Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/15 pp. 2-22
  • ‘’Yar Ruhu’ Tana Ɗaukaka Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘’Yar Ruhu’ Tana Ɗaukaka Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙauna da Take Bisa Ƙa’ida Mai Girma
  • “Farin Zuciya na Ruhu Mai-Tsarki”
  • “Ɗayantuwar Ruhu Cikin Ɗaurin Salama”
  • Kauna​—Hali ne Mai Muhimmanci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/15 pp. 2-22

‘’Yar Ruhu’ Tana Ɗaukaka Allah

“Inda ake ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya da yawa.”—YOH. 15:8.

1, 2. (a) Waɗanne zarafi muke da su na ƙarfafa mutane? (b) Wace baiwa daga wurin Allah ce take kyautata ingancinmu na bauta masa?

KA YI la’akari da wannan yanayin: Wata ’yar’uwa ta lura cewa wata matashiya tana da matsalar da ke damunta. Sai ta shirya su fita hidimar fage tare. Sa’ad da suke tattaunawa bayan sun fita daga gidan mutane, matashiyar ta soma faɗa wa ’yar’uwar abin da ke nauyaya ta. Sa’ad da ’yar’uwar matashiya take addu’a da yamma, ta yi wa Jehobah godiya don kulawa da ’yar’uwar da ta manyanta ta nuna mata, ta ce, lallai abin da nake bukata ke nan. A wani wuri kuma, bai daɗe da wasu ma’aurata suka dawo wa’azi daga ƙasar waje ba. Sa’ad da suke ba da labarai a wani taro, wani ɗan’uwa matashi ya yi shiru yana saurarawa sosai. Wasu shekaru bayan hakan, sa’ad da ɗan’uwan yake shirin yin tafiya zuwa ƙasar waje, ya tuna ma’auratan da kuma tattaunawarsu da ta motsa shi ya zama mai wa’azi a ƙasashen waje.

2 Wataƙila waɗannan labaran sun tuna maka wasu mutane da suka shafi rayuwarka ko kuma waɗanda ka shafi rayuwarsu. Hakika, tattaunawa ba ta yawan sa mutum ya canja salon rayuwarsa, amma dai muna da zarafi da yawa na ƙarfafa mutane a kowacce rana. Ka yi tunani cewa akwai abin da zai iya kyautata ingancinka da halayenka, ya sa su fi amfanar ’yan’uwanka da kuma Allah. Shin hakan ba zai yi kyau ba ne? Hakika, Jehobah ya yi mana irin wannan baiwar, wato, ruhunsa mai tsarki. (Luk 11:13) Yayin da ruhun Allah yana aiki a rayuwarmu, yana sa mu samu halaye masu kyau da suke kyautata dukan fannonin hidimarmu ga Allah. Wannan baiwa ce mai kyau sosa!—Karanta Galatiyawa 5:22, 23.

3. (a) Ta yaya samun ‘’yar ruhu’ yake ɗaukaka Allah? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Jehobah Allah wanda shi ne tushen wannan ruhu mai tsarki yana yin amfani da wannan ruhun don ya nuna halaye da suka jitu da halinsa. (Kol. 3:9, 10) Yesu ya nuna ainihin dalilin da ya sa ya kamata Kiristoci su yi koyi da Allah sa’ad da ya gaya wa manzanninsa: “Inda ake ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya da yawa.”a (Yoh. 15:8) Yadda muke magana da kuma aikatawa za su nuna cewa muna rayuwa da ta jitu da ‘’yar ruhu,’ kuma hakan zai kawo yabo ga Allah. (Mat. 5:16) A waɗanne hanyoyi ne ’yar ruhu ta bambanta da halayen duniyar Shaiɗan? Ta yaya za mu iya samun ’yar ruhu? Ta yaya yin hakan zai iya kasance da ƙalubale? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin yayin da muke tattauna waɗannan fannoni na ɗaya na biyu da na uku na ’yar ruhu, wato, ƙauna da farin ciki da kuma salama.

