Za Ka Samu Albarka Ta Wurin Sarki Da Ruhun Allah Yake Yi Wa Ja-gora!
“Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa.”—ISHA. 11:2.
1. Waɗanne damuwa ne wasu mutane suka furta game da matsalolin duniya?
“A DUNIYA da take cikin matsi na siyasa, na zaman jama’a da kuma na mahalli, ta yaya ’yan Adam za su iya jimre wasu shekaru ɗari?” Ɗan kimiyya Stephen Hawking ne ya yi wannan tambaya a shekara ta 2006. Wani talifi a cikin jaridar New Statesman ya lura: “Ba mu kawar da talauci ba kuma ba mu kawo zaman lafiya a duniya ba. Akasin haka, kamar dai abin da muka cim ma ya saɓa wa wannan. Amma ba wai ba mu yi ƙoƙari ba ne. Mun gwada kome daga kwaminisanci zuwa kasuwanci tsantsa, daga Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya zuwa hana makamashin nukiliya. Mun yi ‘yaƙe-yaƙe da yawa don a daina yaƙi’ don mu gaskata cewa mun san yadda za mu kawo ƙarshen yaƙi.”
2. Ba da daɗewa ba, yaya Jehobah zai nuna ikon mallakarsa a bisa duniya?
2 Irin waɗannan kalaman ba abin mamaki ba ne ga bayin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ba a halicci ’yan Adam su ja-goranci kansu ba. (Irm. 10:23) Jehobah ne kaɗai Mamallakinmu da ya dace. Saboda haka, yana da hakkin kafa mana mizanai, ya bayyana irin rayuwa da za mu yi, kuma ya yi mana ja-gora zuwa wannan nufin. Bugu da ƙari, ba da daɗewa ba, zai aikata da ikonsa ya kawo ƙarshen ƙoƙarce-ƙoƙarcen ’yan Adam na sarautar kansu da ba ta yi nasara ba. Yayin nan kuma, zai halaka dukan waɗanda ta wurin ƙin ikon mallakarsa za su ci gaba da sa ’yan Adam su kasance cikin bauta ga zunubi, ajizanci, da kuma “allah na wannan zamani” Shaiɗan Iblis.—2 Kor. 4:4.
3. Mene ne Ishaya ya annabta game da Almasihu?
3 A cikin Aljanna ta sabuwar duniya, Jehobah zai nuna ikon mallakarsa cikin ƙauna ga ’yan Adam ta wurin Mulkin Almasihu. (Dan. 7:13, 14) Game da Sarkinta, Ishaya ya annabta: “Daga cikin tsutsugen Jesse toho za ya fito, reshe kuma daga cikin sauyoyinsa za ya bada ’ya’ya: ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa, ruhun ilimi da na ganewa, ruhun shawara da iko, ruhun sani da na tsoron Ubangiji.” (Isha. 11:1, 2) A waɗanne hanyoyi ne Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya sa Yesu Kristi “tsutsugen Jesse” ya cancanci yin sarauta bisa ’yan Adam? Waɗanne albarka ne za a samu daga sarautarsa? Kuma mene ne za mu yi don mu samu waɗannan albarka?
Allah Ya sa Ya Cancanta Yin Sarauta
4-6. Wane sani mai muhimmanci ne zai taimaki Yesu ya zama Sarki da Babban Firist, da kuma Alƙali mai hikima da kuma tausayi?
4 Jehobah yana son talakawansa ’yan Adam su samu kamiltawa a ƙarƙashin ja-gorancin wanda da gaske Sarki ne da Babban Firist da kuma Alƙali mai hikima da juyayi. Shi ya sa Allah ya zaɓi Yesu Kristi wanda ta wurin ruhu mai tsarki ya cancanci samun waɗannan hakki mafi muhimmanci. Ka yi la’akari da wasu dalilai da suka sa Yesu zai cika hakkin da Allah ya ba shi da kyau.
5 Yesu ne ya fi sanin Allah. Ɗa makaɗaici ya san Uban da daɗewa fiye da kowa, wataƙila shekaru biliyoyi da yawa. A wannan lokaci, Yesu ya zo ga sanin Jehobah sosai da aka kwatanta shi a matsayin “surar Allah marar-ganuwa.” (Kol. 1:15) Yesu da kansa ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.”—Yoh. 14:9.
6 Da yake shi ne na biyu ga Jehobah, Yesu ya fi sanin dukan halittu, har da ’yan Adam. Kolosiyawa 1:16, 17 ta ce: “A cikinsa [Ɗan Allah] aka halicci dukan abu, cikin sammai da bisa duniya kuma, abubuwa masu-ganuwa da abubuwa marasa-ganuwa, . . . shi ne kuwa gaɓa da dukan abu, a cikinsa kuwa dukan abu suna harhaɗe.” Ka yi tunani a kan wannan! Yesu, a matsayin “gwanin mai-aiki,” na Allah ya saka hannu cikin dukan wasu fasalolin halitta. Saboda haka, ya fahimci kowanne abu dalla-dalla game da dukan sararin samaniya, har da ƙwaƙwalwar ’yan Adam mai ban mamaki. Hakika, Yesu Kristi da kansa kwatanci ne na hikima!—Mis. 8:12, 22, 30, 31.
7, 8. Yaya ruhun Allah ya taimaka wa Yesu a hidimarsa?
7 An shafe Yesu da ruhu mai tsarki na Allah. “Ruhun Ubangiji yana bisa na,” in ji Yesu, “gama ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa: Ya aike ni domin in yi wa ɗaurarru shela ta saki, da mayarwar gani ga makafi, in kwance waɗanda an ƙulle su, in yi shelar shekara ayananniya ta Ubangiji.” (Luk 4:18, 19) Sa’ad da Yesu ya yi baftisma, babu shakka ruhu mai tsarki ya sa ya tuna abubuwan da ya koya kafin ya zo duniya, haɗe da abin Allah yake son sa ya yi a lokacin hidimarsa a duniya a matsayin Almasihu.—Karanta Ishaya 42:1; Luka 3:21, 22; Yohanna 12:50.
8 Domin ruhu mai tsarki ya ba shi iko kuma domin shi kamiltacce ne a jiki da kuma hankali, Yesu mutumi ne mafi girma da kuma babban Malami. A gaskiya, masu sauraronsa sun yi “mamaki da koyarwansa.” (Mat. 7:28) Wani abu kuma shi ne, Yesu ya iya magance ainihin tushen matsalolin ’yan Adam, wato, zunubi da ajizanci da kuma rashin sanin Allah. Kuma yana iya sanin zuciyar mutane kuma ya bi da su hakan.—Mat. 9:4; Yoh. 1:47.
9. Ta yaya aka kyautata tabbacinka ga Yesu a matsayin Sarki ta wajen yin tunani a kan abin da ya fuskanta sa’ad da yake duniya?
9 Yesu ya yi rayuwa na ɗan Adam. Abin da ya fuskanta a matsayin ɗan Adam da kuma tarayyarsa na kusa da ’yan Adam ajizai ya taimaka wajen sa Yesu ya cancanci zama Sarki. Manzo Bulus ya rubuta: “Ya zama wajib [Yesu] ya kamantu ga ’yan’uwansa a cikin dukan abu, domin ya zama babban firist mai-jinƙai, mai-aminci, cikin matsaloli na wajen Allah, domin ya yi kafarar zunuban jama’a. Gama yayinda shi da kansa ya sha wahala ana jarabtarsa, yana da iko ya taimaki waɗanda a ke jarabtarsu.” (Ibran. 2:17, 18) Domin an ‘jarabci’ Yesu, zai ji tausayin waɗanda suke shan wahala. An ga juyayin Yesu sosai sa’ad da yake hidima a duniya. Masu rashin lafiya da naƙasassu da gajiyayyu, har ma yara sun kusace shi. (Mar. 5:22-24, 38-42; 10:14-16) Masu tawali’u da waɗanda suke ɗokin su koya game da Allah sun kusace shi. A wata sassa kuma, masu fahariya da masu girman kai da waɗanda ba sa “ƙaunar Allah” sun ƙi shi, sun tsane shi kuma sun yi masa hamayya.—Yoh. 5:40-42; 11:47-53.
10. A wace hanya mai girma ce Yesu ya nuna ƙaunarsa dominmu?
10 Yesu ya ba da ransa dominmu. Wataƙila abin da ya fi nuna cewa babu Sarki da zai fi Yesu kyau shi ne kasancewarsa a shirye ya mutu dominmu. (Karanta Zabura 40:6-10.) Kristi ya ce: “Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya bada ransa domin abokansa.” (Yoh. 15:13) Hakika, ba kamar sarakuna ’yan Adam ajizai ba, waɗanda sau da yawa suna rayuwar jin daɗi da kuɗin talakawansu, Yesu ya ba da ransa domin ’yan Adam.—Mat. 20:28.
An Ba Shi Ikon Yin Amfani da Fansar
11. Me ya sa muke da cikakken tabbaci ga Yesu mai Fansarmu?
11 Ya dace cewa Yesu a matsayin Babban Firist shi ne zai yi ja-gora wajen yin amfani da fa’idodin hadayarsa ta fansa a madadinmu! Sa’ad da yake hidima a duniya, Yesu ya nuna mana misalin abin da zai yi a matsayin Mai Fansarmu a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu, da za mu more idan muna da aminci. Ya warkar da masu ciwo da naƙasassu, kuma ya ta da matattu, ya ciyar da taro mai girma, kuma ya tsawata wa iskar sai ta lafa ta yi tsit. (Mat. 8:26; 14:14-21; Luk 7:14, 15) Bugu da ƙari, ya yi waɗannan abubuwa ba don ya jawo hankalin mutane ga ikonsa ba amma don ya nuna juyayinsa da kuma ƙaunarsa. Ya gaya wa kuturu da ya roƙe shi ya warkar da shi: “Na yarda.” (Mar. 1:40, 41) Yesu zai nuna irin wannan juyayin a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu a dukan duniya.
12. Ta yaya Ishaya 11:9 za ta samu cikawa?
12 Kristi da abokan sarautarsa za su ci gaba da aikin koya wa mutane game da Allah da Yesu ya soma shekaru dubu biyu da suka shige. Da hakan kalaman Ishaya 11:9 za su cika: “Duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.” Babu shakka, wannan ilimantarwa na Allah zai haɗa da koyarwa a kan yadda za a kula da duniya da halittu masu yawa da ke cikinta, kamar yadda aka gaya wa Adamu ya yi a dā. A ƙarshen shekara dubu, nufin Allah na asali yadda aka faɗa a Farawa 1:28 zai cika, kuma a lokacin an riga an aikata amfanin hadayar fansa.
An Ba Shi Iko Ya Yi Shari’a
13. Yaya Yesu ya nuna ƙaunarsa ga adalci?
13 Kristi ne “Allah ya sanya shi Mai-shari’a na masu-rai da matattu.” (A. M. 10:42) Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Yesu bai ɓata halinsa ba, kuma adalci da aminci suna kama da bel da ya sha ɗamara da shi! (Isha. 11:5) Ya tsane haɗama, munafunci, da wasu abubuwa da ba su da kyau, kuma ya tsauta wa waɗanda ba sa damuwa game da wahalar da wasu suke sha. (Mat. 23:1-8, 25-28; Mar. 3:5) Bugu da ƙari, Yesu ya nuna cewa yadda mutum yake a waje ba ya ruɗinsa, “gama shi da kansa yana sane da abin da ke cikin mutum.”—Yoh. 2:25.
14. A wace hanya ce Yesu yake nuna ƙaunarsa ga adalci da shari’a yanzu, kuma me ya kamata mu tambayi kanmu?
14 Yesu ya ci gaba da nuna yana ƙaunar adalci da shari’a ta wajen kula da aikin wa’azi da koyarwa mai girma da ake yi a tarihin duniya. Babu ɗan Adam, babu gwamnatin ɗan Adam da kuma mugun ruhu da za su iya hana a cika wannan aikin ga gamsuwar Allah. Da hakan, muna da tabbaci cewa bayan Armageddon, shari’ar Allah za ta kasance. (Karanta Ishaya 11:4; Matta 16:27.) Ka tambayi kanka: ‘Ina nuna halin Yesu ga mutane a hidimata? Ina ba Jehobah dukan abin da zan iya ko idan rashin lafiya ko kuma yanayi za su iya rage abin da zan iya yi ne?’
15. Tuna da mene ne zai taimaka mana mu ba Allah dukan abin da za mu iya?
15 Za a taimaka mana mu bauta wa Allah da dukan zuciyarmu idan mun ci gaba da tunawa cewa aikin wa’azi aikinsa ne. Ya ba da umurni a yi shi kuma ta wurin Ɗansa yana ja-gorar aikin, ta hanyar ruhu mai tsarki yana ƙarfafa waɗanda suke sa hannu a wannan aikin. Kana daraja gatar da kake da shi na yin hidima a matsayin abokin aiki na Allah tare da Ɗansa da ruhunsa yake wa ja-gora? Jehobah ne yake motsa mutane fiye da miliyan bakwai, yawanci waɗanda ake ɗaukan “marasa-karatu ne, talakawa” su yaɗa saƙon Mulki ga mutane da ke ƙasashe ɗari biyu da talatin da shida.—A. M. 4:13.
Ka Albarkaci Kanka ta Wurin Kristi!
16. Mene ne Farawa 22:18 take nufi game da albarkar Allah?
16 Jehobah ya gaya wa Ibrahim: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka; domin ka yi biyayya da maganata.” (Far. 22:18) Wannan yana nufin cewa waɗanda suke godiya za su saurari albarka da Ɗa Almasihu zai kawo. Kuma sun shagala ga hidimarsu a yau da waɗannan albarka a zuciya.
17, 18. Wane alkawari ne da Jehobah ya yi yake cikin Kubawar Shari’a 28:2, kuma mene ne yake nufi a gare mu?
17 Allah ya faɗa game da zuriyar Ibrahim da al’ummar Isra’ila: “Dukan waɗannan albarka [da aka faɗa a cikin Dokar alkawari] kuma za su zo maka, su tarshe ka, idan ka saurara ga muryar Ubangiji Allahnka.” (K. Sha 28:2) Za a iya faɗa hakan game da bayin Allah a yau. Idan kana son ka samu albarkar Jehobah, ka ci gaba da ‘saurara ga muryarsa.’ Sa’annan albarkarsa “za su zo maka, su tarshe ka.” Amma, mene ne “saurara[wa]” ya ƙunsa?
18 Saurarawa ya ƙunshi yin tunani sosai ga abin da aka faɗa cikin Kalmar Allah da kuma abinci na ruhaniya da yake tanadinsa. (Mat. 24:45) Yana kuma nufin yin biyayya ga Allah da kuma Ɗansa. Yesu ya ce: ‘Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama.’ (Mat. 7:21) Kuma saurarar Allah yana nufin miƙa kai ga tsarin da ya kafa, wato, ikilisiyar Kirista da dattawa da aka naɗa, “kyautai ga mutane.”—Afis. 4:8.
19. Ta yaya za mu kasance cikin waɗanda za su samu albarka?
19 Hukumar Mulki, waɗanda suke aikata a matsayin wakilai ga dukan ikilisiyar Kirista suna cikin “kyautai ga mutane.” (A. M. 15:2, 6) Hakika, halinmu ga ’yan’uwan Kristi na ruhaniya shi ne ainihi zai nuna yadda za a yi mana shari’a a lokacin ƙunci mai girma da ke zuwa. (Mat. 25:34-40) Hanya ɗaya da za mu iya samun albarka ita ce ta wajen tallafa wa shafaffu na Allah da aminci.
20. (a) Mene ne hakki na musamman na “kyautai ga mutane”? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja waɗannan ’yan’uwan?
20 “Kyautai ga mutane” sun ƙunshi waɗanda suke Kwamitin Reshe da masu kula masu ziyara, da dattawan ikilisiya da aka naɗa dukansu da ruhu mai tsarki. (A. M. 20:28) Hakki na musamman na waɗannan ’yan’uwa shi ne su ƙarfafa mutanen Allah “har dukanmu mu kai zuwa ɗayantuwar imani na sanin Ɗan Allah, zuwa cikakken mutum, zuwa misalin tsawon cikar Kristi.” (Afis. 4:13) Hakika, su ajizai ne kamar dukanmu. Duk da haka, muna yi wa kanmu albarka sa’ad da muke godiya da kuma amince da kulawarsu na ƙauna.—Ibran. 13:7, 17.
21. Me ya sa yake da gaggawa mu yi biyayya ga Ɗan Allah?
21 Ba da daɗewa ba Kristi zai aikata ga mugun zamani na Shaiɗan. Sa’ad da hakan ya faru, rayuwarmu za ta dangana ga hukuncin Yesu, domin Allah ya ba shi iko ya ja-goranci “taro mai-girma” da aka annabta zuwa “maɓulɓulan ruwaye na rai.” (R. Yoh. 7:9, 16, 17) Saboda haka, bari mu yi iyakar ƙoƙarinmu yanzu mu miƙa kai da yardan rai da yin godiya ga Sarkin da ruhun Jehobah yake yi wa ja-gora.
Mene ne Ka Koya Daga . . .
• Ishaya 11:1-5?
• Farawa 22:18?
[Hoton da ke shafi na 17]
An ga cewa Yesu mai juyayi ne sa’ad da ya ta da ’yar Yayirus daga matattu
[Hotuna da ke shafi na 18]
Yesu Kristi yana kula da aikin wa’azi mai girma da ake yi a cikin tarihi