Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/1 p. 21
  • Allah Zai Iya Yin Nadama Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Zai Iya Yin Nadama Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Bauta Ba Tare da Yin Da-na-sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Mutanen Isra’ila Sun Shiga Ka’anan
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/1 p. 21

Ka Kusaci Allah

Allah Zai Iya Yin Nadama Kuwa?

ALƘALAWA 2:11-18

A MATSAYIN ’yan Adam ajizai, muna yin nadama a wasu lokatai. Alal misali, za mu iya yin da na sani bayan mun san cewa mun yi kuskure. Abin mamaki, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana sake nufinsa. Amma za ka ce, ‘Allah kamiltacce ne.’ ‘Ba ya yin kuskure!’ A wace hanya ce Allah yake sake nufinsa? Amsar za ta iya taimaka mana mu fahimci wani abu mai ban al’ajabi: Jehobah yana da juyayi, kuma abubuwan da muka yi za su iya shafan yadda yake ji. Ka yi la’akari da kalaman da suke rubuce a Alƙalawa 2:11-18.

Littafin Alƙalawa da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labarai na mawuyacin lokaci a tarihin Isra’ila. Al’ummar tana zaune a Kan’anan, ƙasar da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari. Ƙarnuka da yawa bayan hakan, za a iya bayyana tarihin Isra’ila da tafarkin rayuwa da ta ƙunshi fuskoki huɗu: gujewa, zalunci, roƙo, da ceto.a

Gujewa. Don rinjayar Kan’aniyawa, Isra’ila ta “bar bin Ubangiji” kuma suka soma bin wasu alloli, a taƙaice suka “bauta ma Baal da Ashtaroth.”b Irin wannan gujewar tana nufin yin ridda. Shi ya sa Isra’ilawa suka “cakuni Ubangiji,” Allahn da ya ceci Isra’ila daga ƙasar Masar!—Ayoyi ta 11-13; Alƙalawa 2:1.

Zalunci. Don fushi mai adalci, Jehobah yana janye kāriyarsa daga mutanen da suka juya masa baya. Sa’annan Isra’ilawa za su faɗa cikin “hannun abokan gābansu,” waɗanda za su zo su kwashe dukan abubuwan da ke ƙasar.—Aya ta 14.

Roƙo. Sa’ad da suke fuskantar wahala sosai, Isra’ilawa za su yi nadama saboda tafarkinsu marar kyau kuma za su yi kira ga Allah don ya taimaka musu. Furcin nan ‘nishi a hannun waɗanda suka tsananta masu’ wataƙila yana nufin roƙon da suke yi. (Aya ta 18) Roƙon Allah abu ne da suka saba yi. (Alƙalawa 3:9, 15; 4:3; 6:6, 7; 10:10) Menene Allah ya yi?

Ceto. Jehobah zai saurari kukan Isra’ila kuma “ya sāke nufinsa.” Kalmar Ibrananci da aka fassara ‘sāke nufi’ tana nufin “mutum ya sāke shawara ko niyya.” Wani aikin bincike ya ce: “A sakamakon nishin da suke yi, Jehobah ya canja nufinsa na yin horo zuwa na yin ceto.” Domin tagomashinsa, Jehobah zai “tayas masu da mahukunta” waɗanda za su ceci mutanensa daga maƙiyansu.—Aya ta 18.

Ka lura da bin da ya sa Allah ya sāke nufinsa, ko kuma ya canja ra’ayinsa kuwa? Saboda tuba da mutanensa suka yi. Ka yi tunanin wannan: Uba mai ƙauna zai iya yi wa yaronsa da ya yi laifi horo, wataƙila ta wajen hana shi wasu abubuwa. Amma da zarar ya ga cewa yaron ya tuba da gaske, uban zai yanke shawarar kawar da horon.

Menene muka koya game da Jehobah daga wannan labarin? Ko da yake yin zunubi da gangan yana ba shi haushi, amma tuba yana sa ya nuna tausayi. Sanin cewa abin da muka yi zai iya shafan yadda Allah yake ji, ya kamata ya sa mu yin tunani sosai. Zai dace ka koyi yadda za ka ‘faranta zuciyar’ Jehobah, ko ba haka ba? (Misalai 27:11) Ba za ka taɓa yin da na sani ba.

[Hasiya]

a Alƙalawa 2:11-18 tana cikin taƙaitawa na farko da ta bayyana irin halayen Isra’ilawa, wanda aka ba da cikakken labarinta a surori da ke gaba.

b Baal shi ne allan Kan’aniyawa da aka fi sani, kuma Ashtaroth allahiya ce da aka ce matar Baal ce.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba