Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 p. 23
  • ‘Ayyukansa Sun Tafi Tare da Shi’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ayyukansa Sun Tafi Tare da Shi’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Sanarwa Ta Musamman
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Sababbi da Aka Haɗa Cikin Hukumar Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Taron da Ya Bayyana Haɗin Kanmu da Kuma Shirye-Shirye Masu Ban Sha’awa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Allah Ya Yi Mana Alheri Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 p. 23

‘Ayyukansa Sun Tafi Tare da Shi’

THEODORE JARACZ, ɗaya daga cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah, ya gama hidimarsa na duniya a safiyar ranar Laraba, 9 ga Yuni, 2010. Shekarunsa 84 ne kuma yana da mata mai suna Melita, kuma sun yi aure shekaru 53. Yana da yaya wadda take da yara uku, namiji guda da mata biyu.

An haife shi a ranar 28 ga Satumba, 1925, a garin Pike Country, Kentucky, a Amirka, kuma Ɗan’uwa Jaracz ya nuna ya keɓe kansa ga Jehobah ta wajen yin baftisma sa’ad da yake ɗan shekara sha biyar, a ranar 10 ga Agusta, 1941. Shekara biyu bayan hakan, sa’ad da yake ɗan shekara sha bakwai, ya soma hidimar majagaba ta kullum, wadda ita ce somawar hidima ta cikakken lokaci da ya yi na kusan shekara 67.

A shekara ta 1946, sa’ad da yake ɗan shekara ashirin, Ɗan’uwa Jaracz ya halarci aji na bakwai na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad. Bayan sun sauƙe karatu, an tura Ɗan’uwa Jaracz ya yi hidimar mai kula mai ziyara a birnin Cleveland, Ohio, a Amirka. A shekara ta 1951, an tura shi yin hidima a ofishin reshe da ke Ostareliya inda ya yi hidima a matsayin mai kula da reshen. Yearbook na Shaidun Jehobah na shekara ta 1983 ya faɗa cewa Ɗan’uwa Jaracz “ya ƙarfafa ’yan’uwan da ke cikin ƙasar gabaki ɗaya ta wurin ƙwazonsa don bin tsarin Allah da kuma yin ja-gora mai kyau a hidimar fage.”

Bayan ya koma Amirka, Ɗan’uwa Jaracz ya auri Melita Lasko a ranar 10 ga Disamba, 1956. Sun soma rayuwarsu ta ma’aurata ta yin hidimar mai kula mai ziyara, sun yi hidima a da’irori da gunduma na Amirka. A ƙarshen shekara ta 1974, an gayyaci Ɗan’uwa Jaracz ya zama ɗaya daga cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah.

Za mu daɗe muna tunawa da Ɗan’uwa Jaracz, amintacce wanda ya keɓe kansa ga Jehobah, kuma ya mai da hankali sosai ga ayyuka na tsarin Allah. Miji ne mai kula da kuma mai ƙauna, kuma mai ruhaniya wanda ya sa bukatun wasu gaba da nasa. (1 Kor. 13:4, 5) Wannan saka bukatun wasu gaba da nasa ya bayyana ta son a bi da kowa cikin juyayi da kirki. Ƙari ga hakan, ƙaunarsa marar iyaka da kuma kulawarsa ga mutane ta bayyana a ƙwazonsa a hidimar fage.

Ko da yake muna baƙin ciki matuƙa saboda rashin da muka yi na mai aiki tuƙuru da kuma ɗan’uwa ƙaunatacce wanda ke cikin iyalin Bethel da kuma ’yan’uwanci na dukan duniya, amma muna farin ciki domin amintacciyar hidima ta shekaru da yawa da Ɗan’uwa Jaracz ya yi ga Jehobah. Muna da tabbaci cewa ya ‘yi aminci har mutuwa kuma an ba shi rawanin rai.’ (R. Yoh. 2:10) Mun kuma tabbata cewa ‘ayyukansa sun tafi tare da shi.’—R. Yoh. 14:13.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba