DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ROMAWA 9-11
Kwatancin Itacen Zaitun
Mene ne sassa dabam-dabam na itacen zaitun take wakilta?
Itacen: cikar abin da Allah yake so ya cim ma ta wurin alkawarin da ya yi da Ibrahim
Jikin itacen: Yesu, wanda shi ne mutum mafi muhimmanci a zuriyar Ibrahim
Rassan: cikakken adadin Kiristoci Shafaffu
Rassan da aka “sassare”: Yahudawa da suka ƙi gaskata da Yesu
Rassan da aka haɗa da itacen: Kiristoci shafaffu da suka fito daga ƙasashe dabam-dabam
Kamar yadda aka annabta, zuriyar Ibrahim, wato Yesu da shafaffun Kiristoci 144,000 za su kawo albarka ga “dukan kabilun duniya.”—Ro 11:12; Fa 22:18
Mene ne na koya game da yadda Jehobah ya cika alkawarin da ya yi game da zuriyar Ibrahim?