama tseren ba. Ya san ya kamata ya ci gaba da aiki tuƙuru har ƙarshe. Bai yi tunani ba cewa ya riga ya samu ladar. (Karanta Filibiyawa 3:12, 13.) Amma ba da daɗewa ba, kafin ya mutu, ya ce: “Na yi yaƙi mai-kyau, na kure fagen, na kiyaye imani.”—2 Tim. 4:7.
15. Mene ne Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwansa su yi?
15 Ƙari ga hakan, Bulus ya yi ɗoki sosai ’yan’uwansa su gama tseren kuma kada su yi kasala a hanya. Alal misali, ya ƙarfafa Kiristoci da ke Filibi su yi aiki tuƙuru don su samu ceto. Ya tuna musu su riƙe “zancen rai” gamgam. Ya ci gaba: “Domin in sami abin fahariya a cikin ranar Kristi, ban yi tsere banza ba, ban kuwa yi wahala banza ba.” (Filib. 2:16) Hakazalika, ya ƙarfafa Kiristoci da ke Korinti: “Haka nan kuma ku yi tsere, domin ku samu [ladar].”—1 Kor. 9:24.
16. Me ya sa ya kamata ladar ta kasance da gaske a gare mu?
16 Masu tsere ba sa ganin iyakar filin tseren sai sun kusan ƙarasa gudun. Amma a koyaushe, masu tseren suna tunani game da ƙarshen kuma sun san cewa sun kusa. Kuma sa’ad da ya san cewa ƙarshen tseren ya kusa, yana ƙuduri aniya ya gama. Kiristoci suna irin wannan tseren. Ya kamata ladar ta kasance da gaske a gare mu. Hakan zai taimaka mana mu ƙuduri aniya mu gama tseren kuma mu samu ladar.
17. Ta yaya bangaskiya take sa ladar ta kasance da gaske a gare mu?
17 Bulus ya rubuta: “Bangaskiya fa ainihin abin da mu ke begensa ne, tabbacin al’amuran da ba a gani ba tukuna.” (Ibran. 11:1) Ibrahim da Saratu suna shirye su bar daɗin da suke ji a gidansu kuma su zama ‘baƙi da alhazai’ a cikin ƙasar. Mene ne ya taimaka musu? Sun ‘rigaya sun amshi alkawarai na Allah.’ Musa ya ƙi “daɗin nishatsin zunubi domin ’yan kwanaki” da kuma “dukiyar Masar.” Ta yaya ya samu bangaskiya da ƙarfin yin hakan? Yana “sauraron sakamakon.” (Ibran. 11:8-13, 24-26) Bulus ya ce kowane cikin waɗannan mutanen sun aikata “ta wurin bangaskiya.” Bangaskiya ta sa ya yiwu su mai da hankali ba ga gwaje-gwaje da wahalar da suka sha ba amma su saurari abin da Allah yake musu a lokacin da kuma a nan gaba.
18. Mene ne za mu yi don mu guji kasa ƙarasa tseren?
18 Ta wajen yin bimbini a kan maza da mata masu bangaskiya da aka ambata a Ibraniyawa sura 11 da kuma yin koyi da misalinsu, za mu iya kasancewa da bangaskiya kuma mu kawar da “zunubin da ke manne mamu.” (Ibran. 12:1) Kuma za mu “lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka” ta halartar taro da waɗanda suke da bangaskiya irin tasu.—Ibran. 10:24.
19. Me ya sa yake da muhimmanci yanzu mu ci gaba da yin tseren?
19 Mun kusa ƙarasa tserenmu, kuma kamar muna ganin ƙarshen tseren. Da taimakon Jehobah da kuma bangaskiya, mu ma za mu iya “tuɓe kowane abin nauwaitawa, da zunubin da ke manne mamu.” Hakika, za mu iya yin gudu don mu yi nasara, wato, samun albarka da Allah da Ubanmu, Jehobah ya yi mana alkawarinta.
[Hasiya]
a Hakan haramu ne ga Yahudawa na dā. Littafin Makabawa na biyu na afokirifa ya ce, Yahudawa sun yi fushi sa’ad da Yason Babban Firist ɗan ridda yake son ya gina ɗakin motsa jiki irin na Hellanawa a Urushalima.—2 Makabawa 4:7-17.
Ka Tuna?
• Mene ne tuɓe “kowane abin nauwaitawa” ya ƙunsa?
• Mene ne zai iya sa Kirista ya yi rashin bangaskiya?
• Me ya sa za mu mai da hankali ga yin nasara?
[Hoto a shafi na 23]
Mene ne “zunubin da ke manne mamu,” kuma ta yaya hakan zai iya faruwa da mu?