Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/15 p. 32
  • “Ya Taimaka Mini na Motsa Zukatan Mutane”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ya Taimaka Mini na Motsa Zukatan Mutane”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ra’ayoyin Mutane Game da Yin Addu’a
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Bishara Don Mutanen Dukan Al’ummai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Mutane Daga “Kowane Harshe” Sun Ji Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/15 p. 32

“Ya Taimaka Mini na Motsa Zukatan Mutane”

AN YI taron ƙasashe don al’amura na duniya a Porto Alegre, birnin da ke kudancin ƙasar Brazil. Dubban mutane daga ƙasashe ɗari da talatin da biyar sun halarci taron. Sa’ad da suke shan iska, rukunin Shaidu daga ikilisiya da ke Porto Alegre suka tuntuɓi mahalartan don su tattauna saƙon Mulki na Littafi Mai Tsarki da su. Ta wace hanya ce suka tattauna?

“Mun yi amfani da ƙasidar nan Good News for People of All Nations,” in ji wata majagaba, Elizabete. Ta daɗa: “Mahalartan da yawa ba su taɓa jin bisharar Mulki ba, amma sun so saƙon sosai. Mun tattauna da mutane daga ƙasar Bolivia, Sin, Faransa, Indiya, Isra’ila, da Nijeriya. Mun ba wasu mahalartan littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a nasu yaren, kuma sun karɓa da farin ciki.”

Wani majagaba a ƙasar Mexico mai suna Raúl ma ya yi amfani da ƙasidar nan kuma ya samu sakamako mai kyau. Kwanakin baya, ya tuntuɓi wani Balarabe mai shekaru tamanin wanda ya rasa matarsa ba da daɗewa ba. Hawaye sun zubo wa mutumin don farin ciki, sa’ad da ya karanta shafi na ƙasidar da ya gabatar da saƙon Mulki a Larabci. Me ya sa? Alkawarin da Allah ya yi cewa mutuwa ba za ta kasance kuma ba, kamar yadda Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4 suka ce, ya motsa shi sosai sa’ad da ya karanta shi a nasa yaren. A wani lokaci kuma da Raúl yake wa’azi sa’ad da ya samu zarafi, sai ya sadu da wani mutum da ke yaren Portugal. Mutumin ma ya taɓa rashin ɗansa ƙaunatacce. Raúl ya sa ya karanta shafin ƙasidar da aka buga a yaren Portugal. Bayan ya karanta shafin, mutumin ya amince cewa yana son ya daɗa sanin Littafi Mai Tsarki kuma ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

Raúl ya yi amfani da ƙasidar nan Good News for People of All Nations don ya yi wa’azi ga masu yaren Armeniya, Sin, Turanci, Faransa, Jamus, Hindi, Koriya, Mixe, Pashiya, Rasha, da Zapotec. Ya ce: “Na ga muhimmancin yin amfani da ƙasidar nan a hidimata. Ta taimake ni na motsa zuciyar mutane ko da yarenmu ba ɗaya ba ne.”

Yayin da mutane da yawa suke yin tafiya kuma suke koma wata ƙasa dabam, muna da zarafi sosai na saduwa da waɗanda suke wani yare dabam. Za mu samu zarafin gaya wa mutane saƙon Mulki ta yin amfani da ƙasidar nan Good News for People of All Nations. Kana fitar hidima da shi kuwa?

[Hotuna da ke shafi na 32]

Raúl tare da ƙasidar da ta taimake shi ya motsa zukatan mutane

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba