Abin Da Ke Ciki
15 Ga Yuli, 2010
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA MAKONNIN:
30 ga Agusta, 2010–5 ga Satumba, 2010
Abin da Ranar Jehobah Za Ta Bayyana
SHAFI NA 3
WAƘOƘI: 133, 40
6-12 ga Satumba, 2010
“Ku Yi La’akari da Irin Mutane da Ya Kamata Ku Zama!”
SHAFI NA 7
WAƘOƘI: 61, 29
13-19 ga Satumba, 2010
Ka Sa Hannu Sosai a Yin Babban Girbi na Ruhaniya
SHAFI NA 16
WAƘOƘI: 103, 102
20-26 ga Satumba, 2010
“Ruhu Yana Binciken . . . Zurfafa na Allah”
SHAFI NA 20
WAƘOƘI: 71, 117
Manufar Talifofin Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA 1, 2 SHAFUFFUKA NA 3-11
A cikin wasiƙarsa ta biyu, manzo Bitrus ya furta damuwarsa domin Kiristocin da suke zaune a kwanaki na ƙarshe. Waɗannan talifofin biyu za su taimaka mana mu riƙa tunawa da ranar Jehobah. Za mu tattauna abin da dole ne mu guje wa da kuma abin da dole ne mu yi don mu kasance a shirye don babbar ranar Jehobah.
TALIFIN NAZARI NA 3 SHAFUFFUKA NA 16-20
Muna rayuwa a lokacin girɓi mai girma na ruhaniya. Waɗanne halaye muke bukata domin mu saka hannu sosai a aikin wa’azi? Ta yaya za mu yi iyakar ƙoƙarinmu a yanayi mai wuya? Wannan talifin zai amsa waɗannan tambayoyin.
TALIFIN NAZARI NA 4 SHAFUFFUKA NA 20-24
Wannan talifin ya tattauna abin da za mu iya yi don mu amfana sosai daga aikin da ruhun Allah yake yi don ya taimaka mana mu fahimci Kalmarsa.
A FITOWAR NAN:
‘Kada Ka Ji Tsoro Ni Zan Taimake Ka’ 12
Ka Koya wa Yaranka Su So Yin Karatu da Kuma Nazari 25
Ka Ci Gaba da ‘Mai da Hankali ga Koyarwa’ 29
Mai da Hankali Yana Kawo Sakamako Mai Kyau 32