Yin Magana A Harsuna Dabam-dabam Ya Fito Ne Daga Wurin Allah?
“BAN taɓa fahimtar abin da suke cewa,” in ji Devon. “A kowane mako a cocinmu, kamar dai mutane da yawa suna samun ruhu mai tsarki kuma a mu’ujizance suna yin magana a harsuna dabam-dabam. Wasu a cikinsu ’yan iska ne. Ni kuwa ina ƙoƙarin yin rayuwa mai kyau. Amma, duk da yawan addu’ar da nike yi don samunsa, ban taɓa samun wannan kyauta ta ruhu ba. Me ya jawo hakan?”
Shi ma Gabriel yana zuwa cocin da kamar dai mutane suna samun ruhu mai tsarki kuma suna yin magana a harsuna dabam-dabam. “Abin da ke damu na,” in ji shi, “shi ne a lokacin da nake addu’o’i, sauran mutanen suna damu na da maganganun da babu wani a cikin ni da su da ya fahimci abin da suke cewa. Babu wani da yake amfana daga waɗannan maganganun. Bai kamata ba ne a ce kyauta ta ruhun Allah tana da manufa mai amfani ba?”
Abubuwan da Devon da Gabriel suka shaida ya ta da wata tambaya mai muhimmanci, Yin magana a harsuna dabam-dabam kamar yadda ake yi a wasu coci a yau ya fito ne daga wajen Allah? Don amsa wannan tambayar, zai dace mu bincika kyautar yin magana ta hanyar mu’ujiza a tsakanin Kiristoci na karni na farko.
Sun “Soma Zance da Waɗansu Harsuna” Dabam
A cikin Littafi Mai Tsarki, mun karanta labarin wasu maza da mata da aka ba ikon yin harsunan da ba su taɓa koya ba. Na farkon ya faru ne a ranar Fentakos na 33 A.Z., ’yan makonni bayan mutuwar Yesu Kristi. A ranar a Urushalima, almajirai 120 na Yesu ‘suka cika da ruhu mai tsarki, suka soma zance da waɗansu harsuna.’ Baƙi daga ƙasashen waje “suka ɗimauce, domin kowane mutum yana jinsu suna zance da nasa harshe.”—Ayyukan Manzanni 1:15; 2:1-6.
Littafi Mai Tsarki ya ambata wasu mabiyan farko na Yesu da suke da wannan iyawar. Alal misali, domin an ƙarfafa shi da ruhu mai tsarki, manzo Bulus ta hanyar mu’ujiza ya yi harsuna dabam-dabam. (Ayyukan Manzanni 19:6; 1 Korintiyawa 12:10, 28; 14:18) Amma dukan waɗannan kyauta na ruhu mai tsarki na Allah suna da manufa mai kyau. Saboda haka, wace manufa ce yin magana a harsuna dabam-dabam ta cika a lokacin Littafi Mai Tsarki?
Alama Ce ta Goyon Baya Daga Allah
Sa’ad da yake rubuta wasiƙa ga Kiristocin da ke birnin Korinti, waɗanda wasu a cikinsu suna iya yin magana a cikin harsuna dabam-dabam, Bulus ya bayyana cewa “harsuna fa domin alama ne . . . ga marasa-bada gaskiya.” (1 Korintiyawa 14:22) Saboda haka, tare da iyawa ta yin mu’ujiza, ikon yin magana a harsuna dabam-dabam alama ce ga masu kallo cewa sabuwar ikilisiyar Kirista da aka kafa tana da amincewar Allah da goyon bayansa. Wannan kyauta ta mu’ujiza kamar alama ce da ke kan hanya wadda take nuna inda ya kamata masu neman gaskiya su je a yanzu su nemi zaɓaɓɓun mutanen Allah.
Wani abu mai muhimmanci shi ne, Littafi Mai Tsarki bai ambata cewa Yesu ko wani daga cikin annabawan da suka rayu kafin zamanin Kiristanci sun yi magana ta hanyar mu’ujiza a harsunan da ba su koya ba. Saboda haka, kyautar yin magana a harsuna dabam-dabam da aka ba mabiyan Yesu yana da wasu ƙarin manufa.
Hanya Ce ta Yaɗa Bishara
A farkon hidimarsa, Yesu ya umurci almajiransa su yi wa’azin bisharar Mulkin Allah ga Yahudawa kaɗai. (Matta 10:6; 15:24) A sakamakon hakan, da wuya almajiran su je inda ba mazaunin Yahudawa ba ne. Amma hakan zai canja ba da daɗewa ba.
Ba da daɗewa ba bayan mutuwarsa a shekara ta 33 A.Z., Yesu da aka ta da daga matattu ya umurci mabiyansa su “almajirtarda dukan al’ummai.” Ya kuma gaya wa mabiyansa cewa za su zama shaidunsa “har kuma iyakan duniya.” (Matta 28:19; Ayyukan Manzanni 1:8) Yaɗa bisharar har iyakan duniya zai bukaci yin amfani da harsuna da yawa fiye da Ibrananci.
Amma, yawancin waɗannan almajiran na farko mutane “marasa-karatu ne, talakawa.” (Ayyukan Manzanni 4:13) To, ta yaya za su iya yin wa’azi a ƙasashe masu nisa inda ake yin harsunan da ba su taɓa ji ba, balle su koyi yadda ake yin sa? Ruhu mai tsarki ya sa wasu daga cikin mutanen nan masu wa’azi da ƙwazo ta hanyar mu’ujiza su yi wa’azi sosai a harsunan da ba su taɓa koya ba a dā.
Da haka, kyautar yin magana da harsuna dabam-dabam ya cim ma manufofi masu muhimmanci guda biyu. Na farko, alama ce da ke nuna goyon baya daga Allah. Na biyu, hanya ce mai muhimmanci na taimaka wa Kiristoci na ƙarni na farko su cika aikinsu na yin wa’azi ga mutane da ke harsuna dabam-dabam. Shin, yin magana da harsuna dabam-dabam da ake yi a coci a yau suna cim ma waɗannan manufofin kuwa?
Yin Magana a Harsuna Dabam-Dabam A Yau—Alama Ce ta Goyon Baya Daga Allah Kuwa?
A ina za ka sanya alamar da za ta amfane mutane da yawa a yankinku? A cikin ɗan ƙaramin gini? A’a! Labarin ranar Fentakos ya gaya mana cewa “taro” na mutanen da ke wucewa sun ga alamar da ta sa mabiyan suka soma yin magana a harsuna dabam-dabam ta hanyar mu’ujiza. A sakamakon hakan, sun “ƙaru da mutum wajen dubu uku” a ikilisiyar Kirista a ranar! (Ayyukan Manzanni 2:5, 6, 41, Littafi Mai Tsarki) Idan mutane a yau suna da’awar cewa suna yin harsuna dabam-dabam amma suna yin hakan ne kawai a cikin ginin coci, ta yaya hakan zai iya kasancewa alama a fili ga marasa bi masu yawa?
Kalmar Allah ta ambata fasikanci da sauran “ayyukan jiki” a matsayin abubuwan da ke hamayya da ruhu mai tsarki, kuma ta daɗa cewa “waɗanda ke aika waɗannan al’amura ba za su gaji mulkin Allah ba.” (Galatiyawa 5:17-21) Idan ka ga mutanen da ba su da ɗabi’a mai kyau suna yin magana a harsuna dabam-dabam, kana iya mamaki cewa, ‘Wannan ba rashin jituwa ba ne, har da yaudara, a ce ruhu mai tsarki na Allah yana aiki a kan mutanen da suka duƙufa cikin halin da Kalmar Alllah da kanta ta haramta ba?’ Za a kwatanta hakan da alamar da aka saka a kan hanya da za ta yaudari mutane su bi inda bai dace ba.
Yin Magana a Harsuna Dabam-Dabam a Yau —Hanya Ce ta Yaɗa Bishara Kuwa?
