Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 6/15 pp. 29-32
  • Jimrewa da Cin Amana na Abokin Aure

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jimrewa da Cin Amana na Abokin Aure
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ga Kanka Yadda Jehobah Yake Ganinka
  • Yadda Jehobah Yake Tanadin Ƙarfafawa
  • Yadda Wasu Za Su Iya Ba da Taimako
  • Ki Guji Son Ramawa
  • Za Ki Iya Yin Nasara!
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka Kasance Da Ra’ayi Mai Kyau Idan Kana Fuskantar Matsala A Aurenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 6/15 pp. 29-32

Jimrewa da Cin Amana na Abokin Aure

MARGARITA da maigidanta Raúl, sun yi shekaru masu yawa suna bauta wa Jehobah a matsayin masu hidima na cikakken lokaci.a Amma ba da daɗewa ba bayan da suka haifi yaronsu na farko, sai Raúl ya fara janyewa daga Jehobah. Daga baya, Raúl ya fara yin lalata kuma aka yi masa yankan zumunci daga cikin ikilisiyar Kirista. “Yayin da dukan waɗannan abubuwa suke faruwa,” in ji Margarita, “na ji kamar zan mutu. Na yi baƙin ciki sosai, kuma ban san abin da zan yi ba.”

Ba da daɗewa ba bayan da Jane ta yi aure, maigidanta ya ci amanar ƙauna da amincewa da ta yi da shi a wata hanya dabam. Ya fara zaluntar ta. “A lokaci na farko da ya naushe ni,” in ji Jane, “na yi mamaki, na ji kunya, kuma ya zubar da mutuncina. Sai ya zama cewa zai riƙa wulakanta ni, bayan haka sai ya roƙe ni in gafarta masa. Ca nake hakki na ne na Kirista kullum in gafarta kuma in mance. Na kuma yi tunanin cewa zai zama rashin aminci in gaya wa wani matsalarmu, har da dattawan ikilisiyarmu. Wannan tafarki na wulakanci da gafartawa ya ci gaba har tsawon shekaru da yawa. A dukan wannan lokaci, ina ganin akwai abin da zan iya yi don in sa maigidana ya ƙaunace ni. Daga bisani da ya bar ni da ’yarmu, sai na ji kamar na yi kuskure, da na yi ko kuma faɗi wani abu don in riƙe aurenmu.”

Kamar Margarita da kuma Jane, wataƙila ke ma kina fama da ɓacin rai, matsalar kuɗi, da kuma fama a ruhaniya don maigidanki ya ci amanar ki. Ko kuma mai yiwuwa kai maigida ne da kake fama da baƙin zuciya da kuma wahala don matarka ta ci amanarka. Babu shakka, muna rayuwa ne a “miyagun zamanu,” kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta. Wannan annabcin ya nuna cewa a “kwanaki na ƙarshe,” dangantakar iyali za ta lalace, tare da rashin ƙauna irin na dabi’a a yawancin yanayi. Wasu za su ƙaryata da’awar da suke yi na bauta wa Allah. (2 Tim. 3:1-5) Kiristoci na gaskiya ma suna fama da irin waɗannan matsalolin; saboda haka, menene zai iya taimaka maki ki jimre idan aka ci amanar ki?

Ka Ga Kanka Yadda Jehobah Yake Ganinka

Da fari, zai iya yi maka wuya ka gaskata cewa wani da kake ƙauna zai iya cin amanarka haka. Kana iya ma fara ɗora wa kanka laifi domin laifinsa ko laifinta.

Ka tuna fa cewa, har ma Yesu kamiltacce, wani da yake ƙauna kuma ya amince da shi ya ci amanarsa. Yesu ya zaɓi abokansa na kusa, manzannin, bayan da ya yi tunani tare da addu’a sosai game da batun. A lokacin, su sha biyun bayin Jehobah ne masu aminci. Saboda haka, babu shakka Yesu ya yi baƙin ciki ƙwarai lokacin da Yahuda ya zama “maci amana.” (Luk 6:12-16) Amma, Jehobah bai ɗora alhakin halayen Yahuda a kan Yesu ba.

Hakika, a yanzu babu wani abokin auren da kamiltacce ne. Mata da miji za su yi kurakurai. Mai zabura da aka hure ya faɗi gaskiya sa’ad da ya rubuta: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zab. 130:3) Ta wajen yin koyi da Jehobah, ya kamata dukan abokan aure su kasance da halin gafarta wa ajizancin juna.—1 Bit. 4:8.

