Ka Tuna?
Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
• Waɗanne abubuwa uku masu muhimmanci ne za su taimaka mana mu ci gaba da guje wa yin ha’inci?
Su ne: (1) Kasancewa da tsoro don kada mu ɓata wa Allah rai. (1 Bit. 3:12) (2) Kasancewa da lamiri da Littafi Mai Tsarki ya koyar. (3) Yin ƙoƙari don kasance da wadar zuci.—4/15, shafuffuka na 6-7.
• Ta yaya muka san cewa bauta wa Allah da hankali shimfiɗe ba ya nufin cewa ba za mu iya shaƙatawa da kuma kasancewa tare da mutane ba?
Ka yi la’akari da misalin Yesu. Ya more cin abinci tare da mutane. Mun san cewa shi mai fara’a ne. Mutane, har da yara ma sun saki jiki sa’ad da suke tare da shi kuma sun ji daɗin kasancewa tare da shi.—4/15, shafi na 10.
• Mene ne ma’aurata za su iya yi idan dangantakarsu ta soma sanyi bayan sun samu ɗa na fari?
Suna bukatar su sake tabbatar da ƙaunarsu ga juna. Maigida zai iya taimaka wa matarsa ta ji cewa dangantakarsu tana da kāriya. Kuma su biyu suna bukatar su yi ƙoƙari don su riƙa tattaunawa da juna sosai game da yadda suke ji da kuma bukatunsu na zahiri.—7/1, shafuffuka na 30-31.
• Mene ne itacen zaitun na Romawa sura 11 take wakilta?
Itacen zaitun tana wakiltar sashe na farko na zuriyar Ibrahim, wato, Isra’ila ta ruhaniya. Jehobah yana kama da saiwar, Yesu kuma rassa na itacen zaitun na alama. Sa’ad da yawancin Yahudawa suka ƙi Yesu, an shigar da ’Yan Al’ummai da suka zuma masu bi, kuma da hakan, sun zama cikakken adadin sashe na biyu na ’ya’yan Ibrahim.—5/15, shafuffuka na 22-25.
• Wane albishiri ne za mu iya gaya wa talakawa?
Albishirin shi ne: Allah ya naɗa Yesu a matsayin Sarki. Shi ne Sarkin da ya ƙware da zai ƙawar da talauci. Don me? Domin shi ne zai yi sarauta bisa dukan ’yan Adam kuma yana da ikon aikatawa, yana juyayi ga talakawa, kuma zai iya sa talauci ya daina da kuma halin son kai da muka gada.—7/1, shafi na 7.
• Zai yiwu ’ya’yan da ya kamata Yesu kamiltacce ya samu su zama sashen fansa?
A’a. Ko da yake da Yesu ya haifi biliyoyin ’ya’ya kamiltattu, amma yaran ba sa cikin sashen fansa. Rayuwar Yesu kaɗai ta yi daidai da na Adamu. (1 Tim. 2:6)—6/15, shafuffuka na 13.
• Ta yaya Kiristoci za su nuna cewa suna yin biyayya ga gargaɗin da ke Ayyukan Manzanni 20:29, 30 game da malaman ƙarya?
Ba sa gayyatar su zuwa gidajensu ko kuma su gai da malaman ƙarya. (Rom. 16:17; 2 Yoh. 9-11) Kiristoci suna guje wa mujallun ’yan ridda da shirye-shiryensu a talabijin da kuma dandalin Yanar gizo da ke ɗauke da koyarwarsu.—7/15, shafuffuka na 15-16.