Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 p. 22
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Zai Cika Nufinsa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Idan Adamu Kamilittacen Mutum ne, Me Ya Sa Ya Yi Zunubi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ta Yaya Mutuwar Yesu Za Ta Cece Mu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 p. 22

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Yesu ya gaya wa masu sauraronsa: “Ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.” Ta yaya ’yan Adam a yau za su ‘zama cikakku’?—Mat. 5:48.

Samun amsa ga wannan tambayar ya dangana ga fahimtar yadda aka yi amfani da kalmomi nan “cikakke” da “cikakku” a cikin Littafi Mai Tsarki. Ba kome ba ne da Nassosi sun kwatanta “cikakke” zai zama hakan gabaki ɗaya ba. Hakika, Jehobah cikakke ne. Mutane ko abubuwa ba sa zama cikakku gabaki ɗaya. Kalmomin Helenanci da Ibrananci da aka fassara “cikakke” sau da yawa suna nufin “manyanta” ko “marar laifi” bisa mizanan da majiya suka kafa.

An halicci Adamu da Hauwa’u cikakku a ɗabi’a da ruhaniya da kuma a zahiri. Su cikakku ne bisa mizanin da Mahaliccinsu ya kafa. Domin rashin biyayyarsu, ba su yi rayuwa da ta jitu da wannan mizanin ba kuma saboda haka da su da yaransu suka zama ajizai. Saboda haka, ’yan Adam sun samu zunubi da ajizanci da mutuwa ta wurin Adamu.—Rom. 5:12.

Amma, kamar yadda Yesu ya bayyana a cikin Huɗuba a kan Dutse, har mutane ajizai za su iya zama cikakku amma ba gabaki ɗaya ba. A wannan jawabi ya kafa mizanai don kamiltacciya ko cikakkiyar ƙauna. Irin wannan ƙaunar ce Allah ya nuna wa ’yan Adam. Yesu ya ce: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a; domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama: gama ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Mat. 5:44, 45) Ta wurin nuna irin wannan ƙaunar, almajiran Yesu suna yin koyi da cikakken misalin Allah.

A yau, Shaidun Jehobah a dukan duniya suna ƙoƙari su kasance da mizani mai girma na ƙaunar mutane. Suna son su taimaki mutane daga wurare dabam dabam da ƙabilu da kuma addinai su samu cikakken sani na koyarwar Littafi Mai Tsarki. A cikin ƙasashe 236, a yanzu Shaidu suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane fiye da 7,000,000 da suke son saƙon.

“Idan kuna ƙaunar masu ƙaunarku kaɗai, wace lada ke gareku?” Yesu ya yi tambaya. “Ko masu-karɓan haraji ba haka su ke yi ba? Idan kuwa kuna gaida ’yan’uwanku kaɗai, ina fifikonku waɗansu? ko al’ummai ma ba haka su ke yi ba?” (Matt. 5:46, 47) Kiristoci na gaskiya ba sa nuna son kai ga mutanen da suka fito daga wasu wurare; ba sa kuma nuna ƙauna ga waɗanda kaɗai za su iya saka musu da alheri. Maimakon haka, suna taimakon talakawa da kuma marar lafiya, yara da kuma manya. A waɗannan hanyoyi, Kiristoci za su iya yin koyi da ƙaunar Jehobah kuma su kasance da tawali’u amma ba a gabaki ɗaya ba.

Za mu taɓa iya more kamiltar da Adamu ya yi hasararta? Hakika, ta wurin ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu, mutane masu biyayya za su kai ga kamilta a Lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, lokacin da ‘Ɗan Allah ya halaka ayyukan Shaiɗan.’—1 Yoh. 3:8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba