Don Matasa
Yadda Za Mu Yi Tsayayya da Jarrabawa
YUSUFU—SASHE NA 1
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosin, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suka ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.
Shimfiɗar ’yan wasa: Yusufu, matar Fotifar
Taƙaitawa: Yusufu ya yi tsayayya da jarrabar yin zina da matar Fotifar.
1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA FARAWA 39:1-12.
Ka kwatanta girma da kyaun gidan Fotifar kamar yadda kake tsammani a zuciyarka.
․․․․․
Yaya za ka kwatanta siffar Yusufu? (Ƙarin haske: Sake karanta aya ta 6.)
․․․․․
Wace irin sosuwar rai ce kake ji a muryar Yusufu sa’ad da yake magana da matar Fotifar a ayoyi 8 da 9?
․․․․․
2 KA BINCIKA SOSAI.
Mene ne zai iya jarraba Yusufu ya yi watsi da ɗabi’a? (Ƙarin haske: Ka karanta Filibiyawa 2:12, kuma ka yi tunani game da yanayin Yusufu. Alal misali, a lokacin, ina ne iyalin Yusufu da sauran masu bauta wa Jehobah suke?)
․․․․․
Me kake ganin ya sa Yusufu ya yi tunani cewa yin zina zunubi ne a gaban Allah, duk da cewa a lokacin babu wata doka daga Allah da ta hana yin zina? (Ƙarin haske: Ka karanta kuma ka yi tunani a kan waɗannan nassosi: Farawa 2:24; 12:17, 18; Romawa 2:14, 15; da Ibraniyawa 5:14.)
․․․․․
3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Dangantakar da ke tsakanin kamun kai da kuma mutunci.
․․․․․
Amfanin da masu bin mizanan Allah game da ɗabi’a suke samu.
․․․․․
Bukatar horar da ‘hankalinka.’ (Ibraniyawa 5:14)
․․․․․
DON ƘARA YIN AMFANI DA ABIN DA KA KOYA.
A waɗanne ɓangarori na rayuwa ne za ka iya ƙara taka tsantsan idan ya zo ga yin tsayayya da jarrabar yin zina? (Ƙarin haske: Ka karanta kuma ka yi tunani a kan Ayuba 31:1; Zabura 119:37; Afisawa 5:3, 4.)
․․․․․
4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․
Ka ƙara koya game da littafi mai tsarki, a duniyar gizon www.watchtower.org da www.jw.org