Ƙauna da Take Bisa Ƙa’ida Mai Girma

4. Wacce irin ƙauna ce Yesu ya koya wa mabiyansa?

4 Ƙaunar da ruhu mai tsarki ke sa mu nuna yana da bambanci da irin ƙaunar da gama gari ne a duniya. Ta yaya? Domin tana bisa ƙa’ida mai girma. Yesu ya nanata wannan bambancin a Huɗuba a kan Dutse. (Karanta Matta 5:43-48.) Ya ambata cewa ko ma masu zunubi suna bi da mutane daidai yadda ake bi da su. Irin wannan “ƙaunar” ba ta bukatar yin sadaukarwa amma ana yin ta ne don biyan abin da aka yi wa mutum. Idan muna son mu ‘zama ’ya’yan Ubanmu wanda ke cikin sama,’ wajibi ne mu kasance dabam. Maimakon mu bi da mutane yadda suke bi da mu, ya kamata mu ɗauke su kuma mu bi da su yadda Jehobah yake ɗaukansu da kuma bi da su. Amma yaya zai yiwu mu ƙaunaci maƙiyanmu, yadda Yesu ya umurce mu?

5. Ta yaya za mu nuna ƙauna ga waɗanda suke tsananta mana?

5 Ka yi la’akari da misali guda na Littafi Mai Tsarki. An kama Bulus da Sila yayin da suke wa’azi a garin Filibi, kuma an yi musu dukan tsiya, kuma aka jefa su cikin kurkuku, inda aka saka ƙafafunsu a cikin turu. Wataƙila yarin ya wulaƙanta su sosai a wannan lokacin. Sa’ad da girgizan ƙasa ya faru kuma aka sake su farat ɗaya, shin sun yi farin ciki don za su iya rama abin da mutumin ya yi musu ne? A’a. Da yake sun damu da zaman lafiyarsa, ƙaunarsu ta sadaukarwa ta motsa su su aikata a madadinsa nan da nan, hakan ya sa yarin da dukan iyalinsa suka zama masu bi. (A. M. 16:19-34) Hakazalika, ’yan’uwanmu da yawa a wannan zamanin sun bi tafarkin ‘albarkar waɗanda ke tsananta musu.’—Rom. 12:14.

6. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ƙauna ta sadaukarwa ga ’yan’uwanmu? (Duba akwatin da ke shafi na 21.)

6 Ƙaunar da muke wa ’yan’uwa masu bi za ta fi hakan. “Ya kamata mu ba da ranmu domin ’yan’uwa.” (Karanta 1 Yohanna 3:16-18.) Amma, sau da yawa za mu iya nuna ƙauna a ƙananan hanyoyi. Alal misali, idan muka faɗa wani abu ko kuma yi abin da ya ɓata wa wani ɗan’uwa rai, muna iya nuna ƙauna ta wajen ɗaukan matakai don yin sulhu. (Mat. 5:23, 24) Idan wani ya yi mana laifi kuma fa? Shin muna “hanzarin gafartawa kuwa” ko kuma a wasu lokatai muna riƙe shi a zuciya? (Zab. 86:5) Ƙauna da ruhu mai tsarki yake sa mu nuna za ta taimaka mana mu gafarta ƙananan laifuffuka, muna gafarta wa mutane a sake “kamar yadda Ubangiji ya gafarta” mana.—Kol. 3:13, 14; 1 Bit. 4:8.

7, 8. (a) Ta yaya ƙauna ga Allah ya shafi ƙaunarmu ga mutane? (b) Ta yaya za mu iya ƙaunar Jehobah sosai? (Ka duba hoton da ke ƙasa.)

7 Ta yaya za mu iya nuna ƙauna ta sadaukarwa ga ’yan’uwanmu? Ta wurin ƙaunar Allah sosai. (Afis. 5:1, 2; 1 Yoh. 4:9-11, 20, 21) Lokacin da muka keɓe don kasancewa tare da Jehobah ta yin karatun Littafi Mai Tsarki da bimbini da kuma addu’a yana ƙarfafa mu kuma yana sa mu ƙaunaci Ubanmu na samaniya sosai. Amma dai, wajibi ne mu keɓe lokaci don kusantar Allah.

8 Alal misali: A ce zai yiwu a karanta Kalmar Allah, a yi bimbini a kai kuma a yi addu’a ga Allah a wani keɓaɓɓen lokaci kawai a kowacce rana. Shin da ba za ka yi amfani da wannan zarafin sosai ba don kada kome ya zo tsakanin lokacin da za ka kasance tare da Jehobah ba? Hakika, babu wanda zai iya hana mu yin addu’a ga Allah, kuma yawancinmu za mu iya karanta Littafi Mai Tsarki a duk lokacin da muke son mu yi hakan. Duk da haka, ya kamata mu ɗauki matakai don kada biɗe-biɗe na kullum su cinye lokacin da za mu kasance da Allah. Shin kana keɓe lokaci yadda zai yiwu a kowacce rana don ka kusaci Jehobah?

“Farin Zuciya na Ruhu Mai-Tsarki”

9. Ruhu mai tsarki zai iya taimake mu mu kasance da farin ciki duk da wane yanayi?

9 Za mu iya ci gaba da kasancewa da farin ciki wanda ɗiyar ruhu ne, duk da matsaloli. Farin ciki yana kamar shuki da ke iya jurewa a yanayi mai wuya. A ko’ina a duniya, bayin Allah da yawa sun “karɓi magana cikin ƙunci mai-yawa, tare da farin zuciya na Ruhu Mai-tsarki.” (1 Tas. 1:6) Wasu kuma suna fuskantar mawuyacin yanayi a rayuwarsu. Duk da haka, Jehobah yana ƙarfafa su ta hanyar ruhunsa don su yi “haƙuri da jimrewa tare da farinciki.” (Kol. 1:11) Mene ne tushen wannan farin cikin?

10. Mene ne ke sa mu farin ciki?

10 Dukiya ta ruhaniya da muka samu daga wurin Jehobah tana da tamani na dindindin ba kamar “wadata marar-tsayawa” na duniyar Shaiɗan ba. (1 Tim. 6:17; Mat. 6:19, 20) Ya ba mu bege na farin ciki na rayuwa marar iyaka a nan gaba. Muna farin cikin kasancewa cikin ’yan’uwancin Kirista na dukan duniya. Fiye da hakan, dangantakarmu da Allah ne ke sa mu farin ciki. Muna ji kamar Dauda, wanda ya yabi Jehobah cikin waƙa ko da an tilasta masa ya yi gudun hijira, yana cewa: “Gama rahamarka ta fi gaban rai; leɓunana za su yi yabonka. Hakanan zan albarkace ka muddar raina.” (Zab. 63:3, 4) Ko sa’ad da muke shan wahala, yabon Allah yana sa mu farin ciki sosai.

11. Me ya sa yake da muhimmanci mu bauta wa Jehobah da farin ciki?

11 Manzo Bulus ya aririce Kiristoci: “Ku yi farinciki cikin Ubangiji kullayaumi: sai in sake cewa, Ku yi farinciki.” (Filib. 4:4) Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci su yi hidimarsu ga Jehobah da farin ciki? Domin batun da Shaiɗan ya ta da game da ikon mallakar Jehobah. Shaiɗan ya yi da’awar cewa babu wanda yake bauta wa Allah da son zuciyarsa. (Ayu. 1:9-11) Idan muna bauta wa Jehobah don ya zama dole ne mu yi hakan, hadayarmu ta yabo ba za ta zama cikakkiya ba. Saboda haka muna ƙoƙari mu yi biyayya ga ƙarfafar marubucin wannan zabura: “Ku bauta wa Ubangiji da farinzuciya: Ku zo gabansa da rairawa.” (Zab. 100:2) Hidima da ake yi da farin ciki da son zuciya tana ɗaukaka Allah.

12, 13. Mene ne za mu iya yi don mu magance mugun tunani?

12 Hakika, a wasu lokatai ko bayin Jehobah masu ƙwazo suna sanyin gwiwa kuma suna fama su kasance da ra’ayi mai kyau. (Filib. 2:25-30) Mene ne zai iya taimaka mana a irin waɗannan lokatai? Afisawa 5:18, 19 ta ce: “Ku cika da Ruhu: kuna zance da junanku cikin zabura da waƙoƙin yabo da waƙoƙi masu-ruhaniya, kuna rairawa kuna yi muzika da zuciyarku ga Ubangiji.” Ta yaya za mu iya amfani da wannan gargaɗin?

13 Sa’ad da muke mugun tunani, muna iya yin addu’a ga Jehobah kuma mu yi ƙoƙari mu yi bimbini a kan abubuwa masu kyau. (Karanta Filibiyawa 4:6-9.) Wasu sun ga cewa rera kaɗe-kaɗen waƙoƙin Mulki na sa su farin ciki kuma yana taimaka musu su yi tunanin kirki. Wani ɗan’uwa da ya fuskanci wata matsala da ta sa shi taƙaici da kuma sanyin gwiwa ya tuna: “Ƙari ga yin addu’a a kai a kai, na haddace wasu waƙoƙin Mulki. Ina samun farin ciki don rera waɗannan waƙoƙi masu daɗi ga Jehobah ko a cikin zuciyata ko kuma da ƙarfi. Kuma an fito da littafin nan Ka Kusaci Jehovah a lokacin. A shekara ta gaba, na karanta littafin sau biyu. Kuma ya sanyaya mini zuciya. Na san cewa Jehobah ya albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcena.”

