Dā Ina Tsoron Mutuwa, Amma Yanzu Ina Jiran ‘Rai A Yalwace’
Piero Gatti ne ya ba da labarin
WATA ƙara da ta soma a hankali ta cika ko’ina. Sai ƙarar jiniya ta soma domin mutane su nemi mafaka su ɓoye. Sai muka ji ƙarar fashewar bama-bamai da kuma rushewar gidaje wadda somawar ta’addanci ne ke nan.
Wannan ya faru a birnin Milan, a Italiya, a shekara ta 1943 da 1944. A matsayina na soja matashi da aka ajiye a wurin, an ce mini sau da yawa na kwashe gawawwakin mutanen da bam ɗin ya yi kaca-kaca da su a cikin gidajen da suka shiga don samun mafaka. Kuma ba mutuwar mutane ba kawai na gani. A wasu lokatai, na sha da ƙyar. A waɗannan lokatai, na yi addu’a ina wa Allah alkawari cewa idan na tsira, zan yi nufinsa.
Yadda na Daina Tsoron Mutuwa
Na yi girma a wani ƙauye kusan mil shida daga birnin Como, a ƙasar Italiya, kusa da iyakar ƙasar Siwizalan. Sa’ad da nake ƙarami, na fuskanci baƙin ciki kuma ina tsoron mutuwa. ’Yan’uwana mata biyu sun mutu sanadiyyar cutar massassara. Sai a shekara ta 1930, sa’ad da nake ɗan shekara shida, mahaifiyata Luigia ta mutu. A matsayi na na ɗan cocin Katolika, ina kiyaye dokokin addinai kuma ina halartar Coci mako-mako. Amma na daina jin tsoron mutuwa shekaru da yawa bayan hakan, ba a coci ba amma a shagon aski.
Ana ta kashe-kashe a Yaƙin Duniya na biyu a shekara ta 1944. Ina ɗaya cikin dubban sojoji da suka gudo daga wurin da ake yaƙi zuwa ƙasar Siwizalan da ba a yaƙi. Sa’ad da muka isa wurin, sai aka kai mu sansanin masu gudun hijira. An tura ni zuwa wani sansanin da ke Steinach, a arewa matso gabas na ƙasar. A wurin an ba mu ’yancin yin wasu abubuwa. Mai askin da ke Steinach yana bukatar wani ya riƙa taimaka masa a shagonsa. Mun yi aiki tare kuma mun kwana a ɗaki ɗaya na wata guda, kuma hakan ya isa mu saba da juna sosai har ya rinjaye ni.
Wani mutum Adolfo Tellin yana yawan zuwa aski a shagon, kuma shi Ba-Italiya ne da ke zama a ƙasar Siwizalan. Shi Mashaidin Jehobah ne. Ban taɓa sanin wannan rukunin ba, kuma hakan ba abin mamaki ba ne domin akwai Shaidu ɗari da hamsin kawai a Italiya baki ɗaya. Adolfo ya tattauna da ni game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki mai ban al’ajabi, wato, alkawarin salama da kuma ‘rai a yalwace.’ (Yoh. 10:10; R. Yoh. 21:3, 4) Wannan saƙon game da rayuwa a nan gaba ba tare da yaƙi da mutuwa ba ya burge ni sosai. Na gaya wa wani matashi Ba-Italiya mai suna Giuseppe Tubini da muke sansanin tare wannan saƙon, kuma hakan ya burge shi. Adolfo da kuma wasu Shaidu sukan ziyarce mu a kai a kai a sansanin.
Adolfo ya kai ni garin Arbon, kusan mil shida daga Steinach, inda ƙaramin rukunin Shaidu suke yin taro a yaren Italiya. Abin da na ji ya burge ni sosai har na taka zuwa wurin taron a mako na gaba. Daga baya, na halarci babban taro na Shaidun a wata majami’ar taro a birnin Zurich. Bidiyon sansanin share dangi inda aka nuna tarin gawawwaki musamman ne ya sa ni baƙin ciki sosai. Na sami labari cewa an kashe Shaidu da yawa a ƙasar Jamus saboda imaninsu. Na haɗu da Maria Pizzato a taron. Hukumomin mulkin Wariya na ƙasar Italiya sun saka ta a kurkuku na shekara sha ɗaya saboda imaninta.
Na koma wata ƙaramar ikilisiya da ke birnin Como a ƙasar Italiya, sa’ad da aka gama yaƙin. Ba a yawan nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, amma na san muhimman koyarwar gaskiya. Maria Pizzato ma tana ikilisiyar. Sai ta gaya mini muhimmancin yin baftisma kuma ta gayyace ni zuwa wurin Marcello Martinelli, wanda ke zama a Castione Andevenno, a lardin Sondrio. Marcello wani ɗan’uwa shafaffe mai aminci ne da aka saka shi cikin kurkuku na tsawon shekara sha ɗaya. Ina tuƙa keke na tsawon mil hamsin don na ziyarce shi.
Marcello ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya bayyana mini farillai na yin baftisma, bayan hakan muka yi addu’a kuma muka je kogin Adda, inda aka yi mini baftisma a shekara ta 1946. Wannan rana ta musamman ce! Zaɓin da na yi na bauta wa Jehobah ya sa ni farin ciki sosai kuma yanzu ina da begen rai a nan gaba, wannan begen ya sa ban tuna cewa na tuƙa keke mil ɗari a ranar ba!
An yi taro na farko bayan yaƙi a birnin Milan a ƙasar Italiya a watan Mayu, 1947. Mutane ɗari bakwai haɗe da mutane da yawa da suka tsira daga tsanantawar mulkin Wariya ne suka halarta. Wani abin mamaki ya faru a wannan taron. Wani mutum da na yi wa wa’azi a sansanin mai suna Giuseppe Tubini ya ba da jawabin baftisma, bayan hakan shi ma ya yi baftisma!
Na samu gatar haɗuwa da Ɗan’uwa Nathan Knorr, daga Bethel na Brooklyn a wannan taron. Ya ƙarfafa ni da Giuseppe mu yi amfani da rayuwarmu a hidimar Allah. Sai na tsai da shawara cewa zan soma hidima ta cikakken lokaci kafin wata guda. Bayan na isa gida, na gaya wa iyali na shawarar da na tsai da, kuma sun nemi su sa ni sanyin gwiwa. Duk da haka, na riga na ƙudurta yin hakan. Saboda haka, wata ɗaya bayan hakan na soma hidima a Bethel da ke birnin Milan. Masu wa’azi a ƙasashen waje huɗu suna hidima a wurin: Giuseppe (Joseph) Romano da matarsa, Angelina; Carlo Benanti da matarsa, Costanza. Na biyar cikin su da bai daɗe da zuwa wurin ba shi ne Giuseppe Tubini, ni ne kuma na shida.
Bayan wata guda a Bethel, an naɗa ni a matsayin mai kula da da’ira, kuma ni ne Ba-Italiya na farko da ya samu wannan gatar. Ɗan’uwa George Fredianelli, wanda shi ne mai wa’azi a ƙasar waje daga Amirka da ya fara zuwa Italiya a shekara ta 1946, yana hidimar mai kula mai ziyara. Ya koyar da ni na ’yan makonni, sai na soma wannan aikin da kaina. Ba zan manta ikilisiya ta farko da na ziyarci ba, wato, Faenza. Ka yi tunani, ban taɓa ba da jawabi a ikilisiya ba! Duk da haka, na ƙarfafa mutane da yawa da suka halarci taron, haɗe da matasa da yawa su soma hidima ta cikakken lokaci. Daga baya, waɗannan matasan sun samu gata mai girma a fagen Italiya.
Na soma rayuwa mai daɗi na mai kula mai ziyara. Rayuwa ce mai ɗauke da abin ban mamaki da yin gyare-gyare da ƙalubale da farin ciki, kuma ’yan’uwan suna ƙauna ta sosai.
Yanayin Addini Bayan an Gama Yaƙi a Italiya
Bari in gaya muku yanayin addini a ƙasar Italiya a lokacin. Cocin Katolika ne suke ko’ina. Ko da yake an yi sabuwar doka a shekara ta 1948, amma sai shekara ta 1956 ne aka daina amfani da dokar da mulkin Wariya ya kafa cewa Shaidu su daina wa’azi. Limamai sun tayar da rigima a tarurrukan da’ira sau da yawa. Amma a wasu lokatai limaman suna shan kunya, kamar yadda ya faru a shekara ta 1948 a Sulmona, wani ƙaramin gari a cibiyar ƙasar Italiya.
An yi taron a wata majami’a. Ni ne mai kujera a ranar Lahadi, kuma Giuseppe Romano ne ya ba da jawabi ga jama’a. Mutane da yawa sun halarci taron. A lokacin Shaidu ba su kai ɗari biyar a ƙasar baki ɗaya ba, amma mutane dubu biyu ne suka halarci taron a cikin majami’ar. Bayan taron, wani matashi da firistoci biyu suka koyar da shi ya haura kan dakalin yin maganan. Ya soma ihu don ya ɗimauce taron. Sai nan da nan na gaya masa, “Idan kana da abin da kake son ka faɗa, to, ka karɓi hayar majami’a sai ka faɗi duk abin da ka ga damar cewa.” Abin da ya yi ya ɓata ran waɗanda suka halarci taron har suka soma ihu don su ɗimauce shi. Sai ya sauka daga dakalin kuma ya gudu.
Yin tafiye-tafiye a lokacin yana da daɗi sosai. A wasu lokatai ina tafiya da ƙafa daga ikilisiya zuwa ikilisiya ko na tuƙa keke ko kuma na shiga mota da ke cike da mutane ko kuma jirgin ƙasa. A wasu lokaci ina sauka a barga ko kuma shagon da ake tara kayan aiki. Mutane da yawa a ƙasar Italiya talakawa ne domin bai daɗe da aka gama yaƙi ba. Babu ’yan’uwa da yawa a ƙasar kuma su ba mawadata ba ne. Rayuwa a hidimar Jehobah tana da daɗi sosai.
Samun Koyarwa a Makarantar Gileyad
An gayyace ni da Giuseppe Tubini mu halarci aji na sha shida na makarantar Gileyad a shekara ta 1950. Daga farko na san cewa ba zai kasance da sauƙi na koyi Turanci ba. Na yi iya ƙoƙari na, amma hakan bai kasance da sauƙi ba. Muna bukatar mu karanta Littafi Mai Tsarki baki ɗaya a Turanci. Don cim ma hakan, nakan fasa cin abincin rana a wasu lokatai don na yi karatu. Daga baya, lokaci na ya zo na ba da jawabi. Ba zan taɓa mantawa da abin da malamin mu ya ce ba, “Yadda ka ba da jawabin yana da kyau sosai, amma ba a fahimci Turancin ka gabaki ɗaya ba!” Duk da hakan, na sauke karatun da kyar. Bayan hakan, aka sake tura ni da Giuseppe zuwa ƙasar Italiya. Koyarwar da aka mana ya sa muka daɗa ƙware don yi wa ’yan’uwanmu hidima.
A shekara ta 1955, na auri Lidia, wadda na ba da jawabin baftismarta shekaru bakwai da suka shige. Mahaifinta Domenico, wani ɗan’uwa ne ƙaunatacce wanda ya ƙoƙarta sosai wajen taimaka wa yaransa bakwai su koyi gaskiya, duk da cewa mulkin Wariya ya tsananta musu sosai kuma ya sa su gudun hijira na shekara uku. Lidia ma ta yi ƙoƙari sosai don gaskiya. Ta bayyana a gaban kotu sau uku don ta kāre izinin da muke da shi na yin wa’azi gida-gida. Mun samu ɗanmu na fari, Beniamino, shekara shida bayan mun yi aure. Mun samu wani ɗa mai suna Marco, a shekara ta 1972. Ina farin ciki sosai domin su biyu tare da iyalansu suna bauta wa Jehobah da ƙwazo.
Kasancewa da Ƙwazo a Hidimar Jehobah
Na shaida abubuwa masu ban farin ciki da yawa a shekaru da yawa da na yi ina yi wa mutane hidima. Alal misali, a farkon shekara ta 1980, mahaifin matata ya rubuta wa shugaban ƙasar Italiya, Sandro Pertini wasiƙa. Su biyu sun yi gudun hijira zuwa tsibirin Ventotene inda aka ajiye waɗanda ba su goyi bayan mulkin Wariya a lokacin ba. Suruki na ya ce a gana da shi don ya samu yi wa shugaban ƙasar wa’azi. Sa’ad da aka amince da hakan, sai na raka shi zuwa wurin, kuma ya marabce mu sosai, ba mu saba yin hakan ba. Shugaban ƙasan ya rungume suruki na. Sai muka tattauna game da imaninmu kuma muka ba shi wasu littattafai.
A shekara ta 1991, bayan shekara arba’in da huɗu da na yi ina hidimar mai kula mai ziyara, sai na daina hidimar bayan na ziyarci ikilisiyoyi a ƙasar Italiya baki ɗaya. A cikin shekaru huɗu na gaba, na yi hidima a matsayin Mai Kula da Majami’ar Taro har lokacin da na daina wannan hidimar saboda ciwo mai tsanani. Amma dai, ina godiya saboda alherin Jehobah, domin har ila ina hidima ta cikakken lokaci. Na yi iya ƙoƙari na don na yi wa’azi kuma na koyar da bishara, kuma har yanzu ina nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Har yanzu ’yan’uwa suna cewa jawabai na suna daɗaɗa su. Ina godiya ga Jehobah domin tsufa bai sa na rasa ƙarfi ba.
Sa’ad da nake matashi, tsoron mutuwa ya sha kaina sosai, amma sanin tacaccen sani na Littafi Mai Tsarki ya ba ni begen rai na har abada, wato, ‘rai a yalwace,’ kamar yadda Yesu ce. (Yoh. 10:10) Ga abubuwan da nake ɗokin gani, rayuwa cikin salama da kāriya da farin ciki da kuma albarkar Jehobah. Bari ɗaukaka ta kasance ga sunan Mahaliccinmu wanda aka ba mu gatar kiranmu da sunansa.—Zab. 83:18.
[Taswira a shafi na 22, 23]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
SIWIZALAN
BERN
Zurich
Arbon
Steinach
ITALIYA
ROMA
Como
Milan
Kogin Adda
Castione Andevenno
Faenza
Sulmona
Ventotene
[Hoto a shafi na 22]
Sa’ad da muke kan hanya zuwa makarantar Gileyad
[Hoto a shafi na 22]
Tare da Giuseppe a makarantar Gileyad
[Hoto a shafi na 23]
A ranar auren mu
[Hoto a shafi na 23]
Matata ƙaunatacciya ta kasance tare da ni cikin shekaru 55