Ɗayan manufar kyautar yin harsuna dabam-dabam a ƙarni na farko fa? Yin magana a harsuna dabam-dabam da ake yi a coci a yau hanya ce kuwa ta yin wa’azin bishara ga mutanen da suke harsuna dabam-dabam ne? Ka tuna cewa taron mutanen da suke Urushalima a ranar Fentakos ta 33 A.Z. sun fito ne daga ƙasashe da yawa, kuma sun fahimci harsunan da almajiran suka yi ta hanyar mu’ujiza sosai. Akasin haka, waɗanda suke magana a harsuna dabam-dabam a yau suna furta kalamai ne da ba ta da ma’ana ga duk wani mai sauraro.
Babu shakka, yin magana a harsuna dabam-dabam a wannan zamanin ya bambanta sosai daga kyauta ta ruhu mai tsarki da aka ba mabiya na farko na Yesu. Kai, babu wani rubutu na gaskiya game da wani da ya samu irin wannan iko na mu’ujiza tun mutuwar manzanni. Hakan ba abin mamaki ba ne ga masu karanta Littafi Mai Tsarki. Game da kyauta ta mu’ujizai, har da na yin magana a harsuna dabam-dabam, manzo Bulus da aka hure ya annabta cewa: “za su kare.” (1 Korintiyawa 13:8) Idan haka ne, ta yaya za a iya sanin wanda yake da ruhu mai tsarki a yau?
Wane ne ke Nuna Cewa Yana da Ruhu Mai Tsarki?
Yesu ya sani cewa kyautar yin managa a harsuna dabam-dabam za ta ƙare da zarar an kafa ikilisiyar Kirista. Gab da mutuwarsa, Yesu ya ambata alamar da ba za ta taɓa ƙarewa ba, wadda za ta sa a gane mabiyansa na gaske. “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina,” in ji shi, “idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) A wannan ayar inda Kalmar Allah ta annabta cewa kyautar yin magana a harsuna dabam-dabam za ta ƙare, ta ce: “Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.”—1 Korintiyawa 13:8.
Ƙauna ce ta farko a cikin jerin sassa guda tara na ’yar ruhu mai tsarki na Allah. (Galatiyawa 5:22, 23) Saboda haka, waɗanda suke ƙaunar Allah da gaske, kuma suke samun goyon baya daga Allah, za su nuna cikakkiyar ƙauna ga juna. Bugu da ƙari, sashe na uku na ruhun shi ne salama. Da haka, waɗanda suke da ruhu mai tsarki a yau za su manne wa salama, kuma su kauce wa nuna tsattsauran ra’ayi, wariya, da mugunta.
Kuma, ka tuna annabcin Yesu da ke rubuce a Ayyukan Manzanni 1:8. Ya annabta cewa almajiransa za su samu iko don su kasance shaidunsa “har kuma iyakan duniya.” Yesu ya kuma nuna cewa wannan aikin zai ci gaba “har ƙarshen duniya.” (Matta 28:20, King James Version) Saboda haka, wannan wa’azi da ake yi a dukan duniya zai ci gaba da kasancewa alamar da za ta sa a gane waɗanda aka ƙarfafa da ruhu mai tsarki da gaske.
Mene ne za ka ce? A cikin waɗanne rukunin mutane ne kake ganin alamar ruhu mai tsarki a yau? Su wane ne suke nuna ’yar ruhu, musamman ƙauna da salama, har hakan ya sa su sha wahala a hannun gwamnatoci domin sun ƙi su ɗauki makami a dukan duniya? (Ishaya 2:4) Su wane ne suke iya ƙoƙarinsu su guje wa ayyukan jiki, irin su zina, har ma su cire masu aika ayyukan nan da suka ƙi tuba daga cikinsu? (1 Korintiyawa 5:11-13) Su wane ne suke yin wa’azi a dukan duniya game da bisharar nan cewa Mulkin Allah ne kaɗai begen da mutane suke da shi?—Matta 24:14.
Mawallafan wannan mujallar ba sa tantamar faɗin cewa Shaidun Jehobah ne suka dace da kwatancin da Littafi Mai Tsarki ya ba da na mutanen da suke da ruhu mai tsarki. Me zai hana ka sanin su kuma ka yanke wa kanka shawara ko da gaske ne suna da goyon baya daga Allah?