Ina Samun Ƙarfi Da Daɗewa Ta Wajen Karanta Littafi Mai Tsarki
Marceau Leroy ne ya ba da labarin
NA SOMA karanta waɗannan kalmomi a cikin ɗaki na, “A cikin farko Allah ya halicci sama da ƙasa.” Me ya sa na yi karatu a ɓoye? Hakika, mahaifina da bai amince da wanzuwar Allah ba, ba zai yarda na karanta Littafi Mai Tsarki ba.
Ban taɓa karanta Littafi Mai Tsarki ba, kuma waɗannan kalaman farko na littafin Farawa sun taɓa zuciyata sosai. Na yi tunani, ‘Wannan amsa ce ga tambaya game da sararin samaniya da na daɗe ina mamaki a kai!’ Don abin ya burge ni sosai, na yi karatu tun daga ƙarfe takwas na dare zuwa ƙarfe huɗu na asuba. Kuma wannan ne somawa ta na karanta Kalmar Allah da na daɗe ina yi. Bari na bayyana yadda karatun Littafi Mai Tsarki ya zama abin ƙarfafa a rayuwata gabaki ɗaya.
“Za Ka Riƙa Karantawa Kowace Rana”
An haife ni a shekara ta 1926, a Vermelles, ƙauyen da ke arewancin Faransa da ake haƙa kwal. Kwal yana da amfani sosai a ƙasar, a lokacin yaƙin duniya na biyu. Ba a ce na shiga aikin soja ba tun da ina haƙa kwal. Amma don na kyautata rayuwa ta, na soma karatu game da rediyo da kuma lantarki, kuma hakan ya sa na fahimci yadda abubuwa suke tafiya a sararin samaniya. Sa’ad da nake ɗan shekara 21, ɗan ajina ya ba ni Littafi Mai Tsarki da na fara samu, kuma ya ce, “Littafi ne da ya kamata ka karanta.” Bayan na gama karanta shi, na kasance da tabbaci cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce, da ya ba ’yan Adam.
Na sayi Littafi Mai Tsarki guda takwas don ina jin cewa maƙwabta na ma za su ji daɗin karanta shi. Amma na yi mamaki, sa’ad da suka soma yi mini dariya da kuma hamayya. ’Yan’uwa na da suka amince da sihiri sun yi mini gargaɗi cewa, “Da zarar ka soma karanta wannan littafin, za ka riƙa karanta shi kullum!” Amma na karanta shi, kuma ban taɓa nadamar yin hakan ba. Ya zama abin da nake yi kullum.
Sa’ad da wasu maƙwabta na suka ga cewa ina son Littafi Mai Tsarki, sai suka ba ni littattafan da Shaidun Jehobah suka ba su. Ƙasidu kamar One World, One Governmenta (a Faransanci) ya bayyana dalilin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Mulkin Allah ne kaɗai begen ’yan Adam. (Mat. 6:10) Na ƙuduri aniya sosai na sa mutane su kasance da wannan begen.
Wani mutum da ya fara karɓan Littafi Mai Tsarki daga hannuna shi ne wani aboki na tun muna yara mai suna Noël. Tun da yake shi ɗan Katolika ne, ya shirya don mu haɗu da wani mutum da ke nazari don ya zama firist. Abin ya tsorata ni sosai, amma duk da haka na tuna abin da na karanta a littafin Zabura 115:4-8 da Matta 23:9, 10 cewa Allah bai amince da yin amfani da gumaka don bauta masa ba da kuma kiran limamai da manyan sunaye. Hakan ya ba ni gaba gaɗi na kāre sabon imani na. A sakamako, Noël ya karɓi gaskiya, kuma har yau, yana bauta wa Jehobah da aminci.
Na kuma ziyarci yata. Mai gidanta yana da littattafan sihiri kuma aljannu suna damunsa sosai. Ko da yake da farko na ji cewa ban da ƙarfi, amma ayoyi kamar Ibraniyawa 1:14 sun tabbatar da ni cewa mala’ikun Jehobah suna goyon baya na. Sa’ad da suruki na ya yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ya daina yin amfani da kayayyakin sihiri, sai aljannun suka rabu da shi. Da shi da yata suka zama Shaidu masu ƙwazo.
Wani Mashaidi, Ba’amirke, mai suna Arthur Emiot ya ziyarce ni a shekara ta 1947. Cike da farin ciki na tambaye shi inda Shaidu suke taro. Ya gaya mini cewa akwai wani rukuni a garin Liévin, da ke da nisan mil 6. Yana da wuya sosai mutum ya sayi keke a wannan lokacin, saboda da haka, na taka zuwa tarurruka watanni da yawa. An hana aikin Shaidun Jehobah na tsawon shekara takwas a Faransa a lokacin. Akwai Shaidu 2,380 a ƙasar baki ɗaya a lokacin, kuma da yawa cikinsu baƙi ne daga ƙasar Poland. Amma an sake amince da aikinmu a ƙasar Faransa a ranar 1 ga Satumba, 1947. An sake kafa ofishin reshe a Villa Guibert, a birnin Paris. Domin babu ko majagaba na kullum guda a Faransa a lokacin, Hidimarmu Ta Mulki ta Disamba 1947 ta ƙarfafa ’yan’uwa su soma hidimar majagaba na kullum wanda zai bukaci su riƙa ba da sa’o’i 150 a duk wata. (An rage shi zuwa sa’o’i 100 a shekara ta 1949.) Da yake na amince da kalaman Yesu da suke rubuce a littafin Yohanna 17:17, da ta ce “maganarka [Allah] ita ce gaskiya,” na yi baftisma a shekara ta 1948, kuma a watan Disamba ta shekara ta 1949, na zama majagaba na kullum.
Na Koma Garin Dunkerque Bayan Na Fito Daga Kurkuku
Ban daɗe a hidimata ta farko a garin Agen, a kudancin Faransa ba. Domin na daina aikin kwal, aka ce na shiga aikin soja. Amma na ƙi yin hakan, sai aka saka ni a kurkuku. Ko da yake ba a yarda na yi amfani da Littafi Mai Tsarki ba, amma na samu ’yan shafofi na littafin Zabura. Karanta su ya ƙarfafa ni. Bayan an sallame ni, ya kamata na tsai da shawara: Shin na daina hidima ta cikakken lokaci don na samu iyali tawa? Amma abin da na karanta a cikin Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini. Na yi bimbini a kan kalaman da ke Filibiyawa 4:11-13: ‘Zan iya yin abu duka ta wurin wannan da yake ƙarfafani.’ Na tsai da shawara na ci gaba da hidimar majagaba. A shekara ta 1950, an tura ni zuwa sabon yanki, wato, Dunkerque, garin da na taɓa yin hidima a dā.
Ba ni da kome, sa’ad da na isa wurin. An yamutse garin a lokacin Yaƙin Duniya na biyu, kuma yana da wuya a samu masauki. Sai na shawarta na ziyarci wata iyali da nake musu wa’azi a dā, kuma uwar gidan ta yi farin ciki sosai: “Malam Leroy, an sako ka ne? Maigidana ya ce da akwai maza kamar kai da yawa, da ba za a taɓa yin yaƙi ba.” Sai suka ba ni wani ƙaramin ɗakin da ke gidansu har zuwa lokacin da baƙi za su soma zuwa. A ranar, Arthur Emiot’s ɗan’uwan Evans, ya ba ni aiki.b Shi mai fassara ne a tashar jirgin ruwan kuma yana neman wanda zai riƙa yin gadin jirgin. Ya gabatar da ni ga ɗaya cikin ma’aikatan jirgin. Bayan da na fito daga kurkuku, ina kamar kara. Sa’ad da Evans ya bayyana dalilin da ya sa nake hakan, ma’aikacin ya ce na cire abinci daga cikin firiji na ci. Aka ba ni ɗaki da aiki da kuma abinci a ranar! Na daɗa tabbata da kalaman Yesu da ke cikin Matta 6:25-33.
Sa’ad da baƙi masu yawon zagayawa suka soma zuwa, ni da ɗan’uwa Simon Apolinarski wanda muke hidimar majagaba tare da shi muna bukatar neman wani masauki, amma mun ƙudurta mu kasance a hidimarmu. Aka ba mu masauki a wani tsohon ɗakin da ake ajiye dawakai a dā, inda muke kwantawa a kan katifar ciyayi. Muna kasancewa a hidimar fage a koyaushe. Mun yi wa mai gidan dawakan wa’azi, kuma ya zama ɗaya cikin mutane da yawa da suka zama Shaidu. Bai daɗe ba aka wallafa wani talifi a cikin jarida da ya yi gargaɗi cewa mazaunan Dunkerque su “yi hankali da ayyukan Shaidun Jehobah a yankin.” Amma ni da Simon da kuma wasu masu shela ne kaɗai Shaidun da suke wurin! Sa’ad da muke fuskantar mawuyacin yanayi, yin bimbini a kan begenmu na Kirista da kuma yin la’akari da yadda Jehobah ya kula da mu ya ƙarfafa mu. Akwai masu shela guda 30 a Dunkerque sa’ad da aka tura ni wani yanki a shekara ta 1952.
Na Samu Ƙarfafa don Cim ma Sabon Hakkina
Ban daɗe ba a birnin Amiens, sai aka naɗa ni majagaba na musamman kuma aka tura ni zuwa birnin Boulogne-Billancourt, kusa da ƙarshen Paris. Ina da ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa, kuma wasu cikinsu sun yi hidima ta cikakken lokaci da kuma wa’azi a ƙasashen wajen daga baya. Wani matashi mai suna, Guy Mabilat, ya karɓi gaskiya kuma ya yi hidima a matsayin mai kula da da’ira da kuma mai kula da gunduma. Daga baya, ya yi hidima a matsayin mai kula sa’ad da ake gina maɗaba’a da Bethel da ke Louviers, ’yan mil daga Paris. Tattauna Littafi Mai Tsarki kowanne lokaci da mutane a hidima ya daɗa sa Kalmar Allah ta kasance a cikin zuciyata, kuma hakan ya sa ni farin ciki kuma ya sa ya yiwu na kyautata koyarwa ta.
Sai farat ɗaya a shekara ta 1953, aka naɗa ni mai kula da da’ira a yankin Alsace-Lorraine, wani yanki da ƙasar Jamus ta ci sau biyu tsakanin shekara ta 1871 da 1945. Saboda haka, na daɗa koyon yaren Jamus. Sa’ad da na soma hidimar mai kula da da’ira, babu motoci da yawa da talabijin da tafireta a yankin kuma babu rediyo da kwamfuta. Amma duk da haka rayuwata tana da ma’ana. Lokaci ne mai cike da farin ciki sosai. Yin biyayya ga gargaɗin Littafi Mai Tsarki cewa mu ‘sa idonmu ya kasance sarai’ ya fi sauƙi a lokacin tun da muna bauta wa Jehobah ba tare da abin raba hankali ba.—Mat. 6:19-22.
Ba zan taɓa mantawa da Taron “Triumphant Kingdom” [“Mulki Mai Nasara”] wanda aka yi a birnin Paris a shekara ta 1955 ba. A nan ne na haɗu da macen da na aura, mai suna Irène Kolanski, wadda ta soma hidima ta cikakken lokaci shekara guda kafin na soma. Iyayenta ’yan ƙasar Poland sun daɗe suna bauta wa Jehobah. Ɗan’uwa Adolf Weber ya ziyarce su sa’ad da suke ƙasar Faransa. Shi mai aiki a lambun ɗan’uwa Russell ne kuma ya zo ne daga ƙasar Turai don ya yi wa’azi. Na auri Irène a shekara ta 1956, kuma mun ci gaba da hidimar mai kula da da’ira tare. Ta kasance mini abin ƙarfafa tun lokacin!
Na samu wata albishir shekaru biyu bayan wannan lokacin sa’ad da aka naɗa ni mai kula da gunduma. Duk da haka, na ci gaba da kai ziyara wasu ikilisiyoyi tun da yake babu ’yan’uwa masu kula da da’ira da yawa. Wannan lokaci mai cike da ayyuka ne sosai! Ƙari ga yin wa’azi na sa’o’i 100 a wata, ina ba da jawabi duk mako kuma ina ziyarar rukunin nazari guda uku da kuma duba da rubuta rahotanni. Da yake ina da ayyuka da yawa, yaya zan samu lokacin karanta Kalmar Allah? Na samu mafita guda, wato, na cire wasu shafuffuka na tsohon Littafi Mai Tsarki kuma ina ajiye su tare da ni. Duk sa’ad da nake jiran wani, nakan ciro shafuffuka ɗin na karanta. Waɗannan ’yan lokatai na wartsakewa ta ruhaniya ya ƙarfafa ni na ci gaba a aiki na.
An gayyace ni da Irène zuwa Bethel da ke Boulogne-Billancourta a shekara ta 1967 don mu yi hidima a wurin. Na soma hidima a Sashen Kula da Hidima, kuma na ci gaba da hakan cikin shekaru arba’in da suka shige. Sashe mafi daɗi na aiki na shi ne ba da amsoshi ga wasiƙar da aka rubuto na tambayoyin Littafi Mai Tsarki. Ina farin ciki sosai don bincika Kalmar Allah da kuma yin “kāriyar bishara.” (Fib 1:7) Ina kuma farin cikin gudanar da tattaunawar Littafi Mai Tsarki a bautar safiya kafin mu ci abinci. A shekara ta 1976, aka naɗa ni ɗaya cikin Kwamitin Reshe na ƙasar Faransa.
Rayuwa Mafi Kyau
Ko da yake na fuskanci mawuyacin lokatai, amma lokaci mafi ƙalubale a rayuwata ita ce yanzu da tsufa, da ciwo ya rage yawan aikin da ni da matata Irène muke yi. Amma duk da haka, karanta da kuma yin nazarin Kalmar Allah sun sa mu ci gaba da kasancewa da bege. Muna farin cikin shigan bas zuwa yankinmu don yin wa’azi. Labarai na da na matata na shekara 120 da muka yi a hidima ta cikakken lokaci ya motsa mu mu ƙarfafa duk waɗanda suke ɗokin yin rayuwa mai daɗi da kuma farin ciki su yi hidima ta cikakken lokaci. Sa’ad da Sarki Dauda ya rubuta kalaman da ke Zabura 37:25, ya yi “tsufa,” amma kamar shi, ban “taɓa gani an yar da mai-adalci ba.”
Jehobah ya ƙarfafa ni da Kalmarsa a rayuwa ta gabaki ɗaya. Dangi na sun faɗa mini shekaru 60 da suka shige cewa, karatun Littafi Mai Tsarki zai zama hali na na kullum. Kalamansu gaskiya ce. Abu ne da nake yin kullum da ba zan taɓa yi da na sani ba!
[Hasiya]
a An wallafa shi a shekara ta 1944, amma yanzu an daina bugawa.
b Don ƙarin bayani game da Evans Emiot, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 1999, shafuffuka na 22 da 23 na Turanci.
[Hoto a shafi na 5]
Ni da Simon
[Hoto a shafi na 5]
Sa’ad da nake hidimar mai kula da gunduma
[Hoto a shafi na 5]
Littafi Mai Tsarki da ya yi kama da wanda na fara samu
[Hoto a shafi na 6]
Ranar aurenmu
[Hoto a shafi na 6]
Ni da matata Irène muna jin daɗin karanta da kuma yin nazarin Kalmar Allah