Annabci Mai Muhimmanci Sosai
“Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”—MATTA 24:14, Littafi Mai Tsarki.
MASANA sun yarda cewa wannan ayar tana da muhimmanci sosai. Tana da muhimmanci domin za a yi aikin da ta kwatanta ne a dukan duniya. Tana kuma da muhimmanci domin ta nuna abin da ya kamata Kiristoci su riƙa yi, wato, aikin wa’azin da zai gabaci kuma ya sanar da aukuwa ta musamman a dukan duniya wadda Yesu ya kira “ƙarshe.”
Wannan ayar wadda annabci ce tana samun cikawa a yau. Hakan ya shafe ka domin bisharar tana ɗauke da gayyata da kuma gargaɗi. Ta ba ka zaɓi: Ka amince da Mulkin Allah ko ka yi hamayya da shi. Zaɓin da ka yi zai shafi rayuwarka.
Ka yi la’akari da mahallin. Akwai lokacin da almajiran Yesu suka zo wurinsa kuma suka tambaye shi game da abubuwan da za su faru a gaba. Suna sha’awar sanin Mulkin Allah da za a kafa, wanda Yesu ya sha yin maganarsa. Kuma suna son su san ma’anar “ƙarewar zamani,” ko kuma “ƙarshen duniya,” kamar yadda wasu fassara suka kira wannan furcin.—Matta 24:3, LMT, American Standard Version, King James Version.
Sa’ad da yake ba su amsa, Yesu ya annabta cewa za a yi yaƙe-yaƙe sosai, yunwa, annoba, da manyan girgizar ƙasa. Ya ce mugunta za ta ƙaru, malaman addinan ƙarya za su yaudari mutane da yawa, za a ƙi jinin Kiristoci na gaskiya kuma za a tsananta musu. Dukan waɗannan labaran ba su da daɗi.—Matta 24:4-13; Luka 21:11.
Amma akwai albishiri. Yesu ya faɗi kalmomin da aka yi ƙaulinsu a sama, kalmomin da ƙarnuka da dama sun sa mutane yin tunani game da ma’anarsu kuma sun sa su kasance da bege. Ko da yake mutane sun amince da muhimmancin kalmomin Yesu, bayanan da suka ba da game da mana’arsu sun saɓa wa juna. Mece ce ainihin wannan bisharar? Mene ne Mulkin? A yaushe ne wannan annabcin zai cika kuma ta hanyar wa? Kuma mene ne ƙarshen? Bari mu gani.
[Hoton da ke shafi na 2, 3]
Kofin rubutun Washington na linjila huɗu.An taƙaita Matta 24:14
[Inda Aka Ɗauko]
Daga littafin nan Facsimile of the Washington Manuscript of the Four Gospels in the Freer Collection 1912