Don Matasa
Ka Guji Muguwar Tarayya!
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosi, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.
Shimfiɗar ’Yan Wasa: Dinah da Shechem da Yakubu da Simeon da Lawi
Taƙaitawa: Shechem ya ɓāta Dinah, kuma ’yan’uwanta da ke cike da fushi suka je suka ɗauki fansa.
1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA FARAWA 34:1-31.
Waɗanne irin sha’ani ne kake tunanin cewa Dinah ta yi da ƙawayenta a Ka’anan?
․․․․․
Waɗanne irin kalmomi masu daɗi ne kake tunanin cewa Shechem yake yi wa Dinah?
․․․․․
Wace irin sosuwar rai ce kake ji a muryar Yaƙub sa’ad da yake yi wa Simeon da Lawi faɗa a aya ta 30?
․․․․․
2 KA BINCIKA SOSAI.
A ganin ka, me ya sa Dinah take yawan ziyartar ’yan matan Kan’anan? (Alal misali, waɗanne abubuwa ne take so da su ma suke so? Mene ne wataƙila take samu a tsakanin mutanen Ka’ana da ba ta samu a gida?)
․․․․․
Waɗanne halaye masu jan hankali na Shechem ne wataƙila Dinah ta gani? (Sake karanta ayoyi na 3, 12 da na 19.)
․․․․․
Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba ta son ta yi jima’i da Shechem? (Sake karanta aya ta 2.)
․․․․․
Ɗaukar fansar da Simeon da Lawi suka yi ta wajen kashe mazajen birnin Shechem yana da kyau? Me ya sa yake da kyau, ko me ya sa bai da kyau?
․․․․․
3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Muhimmancin zaɓan abokan kirki.
․․․․․
Muhimmancin kasancewa da kamun kai, ko da kana da dalili mai kyau na yin fushi.
․․․․․
DOMIN ƘARA YIN AMFANI DA ABIN DA KA KOYA.
Waɗanne matakai ne za ka iya ɗauka don guje wa masu lalata da yara, wato, waɗanda ba sa bin mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a?
․․․․․
4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․
Ka ƙara koya game da littafi mai tsarki, a yanar gizon www.watchtower.org da www.jw.org