Duk da haka, “kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Rom. 14:12) Idan abokin aure ya kafa tafarkin yin baƙar magana ko mugun hali, shi mai laifin ne zai kawo lissafin kansa ga Jehobah. Jehobah ya haramta mugunta da kuma baƙar magana, saboda haka babu wani dalili na nuna wa abokin aure irin wannan mugun hali na rashin ƙauna da daraja. (Zab. 11:5; Afis. 5:33; Kol. 3:6-8) A gaskiya, idan Kirista ya ci gaba da nuna fushi da rashin tuba kuma ya ƙi canjawa, za a yi shi ko ita yankan zumunci daga ikilisiyar Kirista. (Gal. 5:19-21; 2 Yoh. 9, 10) Bai kamata abokin aure ya ji cewa laifi ne ya kai ƙarar irin wannan halin da ba na Kirista ba ga dattawa. Hakika, Jehobah yana jin tausayin waɗanda ake yi wa irin wannan zaluncin.

Sa’ad da abokin aure ya yi zina, ya yi zunubi ga abokiyar aurensa da kuma Jehobah. (Mat. 19:4-9; Ibran. 13:4) Idan abokiyar aure marar laifin tana ƙoƙarin yin rayuwa daidai da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, ba ta da wani dalilin ɗora wa kanta alhakin zunubin cin amana na wanda ya yi zinan.

Ki tuna cewa Jehobah ya san yadda kike ji. Ya kwatanta kansa a matsayin mijin al’ummar Isra’ila, kuma Kalmarsa tana ɗauke da kalmomi masu taɓa zuciya da ke nuna baƙin cikin da ya ji saboda al’ummar nan ta ƙi bauta masa. (Isha. 54:5, 6; Irm. 3:1, 6-10) Ki san cewa Jehobah yana ganin hawaye da ke fita daga idanunki domin amanarki da abokin aurenki ya ci. (Mal. 2:13, 14) Ya san kina bukatan ƙarfafawa.

Yadda Jehobah Yake Tanadin Ƙarfafawa

Hanya ɗaya da Jehobah yake tanadin ƙarfafawa ita ce ikilisiyar Kirista. Jane ta samu irin wannan taimakon. “Mai kula da da’ira ya zo daidai lokacin da nake baƙin ciki sosai,” in ji Jane. “Ya san irin baƙin cikin da nake ji a sakamakon kashe aure da mai gidana ya yi. Ya yi amfani da lokaci sosai don ya taimake ni in yi tunani a kan nassosi irinsu 1 Korintiyawa 7:15. Ayoyin Littafi Mai Tsarki da kalamansa sun taimaka wajen sauƙaƙa alhakin da nake ji kuma hakan ya sa hankali na ya ɗan kwanta.”b

Margarita, da aka ambata a baya, ita ma ta fahimci cewa Jehobah yana tanadin taimako mai kyau ta wurin ikilisiyar Kirista. “Yayin da ya kasance a bayyane cewa maigidana ba ya son ya tuba,” in ji Margarita, “Na kwashi yarana biyu muka kuma ƙaura zuwa wani birni. Da muka isa, na yi hayar ɗakuna biyu. Kashegari, cike da baƙin ciki, ina cikin cire kayayyakin da ke cikin jikunanmu sai na ji an ƙwanƙwasa kofa. Ina tsammanin cewa maigidan ce da take ɗakin da ke gefen namu. Abin mamaki, sai na ga cewa ’yar’uwar da ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da uwata kuma ta taimaka wa iyalinmu koyon gaskiya ce. Ba ta yi tsammanin gani na ba don ta zo ne ta yi nazari ne da matar da ke da gidan da muke ciki. Hakan ya sa na samu sauƙi, na kasa riƙe hawaye na. Na bayyana mata yanayina, kuma muka yi kuka tare. Nan da nan ta shiri don mu halarci taro a wannan ranar. Ikilisiyar ta marabce mu, kuma dattawan suka yi shirye-shirye masu kyau don su taimaka mini in kula da bukatun ruhaniyar iyalina.”

Yadda Wasu Za Su Iya Ba da Taimako

Hakika, waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista za su iya ba da taimako a hanyoyi da yawa. Alal misali, Margarita tana bukatan ta nemi aiki. Wata iyali a cikin ikilisiyar ta ce za su taimaka wajen kula da yaranta idan suka dawo daga makaranta idan da bukata.

“Abin da na ji daɗinsa sosai,” in ji Margarita, “shi ne lokacin da ’yan’uwa maza da mata suka ba da kansu su fita hidimar fage tare da ni da yarana.” Ta wurin ba da irin wannan taimakon, waɗanda suke cikin ikilisiya suna taimakawa wajen ‘ɗaukan kayan juna’ kuma ta yin haka suna cika “shari’ar Kristi.”—Gal. 6:2.

Waɗanda suke shan wahala don zunuban waɗansu suna godiya sosai saboda taimako mai amfani da ake yi musu. Monique, wadda mijinta ya bar ta, kuma ya bar ta da bashin dala 15,000 da kuma renon yara huɗu, ta ce: “’Yan’uwana na ruhaniya maza da mata sun nuna mini ƙauna. Babu yadda zan rayu da a ce ba su taimaka mini ba. Na ji kamar Jehobah ya yi tanadin ’yan’uwa maza masu nuna ƙauna, waɗanda suka ba da kansu ga ’ya’yana. Na yi farin cikin ganin ’ya’yana sun manyanta a ruhaniya da irin wannan taimakon. Idan ina bukatar shawara, dattawa suna taimaka mini. Idan ina bukatar in yi magana da wani, ’yan’uwan suna sauraro na.” —Mar. 10:29, 30.

Hakika, aboki mai ƙauna zai fahimci lokacin da ya fi kyau kada ya ambata batun matsalar wani. (M. Wa. 3:7) “A yawancin lokaci,” in ji Margarita, “Ina jin daɗin tattaunawa da ’yan’uwa mata na sabuwar ikilisiyarmu game da aikin wa’azi, waɗanda muke nazari da su, da yaranmu, muna yin hirar komi amma ban da matsala ta. Ina farin ciki cewa sun sa na manta da abin da ya faru da ni a dā kuma sun taimaka mini in fara sabuwar rayuwa.”

Ki Guji Son Ramawa

A wasu lokatai, maimakon ɗaukan alhakin zunubin abokin aurenki, kina iya jin haushin cewa kina shan wahala sosai don laifinsa ko laifinta. Idan kika ƙyale hakan ya ci gaba, wannan haushin zai iya raunana ƙudurinki na kasancewa da aminci ga Jehobah. Alal misali, za ki iya faɗa wa gwajin neman hanyoyi rama abin da abokin aurenki ya yi maki.

Idan kika fahimci cewa a cikin zuciyarki kina son ki rama, za ki iya yin tunanin misalin Joshua da kuma Kaleb. Waɗannan mutane masu aminci sun sadaukar da ransu domin su leƙo asirin Ƙasar Alkawari. Sauran ’yan leƙen asirin sun yi rashin bangaskiya kuma suka juya mutanen daga yi wa Jehobah biyayya. Wasu Isra’ilawa sun so su jejjefi Joshua da Kaleb da duwatsu lokacin da suka yi ƙoƙarin su ƙarfafa al’ummar su kasance da aminci. (Lit. Lis. 13:25–14:10) A sakamakon halin Isra’ilawa, an tilasta wa Joshua da Kaleb su yi yawo a jeji na tsawon shekara arba’in, ba don zunubinsu ba, amma don zunuban waɗansu.

Ko da yake Joshua da Kaleb wataƙila sun ji taƙaici, amma ba su bar zunuban ’yan’uwansu ya sa su ƙiyayya ba. Sun mai da hankali ga hidimarsu ga Jehobah. A ƙarshen shekara arba’in a cikin jeji, su da Lawiyawa suka sami albarka ta wurin zama zuriyar da ta tsira kuma aka yarda ta shiga Ƙasar Alkawari.—Lit. Lis. 14:28-30; Josh. 14:6-12.

Halin rashin aminci na abokin aurenki zai iya sa ki sha wahala na dogon lokaci. Za ku iya kashe auren, har ila za ki sha wahalar motsin zuciya da kuma wahalar kuɗi bayan hakan. Maimakon barin mugun tunani ya sha kanki, ki tuna cewa Jehobah ya san yadda zai bi da waɗanda suka ƙi mizanansa da gangan, kamar yadda Isra’ilawa marasa aminci a cikin jeji suka gani.—Ibran. 10:30, 31; 13:4.

Za Ki Iya Yin Nasara!

Maimakon ki ƙyale mugun tunani ya nauyaya ki, ki cika zuciyarki da tunanin Jehobah. “Na gano cewa sauraron Hasumiyar Tsaro da Awake! da aka ɗauka a kaset ya taimaka mini in jimre,” in ji Jane. “Taro ya zama tushen ƙarfafawa sosai. Saka hannu sosai a taro ya taimaka mini in manta da matsalolina. Aikin wa’azi ya kuma taimaka mini. Ta wurin taimaka wa mutane su ƙarfafa bangaskiyarsu a kan Jehobah, na ƙarfafa bangaskiyata. Kuma kulawa da waɗanda nake nazari da su ya taimake ni in sa zuciyata a kan abubuwan da suka fi muhimmanci.”

Monique da aka ambata a baya, ta ce: “Ta wurin halartan taro a kai a kai da kuma fita hidimar fage daidai yadda zan iya, ya sa in jimre. Iyalina ta kusaci juna da kuma ga ikilisiya. Wahalar da na fuskanta ta taimaka mini in fahimci kasawa ta. An jarraba ni, amma na jimre da taimakon Jehobah.”

Ke ma za ki iya jure da irin wannan gwajin. Duk da baƙin cikin da cin amana yake jawowa, ki yi ƙoƙari ki bi hurarriyar shawarar Bulus: “Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi za mu girbe, in ba mu yi suwu ba.”—Gal. 6:9.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

b Don samun bayani dalla-dalla game ra’ayin Littafi Mai Tsarki game da rabuwa da kashe aure, ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafofi na 125-130, 219-221.

[Hoton da ke shafi na 31]

Abokan aure da aka yasar suna godiya ga waɗanda suke taimaka musu a hidimar fage

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba