Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/1 pp. 18-20
  • Yin Renon Yara Don Su Zama Nagargaru

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Renon Yara Don Su Zama Nagargaru
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Iyaye Ku Kāre Kyautarku Mai Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ku Koya Wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/1 pp. 18-20

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Yin Renon Yara Don Su Zama Nagargaru

George:a “Hakan na faruwa kowanne yamma. Michael, ɗana mai shekara huɗu, ya watsar da kayayyakin wasansa ko’ina a cikin gida. Na ƙoƙarta ya kwashe su kafin ya yi barci. Amma sai Michael ya yi fushi, ya soma yin ihu kuma ya ci gaba da rikitar da abubuwa. A wasu lokatai raina yana ɓacewa har in daka masa tsawa, amma hakan yana daɗa ɓata mana rai ne. Ina son lokacin barci ya kasance na farin ciki. Saboda haka na ƙyale shi kawai kuma na kwashe abin da kaina.”

Emily: “Matsalar ta soma ne sa’ad da ’yata Jenny, ’yar shekara sha uku, ba ta fahimci aikin da malamarta ta ba ta a makaranta ba. Jenny ta yi kuka na tsawon awa ɗaya sa’ad da ta dawo daga makaranta. Na ƙarfafata ta nemi taimako a makaranta, amma Jenny ta faɗi cewa malamarta muguwa ce, saboda haka tana tsoron yi mata magana. Cike da fushi, na so in je makarantar in ci mutuncin malamar. Na yi tunanin cewa babu wacce ta isa ta takura wa ’yata!”

KANA jin yadda George da Emily suka ji kuwa? Kamar waɗannan iyayen, iyaye da yawa ba sa farin cikin ganin yaransu suna fama da wata matsala ko baƙin ciki. Dukan iyaye suna son su kāre yaransu. Amma, yanayin da aka bayyana a sama ya ba waɗannan iyayen zarafin su koya wa yaransu darassi mai muhimmanci game da hakki. Hakika, darussa da yaro mai shekara huɗu da kuma yarinya mai shekara sha uku za su koya ya bambanta.

Gaskiyar ita ce, ba za ka riƙa kasancewa da yaronka a kowane lokaci ba don ka kāre shi daga matsalolin rayuwa. Daga baya, yaro zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa kuma zai “ɗauki kayan kansa” na hakki. (Galatiyawa 6:5; Farawa 2:24) Don yara su iya kula da kansu, ya kamata iyaye su mai da hankali ga koya musu su zama mutane marar son kai, masu kula kuma masu kan gado. Wannan ba ƙaramin aiki ba ne!

Abin farin ciki, Yesu abin koyi ne mai kyau ga iyaye ta yadda ya bi da almajiransa da kuma yadda ya koyar da su. Yesu ba shi da yara. Amma makasudinsa na zaɓan almajiransa da kuma koyar da su shi ne ya ƙarfafasu su ci gaba da yin aikin, ko bayan ya koma sama. (Matta 28:19, 20) Abin da Yesu ya cim ma ya yi daidai da makasudin da kowanne iyaye suke son su cim ma na samun yaran kirki. Ka yi la’akari da fasaloli uku na misalin da Yesu ya kafa wa iyaye.

Ku Kafa Wa Yaranku “Kwatanci” Gab da ƙarshen rayuwarsa, Yesu ya ce wa almajiransa: “Na yi muku kwatanci, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi muku.” (Yohanna 13:15) Hakazalika, iyaye suna bukatan su bayyana kuma su nuna ta halinsu ainihin ma’anar kasancewa mutumin kirki.

Ka tambayi kanka: ‘Ina yawan maganar kula da hakkoki na a hanya mai kyau kuwa? Ina ambata gamsuwar da nake samu daga yi wa wasu ayyuka? Ko kuwa ina yawan yin gunaguni da kuma kwatanta kaina da waɗanda suke kamar dai ba su da matsala a rayuwa?’

Hakika, babu mutum kamiltacce. Dukanmu mukan ji cewa abubuwa sun yi mana yawa a wasu lokatai. Amma wataƙila misalinka ne hanya mafi muhimmanci na taimaka wa yaranka su ga muhimmanci da amfanin kasancewa da hali mai kyau.

GWADA WANNAN: Idan zai yiwu, ka riƙa kai yaronka wurin aiki a wasu lokatai don ka nuna wa shi ko ita abin da kake yi don tallafawa iyalin da kuɗi. Tare da yaronka, ka taimaka wa wani da ke bukatan taimako. Bayan hakan, ka tattauna farin cikin da ka samu daga yin wannan aikin.—Ayyukan Manzanni 20:35.

Zatonka Ya Kasance Daidaitacce Yesu ya fahimci cewa zai ɗauki lokaci kafin almajiransa su ɗauki matsayi da hakkokin da yake so. Akwai lokacin da ya ce musu: “Ina da sauran zance da yawa da zan yi maku tukuna, amma ba ku iya ku ɗauke su yanzu ba.” (Yohanna 16:12) Yesu bai ce wa almajiransa nan take cewa su yi wani abu da kansu ba. Maimakon haka, ya ɗauki lokaci sosai yana koya musu abubuwa da yawa. A lokacin da ya ga cewa sun isa ne Yesu ya tura almajiransa su kaɗai.

Hakazalika, wawanci ne iyaye su ce yaransu su soma aikin manya kafin su cancanci yin hakan. Duk da haka, yayin da yara suke girma, ya kamata iyaye su san irin ayyuka da hidimomin da ya dace da su. Alal misali, iyaye suna bukatan su koya wa yaransu su riƙa tsabtace kansu, tsabtace ɗakinsu, kada su riƙa makara, kuma su riƙa yin manejin kuɗi sosai. Sa’ad da yaro ya soma makaranta, iyaye suna bukatan su sa ɗansu ko ’yarsu ta ɗauki aikin makaranta a matsayin hakki mai muhimmanci da shi ko ita ya kamata ta kula da shi.

Ba hakkoki kaɗai iyaye za su riƙa ba yaransu ba. Wajibi ne su taimaka wa yaron don ya yi nasara a ƙoƙarce-ƙoƙarcensa. George, mahaifin da aka ambata da farko, ya fahimci cewa ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Michael ya yi fushi game da kwashe kayayyakin wasansa shi ne aikin ya yi masa yawa. “Maimakon in daka wa Michael tsawa don ya kwashe kayayyakin wasansa,” in ji George, “Na yi ƙoƙarin koya masa yadda zai kwashe su.”

Menene ainihin abin da ya yi? “Da farko,” in ji George, “Na keɓe ainihin lokacin kwashe kayayyakin wasan a kowane dare. Bayan hakan, ni da Michael muna yin aikin tare, ta wajen somawa da ɓangare ɗaya na ɗakin. Na sa yin aikin ya zama abin farin ciki, har ma na mai da aikin kamar gasa don ganin wanda zai riga gamawa. Ba da daɗewa ba, wannan ya zama abin da muke yi kullum kafin mu yi barci. Na yi wa Michael alkawarin cewa idan ya yi aikin da sauri, zan ba shi ƙarin tatsuniya kafin ya yi barci. Amma idan bai yi aikin da sauri ba, zan rage tsawon tatsuniyar.”

GWADA WANNAN: Ka bincika abin da kowanne cikin yaranka zai iya yi don kome ya tafi daidai a gidanka. Ka tambayi kanka, ‘Shin akwai abubuwan da har ila nake yi wa yarana da za su iya yi da kansu?’ Idan haka ne, ka yi aiki tare da yaranka har sai ka tabbata cewa za su iya yin aikin da kansu. Ka sa su san cewa akwai sakamako, mai kyau ko marar kyau, bisa ga yadda suka yi aikinsu. Sai ka hore su ko ka ba su ladan.

Ka Ba da Ainihin Umurni Kamar kowane malami mai kyau, Yesu ya san cewa hanya mafi kyau na koyon wani abu shi ne ta yin abin. Alal misali, sa’ad da Yesu ya ga cewa lokaci ya yi, ya aiki almajiransa “biyu biyu a gabansa zuwa kowane birni da kowane wurin da ya ke shirin zuwa da kansa.” (Luka 10:1) Amma, bai tura su su yi abin da suka ga dama ba. Kafin ya aike su, ya gaya musu ainihin abin da za su yi. (Luka 10:2-12) Sa’ad da almajiran suka dawo kuma suka ba shi rahoton nasarar da suka yi, Yesu ya yaba musu kuma ya ƙarfafa su. (Luka 10:17-24) Ya furta gaba gaɗin da yake da shi a iyawarsu da kuma amincewarsa.

Sa’ad da yaranka suka fuskanci hakkoki masu wuya, menene kake yi? Kana neman ka kāre yaranka daga abubuwan da suke jin tsoro, kana neman ka tsare su daga gazawa? Abin zai fara zuwa zuciyarka shi ne ka “ceci” yaronka ko ka ɗauki nauyin da kanka.

Amma ka yi la’akari da wannan: A duk lokacin da ka “ceci” yaronka ko ta yaya, menene kake gaya musu? Kana nuna ne cewa ka amince da su kuma ka yarda da ingancinsu? Ko dai kana gaya musu ne cewa har yanzu kana ganinsu kamar jariran da suke bukatan su dogara da kai a duk wani abin da za su yi?

Alal misali, yaya Emily, wadda aka ambata ɗazun, ta bi da matsalar ’yarta? Maimakon ta sa baki, ta ƙyale Jenny ta je ta yi wa malamar magana da kanta. Emily da Jenny suka rubuta tambayoyin da Jenny za ta kai makaranta. Bayan haka, suka tattauna sa’ad da za ta yi wa malamar magana. Sun ma gwada yadda tattaunawar za ta kasance. “Jenny ta yi gaba gaɗi don ta yi wa malamar magana,” in ji Emily, “kuma malamar ta ƙarfafa ta don gaba gaɗin da ta yi. Jenny ta yi alfaharin kanta sosai, kuma ni ma ina ji da ita sosai.”

GWADA WANNAN: Ka rubuta ƙalubalen da yaronka yake fuskanta a yanzu. A gaban ƙalubalen, ka rubuta abin da za ka iya yi don taimaka wa yaronka ya sha kan ƙalubalen ba tare da “ceto” shi ko ita ba. Kai da yaronka ku gwada matakan da ake bukatan a ɗauka don shawo kan ƙalubalen. Ka furta tabbacinka ga iyawar yaron.

Idan kana kāre yaranka daga abubuwa masu wuya a kullum, za ka iya rage iyawarsu na cim ma ƙalubalen rayuwa. Maimakon hakan, ka ƙarfafa yaranka ta wajen koya musu karɓar hakki tun suna yara. Yin hakan zai zama baiwa mafi tamani da za ka iya ba su.

[Hasiya]

a An canja sunaye.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ Ina da daidaitaccen zato game da yara na kuwa?

▪ Ina gaya musu da kuma nuna musu abin da ya kamata su yi don su yi nasara kuwa?

▪ Yaushe rabona da in ƙarfafa ko yabawa yaro na?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba