Ka Samu Kāriya Tsakanin Mutanen Allah
“Zan yi maka godiya cikin babban taron jama’a.”—ZAB. 35:18.
1-3. (a) Menene zai iya sa wasu Kiristoci su faɗa cikin yanayi mai haɗari na ruhaniya? (b) A ina ne mutanen Allah za su iya samun kāriya?
SA’AD da suke hutu, Joe da matarsa sun saka abin shaƙa iska suna iyo a ƙarƙashin teku cike da kifaye kala-kala da girma dabam-dabam. Sun yi iyo da ɗan nisa don su kalli ƙarƙashin tekun. Sa’ad da suka yi iyo zuwa inda ruwan ya yi zurfi, matar Joe ta ce, “Kamar fa muna yin nisa sosai.” “Kada ki damu,” in ji Joe. “Na san abin da nake yi.” Joe ya tuna cewa ba da daɗewa ba ya soma mamaki, ‘Ina dukan kifayen suka tafi?’ Cike da tsoro sai ya ga dalilin. Daga cikin zurfin ruwan, wani kifi mai suna shark ya nufo shi. Kuma babu yadda zai yi da kifin. Sa’ad da kifin ya yi ɗan kusa da shi, sai ya juya ya ɓace.
2 Kirista yana iya yin sha’awar abubuwan jan hankali na duniyar Shaiɗan, kamar su nishaɗi, aiki, dukiya, har ya kasa fahimtar cewa ya soma yin nisa cikin yanayi mai haɗari ba. “Abin da na fuskanta ya sa na yi tunani game da waɗanda muke tarayya da su,” in Joe, dattijo Kirista. “Ka yi iyo inda babu haɗari kuma mai daɗi, wato, a cikin ikilisiya!” Kada ka yi iyo cikin ruwa mai zurfi, inda za ka kaɗaita a ruhaniya kuma ka jefa kanka cikin haɗari. Idan ka samu kanka a wajen, ka juya nan da nan ka nufi inda ‘babu haɗari.’ Idan ba haka ba, kana iya jefa dangantakarka da Jehobah cikin haɗari.
3 A yau, duniya wuri ne mai haɗari ga Kiristoci. (2 Tim. 3:1-5) Shaiɗan ya san cewa kwanakinsa sun kusan ƙarewa, kuma yana neman ya halaka waɗanda ba sa a faɗake. (1 Bit. 5:8; R. Yoh. 12:12, 17) Amma, muna da kāriya. Jehobah ya yi wa mutanensa mafaka ta ruhaniya, wato, ikilisiyar Kirista.
4, 5. Yaya mutane da yawa suke ji game da rayuwarsu ta nan gaba, kuma me ya sa?
4 Al’ummar da muke cikinta tana ba da kāriya kaɗan kawai, a zahiri ko kuma a motsin zuciya. Mutane da yawa suna jin cewa aikata laifi, mugunta, tsadar abubuwa, har ma batutuwa na mahalli suna yi wa kāriyarsu na zahiri barazana. Dukanmu muna fuskantar matsalolin tsufa da rashin lafiya. Dukan waɗanda suke da aiki, gidaje, isashen kuɗi, da kuma koshin lafiya suna iya yin tunanin ko har yaushe za su ci gaba da more hakan.
5 Mutane da yawa ba sa iya samun kwanciyar rai. Abin baƙin ciki, mutane da yawa da suke sa ran cewa za su samu salama da gamsuwa a aure da kuma cikin iyali sun ga cewa abin da suke zato bai faru ba. A batun biyan bukatun mutum na ruhaniya, mutane da yawa masu zuwa coci sun rikice, suna shakkar amfanin ja-gorar da suka samu. Suna jin hakan ne musamman idan suka duba mummunan halaye da koyarwa da ba na nassi ba da ke fita daga bakin shugabannan addinansu. Saboda haka, mutane da yawa suna jin cewa zaɓin da suke da shi kaɗai shi ne su sa begen su a kimiyya ko hali da tunanin kirki na ’yan adam. Ba abin mamaki ba ne, cewa mutane da suka kewaye mu ba su da kwanciyar rai ko kuma sun fi son kada su yi tunani sosai game rayuwarsu ta nan gaba.
6, 7. (a) Me ya sa ra’ayin waɗanda suke bauta wa Allah ya bambanta da na waɗanda ba sa bauta masa? (b) Menene za mu bincika?
6 Wannan bambancin ra’ayi ne mai girma tsakanin waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista da kuma waɗanda ba sa ciki! Ko da yake mu mutanen Jehobah muna fuskantar irin batutuwa da matsaloli masu yawa da maƙwabtanmu suke fuskanta, yadda muke bi da batun ya bambanta. (Karanta Ishaya 65:13, 14; Malakai 3:18.) Me ya sa? Domin mun samu bayani mai gamsarwa a cikin Littafi Mai Tsarki game da yanayin da ’yan Adam suka samu kansu a ciki, kuma an shirya mu mu bi da ƙalubale da matsaloli na rayuwa. Saboda haka, ba ma damuwa ainun game da nan gaba. Bauta wa Jehobah da muke yi yana kāre mu daga koyarwan ƙarya game da nassi, ayyukan lalata, da sakamakonsu. Shi ya sa waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista suke samun kwanciyar hankali da wasu ba su da shi.—Isha. 48:17, 18; Filib. 4:6, 7.
7 Akwai wasu misalai da za su iya taimaka mana mu yi tunani a kan kāriya da waɗanda suke bauta wa Jehobah suke morewa akasin waɗanda ba sa bauta masa. Waɗannan misalai suna iya motsa mu mu bincika ra’ayinmu da ayyukanmu kuma mu yi tunani a kan ko muna bukatan mu ƙara bin shawarar Allah sosai, wadda aka yi don ta kāre mu.—Isha. 30:21.
“Saura Kaɗan Takawata ta Zame”
8. Menene bayin Jehobah a koyaushe suke yi?
8 Tun daga farkon tarihin ’yan Adam, waɗanda suka zaɓi su bauta wa Jehobah da kuma yi masa biyayya sun guji yin tarayya na kud da kud da waɗanda ba sa bauta masa. Hakika, Jehobah ya nuna cewa ƙiyayya za ta kasance tsakanin masu bauta masa da waɗanda suke bin Shaiɗan. (Far. 3:15) Domin sun manne wa ƙa’idodin Allah, mutanen Allah sun aikata dabam daga waɗanda suka kewaye su. (Yoh. 17:15, 16; 1 Yoh. 2:15-17) Ɗaukan irin wannan matakin bai da sauƙi a kowane lokaci. Hakika, wasu cikin bayin Jehobah a wani lokaci sun yi shakkar hikimar bin tafarkin rayuwa na sadaukar da kansu.
9. Ka kwatanta faman da marubucin Zabura ta 73 ya fuskanta.
9 Ɗaya daga cikin bayin Jehobah da ya soma mamakin ko ya tsai da shawarwari masu kyau shi ne marubucin Zabura ta 73, wataƙila ɗaya cikin zuriyar Asaph ne. Mai zaburar ya yi tambaya a kan abin da ya sa miyagu sau da yawa suke yin nasara, farin ciki, da ni’ima, yayin da wasu da suke ƙoƙartawa su bauta wa Allah suke shan jarrabobi da wahala.—Karanta Zabura 73:1-13.
10. Me ya sa batutuwan da mai zabura ya ta da suke da muhimmanci a gare ka?
10 Ka taɓa samun kanka kana irin tambayoyi da mai zabura ya rubuta? Idan haka ne, ba ka bukatan ka ji kana da laifi ko kuma ka yi tunanin cewa bangaskiyarka ta soma raguwa. Hakika, bayin Jehobah da yawa, har da wasu da Jehobah ya yi amfani da su wajen rubuta Littafi Mai Tsarki, sun yi irin wannan tunanin. (Ayu. 21:7-13; Zab. 37:1; Irm. 12:1; Hab. 1:1-4, 13) Hakika, dole ne dukan waɗanda suke son su bauta wa Jehobah su yi tunani sosai a kan wannan tambayar kuma su amince da amsarta: Bauta wa Allah da yi masa biyayya su ne abu mafi kyau da ya kamata mu yi? Hakan ya shafi batun da Shaiɗan ya ta da a lambun Adnin. Yana da muhimmanci ga tambayar da dukan mutane suke yi game da ikon mallaka na Allah. (Far. 3:4, 5) Saboda haka, yana da kyau dukanmu mu bincika batun da mai zabura ya ta da. Ya kamata ne mu yi kishin miyagu da kamar suna rayuwarsu babu matsala? Ya kamata ne mu “zame” daga bauta wa Jehobah kuma mu yi koyi da su? Ainihin abin da Shaiɗan zai so mu yi ke nan.
11, 12. (a) Yaya mai zabura ya sha kan shakkarsa, kuma menene wannan ya koya mana? (b) Menene ya taimaka maka ka kai ga irin kammalawar mai zabura?
11 Menene ya taimaka wa mai zabura ya sha kan shakkarsa? Ko da yake ya yarda cewa ya kusan zamewa daga adalci, ra’ayinsa ya canja sa’ad da ya shiga “wuri mai-tsarki na Allah,” wato, sa’ad da ya yi cuɗanya da mutane masu ruhaniya a mazauni ko haikalin Allah kuma ya yi bimbini game da nufe-nufen Allah. Sai ya kasance a bayyane ga mai zabura cewa ba ya son sakamakon abin da zai sami miyagu. Ya ga cewa tafarkinsu da zaɓinsu a rayuwa ya saka su a kan “wurare masu-santsi.” Mai zabura ya lura cewa dukan waɗanda suke barin Jehobah, babu shakka ƙarshensu zai zo da “razaizani,” yayin da Jehobah zai tallafa wa waɗanda suke bauta masa. (Karanta Zabura 73:16-19, 27, 28.) Babu shakka ka ga gaskiyar wannan furcin. Yin rayuwa don kanmu ba tare da daraja dokar Allah ba yana iya yin kyau a gaban mutane da yawa, amma ba za a iya guje wa mugun sakamakon irin wannan tafarki ba.—Gal. 6:7-9.
12 Menene kuma muka koya daga abin da ya faru da mai zabura? Ya samu kāriya da hikima tsakanin mutanen Allah. Ya soma tunanin kirki sa’ad da ya tafi wurin da ake bauta wa Jehobah. Hakazalika a yau, za mu samu mashawarta masu hikima kuma mu more abinci na ruhaniya mai kyau a taron ikilisiya. Shi ya sa, Jehobah ya gaya wa bayinsa su halarci taron Kirista. A wajen ne za su sami ƙarfafawa kuma za a motsa su su aikata da hikima.—Isha. 32:1, 2; Ibran. 10:24, 25.
Ka Zaɓi Abokanka da Kyau
13-15. (a) Menene ya sami Dinah, menene wannan ya nuna? (b) Me ya sa tarayya da Kiristoci masu bi kāriya ne?
13 Dinah, ’yar Yakubu misali ce na wadda ta shiga cikin matsala mai tsanani domin tana tarayya da abokai ’yan duniya. Labarinta da ke cikin littafin Farawa ya gaya mana cewa ta saba yin tarayya da matan Kan’aniyawa matasa a wurin da iyalinta ke da zama. Kan’aniyawa ba su da mizanan ɗabi’a mai girma kamar masu bauta wa Jehobah. Akasin haka, abin da ’yan tonan ƙasa suka samu ya nuna cewa tafarkin Kan’aniyawa ya sa ƙasarsu ta cika da bautar gunki, lalata, bautar jima’i na ƙazanta, da mugunta. (Fit. 23:23; Lev. 18:2-25; K. Sha 18:9-12) Ka tuna sakamakon tarayyar Dinah da waɗannan mutanen.
14 Wani mutumin garin, mai suna Shechem, da aka kwatanta a matsayin wanda “ana ba shi girma gaba da dukan gidan ubansa,” ya ga Dinah “sai ya ɗauke ta, ya kwana da ita, ya bāta ta.” (Far. 34:1, 2, 19) Wannan bala’i ne! Kana ganin Dinah ta taɓa tunanin cewa irin wannan abin zai iya samun ta? Wataƙila tana biɗan abota ne da matasan garin, waɗanda take ganin ba za su cuce ta ba. Amma, an ruɗi Dinah sosai.
15 Menene wannan labarin ya koya mana? Babu yadda za mu yi tarayya da marasa bi kuma mu yi tunanin cewa ba abin da zai same mu. Nassosi ya faɗi cewa “zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Kor. 15:33) A wata sassa kuma, tarayya da mutanen da suke bin imaninka, mizanan ɗabi’a mai girma, da kuma ƙaunarka ga Jehobah zai kāre ka. Irin wannan tarayya mai kyau zai ƙarfafa ka ka aikata da hikima.—Mis. 13:20.
An “Wanke Ku”
16. Menene manzo Bulus ya faɗa game da wasu a cikin ikilisiyar Koranti?
16 Ikilisiyar Kirista ta taimaka wa mutane da yawa su tsabtace kansu daga ayyukan ƙazanta. Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta farko zuwa ga ikilisiyar da ke Koranti, ya yi magana a kan canje-canjen da Kiristocin da suke wajen suka yi don su yi rayuwa da ta jitu da mizanan Allah. Wasu a dā mazinata ne, masu bautar gumaka, ’yan daudu, ɓarayi, masu yin maye, da sauransu. Bulus ya gaya musu cewa an “wanke ku.”—Karanta 1 Korantiyawa 6:9-11.
17. Ta yaya yin rayuwa daidai da mizanan Littafi Mai Tsarki ya canja rayuwar mutane da yawa?
17 Mutane marasa bangaskiya ba su da ƙa’idodin da ke yi musu ja-gora. Suna kafa tafarkinsu, ko kuma su bi hanyoyin lalata na mutanen da suka kewaye su, kamar yadda wasu Korantiyawa na dā suka yi kafin su zama masu bi. (Afis. 4:14) Amma, cikakken sani na Kalmar Allah da nufe-nufensa, suna da ikon canja rayuwar dukan waɗanda suka bi abin da ke cikin Nassosi. (Kol. 3:5-10; Ibran. 4:12) Mutane da yawa a yau da suke cikin ikilisiyar Kirista za su iya gaya maka cewa kafin su koyi mizanan adalci na Jehobah da kuma amince da ita, suna rayuwa ne da suka ga dama. Duk da haka, ba su samu gamsuwa da farin ciki ba. Sa’ad da suka soma tarayya da mutanen Allah da kuma yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kaɗai ne suka samu salama.
18. Menene wata matashiya ta fuskanta, menene hakan ya nuna?
18 Akasin haka, wasu da a dā suka zaɓi su bar ikilisiyar Kirista suna nadama sosai game da shawararsu. Wata ’yar’uwa da za mu kira Tanya ta bayyana cewa “na san gaskiya sa’ad da nake girma,” amma sa’ad da ta kai ’yar shekara sha shida ta bar ikilisiya don ta “biɗi abubuwan jan hankali na duniya.” Cikin shege da zubar da ciki suna cikin sakamakon da ta samu. Yanzu ta ce: “Shekara uku da na yi ba na cikin ikilisiya sun jawo mini baƙin cikin da ba zan taɓa mantawa ba. Wani abin da ya ci gaba da damuna shi ne jaririna da na kashe a cikin cikina. . . . Ina son in gaya wa dukan matasan da suke fatan su ‘ɗanɗana’ duniya ko na ɗan lokaci: ‘Kada ku kuskura!’ Kuna iya jin daɗinsa da farko, amma ƙarshen bai da kyau. Duniya ba ta da abin da za ta ba da sai baƙin ciki. Na san hakan domin na ɗanɗana. Ku zauna a ƙungiyar Jehobah! Ita kaɗai ce hanyar rayuwar da za ta kawo farin ciki.”
19, 20. Wace kāriya ce ikilisiyar Kirista take bayarwa, kuma ta yaya?
19 Ka yi tunanin abin da zai same ka idan ka bar mahalli na kāriya na ikilisiyar Kirista. Mutane da yawa da suka tuna irin rayuwar banza da suka yi kafin su karɓi gaskiya, ba sa ma son su tuna hakan. (Yoh. 6:68, 69) Za ka iya ci gaba da samun kwanciyar rai da kāriya daga matsaloli da kaito da ke ko’ina a duniyar Shaiɗan ta wajen kasancewa kusa da ’yan’uwanka Kiristoci. Yin cuɗanya da su da kuma halartan taron ikilisiya a kai a kai zai ci gaba da tuna maka hikima na mizanan adalci na Jehobah kuma zai ƙarfafa ka ka yi rayuwar da ta jitu da su. Kana da dukan dalilin ‘yi wa Jehobah godiya cikin babban taron jama’a,’ kamar yadda mai zabura ya yi.—Zab. 35:18.
20 Hakika, don dalilai dabam-dabam, dukan Kiristoci sukan fuskanci lokacin da kasancewa da aminci na Kirista yake da wuya. Wataƙila abin da suke bukata kawai shi ne wani ya nuna musu abin da ya dace da za su yi. Menene kai da kuma dukan waɗanda suke cikin ikilisiya za ku yi don ku taimaka wa ’yan’uwa masu bi a irin wannan lokacin? Talifi na gaba zai tattauna yadda za ku ci gaba da yi wa ’yan’uwanku ‘ta’aziya da kuma gina su.’—1 Tas. 5:11.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene muka koya daga labarin marubucin Zabura ta 73?
• Menene abin da ya samu Dinah ya koya mana?
• Me ya sa za mu samu kāriya a cikin ikilisiyar Kirista?
[Hotuna da ke shafi na 7]
Ka yi iyo inda babu haɗari; ka kasance cikin ikilisiya!