“Ɗayantuwar Ruhu Cikin Ɗaurin Salama”

14. Mene ne fitaccen yanayi na salama da ruhu mai tsarki yake haifarwa?

14 ’Yan’uwa na ƙasashe dabam dabam suna farin cikin yin cuɗanya da ’yan’uwansu Kiristoci a taron ƙasashe. Irin wannan yanayin yana nuna salamar da mutanen Allah suke morewa a yau, wato, haɗin kai na dukan duniya. Mutane suna mamaki sa’ad da suka ga mutanen da ya kamata su riƙa gaba da juna suna ‘ƙwazo su kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.’ (Afis. 4:3) Wannan haɗin kai yana da ban mamaki domin mutane da yawa sun bar halayensu na dā don su kasance hakan.

15, 16. (a) Yaya aka raine Bitrus, kuma yaya hakan ya kasance da ƙalubale a gare shi? (b) Ta yaya Jehobah ya taimaki Bitrus ya daidaita ra’ayinsa?

15 Yana da ƙalubale mutane daga al’adu dabam dabam su kasance da haɗin kai. Don mu fahimci abin da ya kamata mu yasar don mu kasance da wannan haɗin kai, bari mu yi la’akari da misalin manzo Bitrus a ƙarni na farko. Ra’ayinsa game da ’Yan Al’ummai da ba su yi kaciya ba ya bayyana a waɗannan kalamai da ya furta: “Ku da kanku kun sani haram ne ga mutum Ba-yahudi ya saje da mutum na wani dangi dabam, ko kuwa shi zo wurinsa; amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowane mutum haram ko mai-ƙazanta.” (A. M. 10:24-29; 11:1-3) Bisa ga ra’ayi da gama gari ne a lokacin, wataƙila Bitrus ya girma da ra’ayin cewa Dokar ta bukace shi ya yi ƙaunar ’yan’uwansa Yahudawa kawai. Wataƙila ya ga ya dace ya ɗauki ’Yan Al’ummai a matsayin abokan gaba da ya kamata ya tsana.b

16 Ka yi tunanin irin ƙyamar da Bitrus ya yi sa’ad da ya shiga gidan Karniliyus. Shin zai yiwu mutumin da a dā yake da ra’ayi marar kyau game da ’Yan Al’ummai ya kasance “haɗaɗe” da kuma “ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama”? (Afis. 4:3, 16) Hakika, zai yiwu domin a ’yan kwanakin da suka gabata, ruhun Allah ya buɗe zuciyar Bitrus, kuma ya sa ya soma daidaita ra’ayinsa kuma ya sha kan wariya da yake yi. Jehobah ya bayyana masa ta wahayi cewa ra’ayin Allah game mutane bai dangana ba ga launin fata ko kuma ƙasa ba. (A. M. 10:10-15) Saboda haka, Bitrus ya gaya wa Karniliyus: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (A. M. 10:34, 35) Bitrus ya daidaita ra’ayinsa, kuma ya kasance da haɗin kai da dukan “’yan’uwanci.”—1 Bit. 2:17.

17. Ta yaya haɗin kai da mutanen Allah suke morewa yake da ban mamaki?

17 Abin da ya faru da Bitrus ya taimaka mana mu fahimci canji mai girma da ke faruwa a tsakanin mutanen Allah a yau. (Karanta Ishaya 2:3, 4.) Miliyoyin mutane “daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna” sun daidaita ra’ayinsu ya jitu da “nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” (R. Yoh. 7:9; Rom. 12:2) Ƙiyayya da magabtaka da tsatsaguwa na duniyar Shaiɗan ya rinjayi mutanen nan da yawa a dā. Amma ta wurin nazarin Kalmar Allah da taimakon ruhu mai tsarki, sun koya su biɗa “abu fa da ke nufa wajen salama.” (Rom. 14:19) Haɗin kai da aka samu ta yin hakan yana sa a ɗaukaka Allah.

18, 19. (a) Ta ya kowannenmu zai sa ikilisiya ta kasance da salama da haɗin kai? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Ta yaya kowannenmu zai sa salama da haɗin kai ya kasance tsakanin mutanen Allah? Ikilisiyoyi da yawa suna da mutane da suka fito daga wasu ƙasashe. Wataƙila wasu mutanen suna da al’adu dabam dabam ko kuma ba sa iya faɗan yarenmu da kyau ba. Shin muna ƙoƙari mu san su sosai? Wannan ne tafarki da Kalmar Allah ta ce mu bi. Sa’ad da yake rubuta wa ikilisiyar da ke Roma, wadda ta ƙunshi masu bi Yahudawa da ’Yan Al’ummai, Bulus ya ce: “Ku karɓi juna, kamar yadda Kristi kuma ya karɓe ku, zuwa ga darajar Allah.” (Rom. 15:7) Akwai wani a ikilisiyarku da za ka yi ƙoƙari ka san shi sosai?

19 Mene ne kuma za mu iya yi domin mu sa ruhu mai tsarki ya ja-gorance mu? Talifi na gaba zai bincika wannan tambayar yayin da muke tattauna fannonin ’yar ruhu da suka rage.

[Hasiya]

a ’Ya’ya da Yesu ya ambata sun haɗa da ‘’yar ruhu’ da kuma ‘’ya’yan leɓuna’ waɗanda Kiristoci suke nunawa ta aikin wa’azin Mulki da suke yi.—Ibran. 13:15.

b Littafin Levitikus 19:18 ya ce: “Ba za ka ɗauka wa kanka fansa, ba kuwa za ka yi nukuran ’ya’yan jama’arka; amma sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” Shugabannin addinan Yahudawa sun gaskata cewa “’ya’yan jama’arka” da “maƙwabcinka” yana nufin Yahudawa ne kawai. A gaskiya, Dokar ta ce Isra’ilawa su ware kansu daga sauran al’ummai. Amma dai, bai ƙarfafa ra’ayin da shugabannin addinin Yahudawa na ƙarni na farko suke da shi ba cewa dukan waɗanda ba Yahudawa ba ne maƙiya da za su tsana.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya za mu nuna ƙauna ta sadaukarwa ga ’yan’uwanmu?

• Me ya sa yake da muhimmanci mu yi hidimarmu ga Allah da farin ciki?

• Ta yaya kowannenmu zai sa ikilisiya ta kasance da salama da haɗin kai?

[Akwati da ke shafi na 21]

“Waɗannan Ne Kiristoci na Gaske”

Littafin nan Between Resistance and Martyrdom—Jehovah’s Witnesses in the Third Reich ya rubuta abin da wani majagaba matashi Bayahude wanda yake kurkuku ya faɗa game da yadda ya fara saduwa da Shaidun Jehobah bayan ya isa sansanin Neuengamme:

“Da zarar mu Yahudawa daga Dachau muka shigo cikin sansanin, Yahudawa da suke wurin suka soma ɓoye komi da suke da shi don kada su ba mu. . . . Muna taimakon juna kafin a saka mu a cikin kurkuku. Amma a wannan yanayi na a yi rai ko a mutu, kowa yana son ya ceci kansa, ba wani ba. Amma ka yi tunanin abin da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke yi. A lokacin, sun yi aiki tuƙuru, suna gyara wasu famfunan ruwa. Akwai sanyi sosai a lokacin kuma a dukan ranar sun tsaya a cikin ruwan ƙanƙara. Babu kowa da ya san yadda za su jimre da wannan yanayin. Sun ce Jehobah ne ya ba su ikon. Suna bukatar burodi da za su ci sosai, kamar mu, domin suna jin yunwa. Amma mene ne suke yi? Suka karɓi dukan burodin da suke da shi, sai suka ɗebi rabi, kuma suka ba ’yan’uwansu masu bi da suka zo daga Dachau rabin da ya rage. Sai suka marabce su kuma suka yi musu sumba. Suna yin addu’a kafin su ci abinci. Bayan haka, dukansu suka gamsu kuma suka yi farin ciki. Suka ce sun daina jin yunwa. Ka ga dalilin da ya sa na yi tunani cewa: Waɗannan ne Kiristoci na gaske.”

[Hotuna da ke shari na 19]

Shin kana keɓe lokaci daga wasu ayyuka kowace rana don ka kusaci Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba