Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 3/15 pp. 30-32
  • Ka Kasance da “Tsabtar Zuciya” A Waɗannan Miyagun Zamanu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance da “Tsabtar Zuciya” A Waɗannan Miyagun Zamanu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Kasancewa da “Tsabtan Zuciya” Yake Nufi?
  • Kasancewa da “Tsabtan Zuciya” Ba Shi da Sauƙi
  • Sa’ad da Muke Fuskantar Sha’awoyi na Jiki
  • “Tsabtar Zuciya” Sa’ad da Muke Fuskantar Gwaji
  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehobah Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Kiyaye Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 3/15 pp. 30-32

Ka Kasance da “Tsabtar Zuciya” A Waɗannan Miyagun Zamanu

“BABU wanda zai yi musun cewa kasancewa da tsabta ta ɗabi’a matsala ce a cikin Coci a yau.” Vittorio Messori, wani manemin labarai na Katolika ne ya faɗi hakan game da mugun labari na lalata da ya shafi Coci a Italiya a kwanan nan. “Kuma ba za a magance wannan matsalar ba ta wajen kawar da dokar da ta hana limamai yin aure domin kashi tamanin na matsalar ya shafi ’yan luɗu, wato, firistoci da suke lalata da maza da yara maza.”—La Stampa.

Babu shakka, mugunta da ke ko’ina alama ce na waɗannan “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamanin. (2 Tim. 3:1-5) Kamar yadda labarai suka nuna, taɓarɓarewar ɗabi’a yana shafan mutane gabaki ɗaya har da waɗanda suke kiran kansu mutanen Allah. Lalatacciyar zuciyarsu marar tsarki tana motsa su su riƙa yin ayyukan lalata. (Afis. 2:2) Da dalili mai kyau, Yesu ya yi kashedi cewa “daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, alfasha.” (Mat. 15:19) Amma, Jehobah Allah yana son bayinsa su ƙaunaci “tsabtar zuciya.” (Mis. 22:11) Yaya Kirista zai kasance da tsabtar zuciya a waɗannan miyagun zamanu?

Menene Kasancewa da “Tsabtan Zuciya” Yake Nufi?

A cikin Littafi Mai Tsarki, sau da yawa ana amfani da “zuciya” a azanci na alama. Wata majiya ta ce, kalma ta Littafi Mai Tsarki na zuciya tana nuna “can cikin mutum” kuma sashe ɗaya ne na mutum da Allah yake dubawa, inda mutum yake kafa dangantakarsa da Allah, da ke nuna hali na ɗabi’a.” Zuciya tana nuna ainihin abin da muke a ciki. Kamar yadda majiyar da aka yi ƙaulinta a baya ta nuna, zuciya ce Jehobah yake bincika kuma ita yake so a cikin bayinsa.—1 Bit. 3:4.

A cikin Littafi Mai Tsarki, “tsarki” da “tsabta” suna iya nuna abin da ke da tsabta a azanci na zahiri. Amma ana amfani da kalaman ne sa’ad da ake nuni ga abin da ba a ɓata ba, wanda ba a gauraya ba, ko wanda ba a gurɓata ba, a azanci na ɗabi’a da na addini. A Huɗuba Bisa Dutse, Yesu ya sanar: “Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya: gama su za su ga Allah.” Yana nuni ga waɗanda suke da tsabta a ciki. (Mat. 5:8) Ƙaunarsu, sha’awoyinsu, da muradinsu suna da tsarki. Da yake ƙauna da godiya ne yake motsa su, suna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu, da gaske, ba tare da riya ba. (Luk 10:27) Kana son ka kasance da tsabta a wannan azancin, ko ba haka ba?

Kasancewa da “Tsabtan Zuciya” Ba Shi da Sauƙi

Bawan Jehobah yana bukatan ya kasance da “hannuwa masu-tsabta” da kuma “zuciya mai-tsarki.” (Zab. 24:3, 4) Amma, a yau yana daɗa yi wa bayin Allah wuya su kasance da “zuciya mai-tsarki.” Shaiɗan da duniyar da ke ƙarƙashin sarautarsa da kuma jikinmu ajizi, suna matsa mana sosai don su ware mu daga Jehobah. Don mu ƙi waɗannan matsi, yana da muhimmanci sosai mu yi ƙaunar “tsabtar zuciya” kuma mu ƙuduri aniyar riƙe ta. Hakan zai kāre mu kuma ya taimaka mana mu ci gaba da zama abokan Allah. Ta yaya za mu kasance da tsabtar zuciya?

A Ibraniyawa 3:12, an yi mana gargaɗi: “Ku yi lura fa, ’yan’uwa, kada wataƙila mugunyar zuciya ta rashin bangaskiya ta kasance a cikin kowane ɗayanku, da za ku ridda daga Allah mai-rai.” Ba za mu ci gaba da kasancewa da “tsabtar zuciya” ba idan muka kasance da “zuciya ta rashin bangaskiya.” Waɗanne ra’ayoyi ne Shaiɗan Iblis ya yaɗa don ya raunana bangaskiyarmu ga Allah? Wannan ya haɗa da ra’ayin bayyanau, ra’ayin cewa babu mizani na gaske game da abu mai kyau da marar kyau, da kuma shakkar cewa Allah ne ya hure Nassosi Masu Tsarki. Kada mu ƙyale irin waɗannan mugun tunani su shafe mu. (Kol. 2:8) Karanta Littafi Mai Tsarki kullum da kuma yin bimbini sosai su ne kāriya na musamman a kan waɗannan hari. Cikakken sani na Kalmar Allah zai ƙarfafa ƙaunarmu ga Jehobah da kuma fahiminmu na yadda yake bi da mutane. Muna bukatan irin wannan ƙauna da godiya idan muna son mu ƙi tunanin ƙarya kuma mu kasance da bangaskiya sosai ga Jehobah don mu ci gaba da kasancewa da tsabtar zuciya.—1 Tim. 1:3-5.

Sa’ad da Muke Fuskantar Sha’awoyi na Jiki

Wani irin farmaki da za mu iya fuskanta sa’ad da muke ƙoƙarin mu kasance da “tsabtar zuciya” ya ƙunshi sha’awoyi na jiki da na abin duniya. (1 Yoh. 2:15, 16) Son kuɗi ko kuma sha’awar tara dukiya da abin duniya za su iya ɓata zuciya, suna iya sa Kirista ya yi abubuwan da suka saɓa wa nufin Allah. Wasu sun nuna rashin gaskiya a wajen aiki, sun cuci wasu, ko kuma sun saci kuɗi ko abubuwa da ba nasu ba.—1 Tim. 6:9, 10.

A wani ɓangaren kuma, ta wajen jin tsoron ɓata wa Jehobah rai, mu ƙaunaci adalci, kuma mu ƙudurta kasancewa da lamiri mai kyau, za mu nuna cewa muna ƙaunar “tsabtar zuciya.” Wannan ƙaunar tana motsa mu mu ci gaba da yin “tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibran. 13:18) Sa’ad da muka aikata daidai, yin gaskiya zai iya sa a ba da shaida mai kyau. Emilio, wani Mashaidi ɗan Italiya wanda yake tuka wa wani kamfanin sufuri mota ya samu alabe da ke ɗauke da dalla 680. Abokan aikinsa sun yi mamaki sosai sa’ad da ya miƙa alaben ga shugabansa, wanda daga baya ya miƙa alaben ga wanda ya ɓatar da shi. Halin Emilio ya burge wasu abokan aikinsa sosai har suka soma son Littafi Mai Tsarki kuma suka soma nazari. A sakamakon haka, mutane bakwai daga iyalai biyu sun karɓi gaskiya. Hakika, yin gaskiya daga tsabtar zuciya zai motsa mutane su yabi Allah.—Tit. 2:10.

Wani abu kuma da zai shafi tsabtar zuciya na Kirista shi ne ra’ayin da bai dace ba game da jima’i. Da yake mutane da yawa suna ɗaukan cewa yin jima’i kafin aure, yin zina, da kuma luɗu ba laifi ba ne, hakan yana iya ɓata zuciyar Kirista. Mutumin da ya yi lalata yana iya yin rayuwa iri biyu, yana ɓoye zunubin. Hakan ba zai nuna “tsabtar zuciya” ba.

Gabriele ya yi baftisma sa’ad da yake ɗan shekara 15 kuma ya soma hidimar majagaba nan da nan. Amma daga baya, ya soma tarayya da abokan banza kuma suna zuwa fati a hotal da daddare tare. (Zab. 26:4) Mafarinsa na soma salon rayuwa na lalata da munafunci ke nan, kuma aka yi masa yankan zumunci daga ikilisiyar Kirista. Irin wannan horo daga wurin Jehobah ya sa shi yin tunani sosai. Gabriele ya tuna: “Na soma yin dukan abubuwan da bana ɗauka da muhimmanci a dā. Na soma karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana, ina ƙoƙarin na fahimci abin da Jehobah yake faɗa, kuma na yi nazarin littattafai na tsarin Allah da kyau. Na ga yadda nazari na kaina yake da ban albarka da gamsarwa da kuma yawan ƙarfi da mutum zai samu daga karatun Littafi Mai Tsarki da kuma yin addu’a sosai.” Wannan ya taimaki Gabriele ya bar halinsa na lalata kuma ya sake ƙulla dangantakarsa da Jehobah.

Yanzu Gabriele ya soma hidimar majagaba kuma, tare da matarsa. Abin da ya faru da shi ya tabbatar da yadda nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafai daga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” za su iya taimaka wa mutum ya kasance da tsabtar zuciya kuma ya ƙi lalata.—Mat. 24:45; Zab. 143:10.

“Tsabtar Zuciya” Sa’ad da Muke Fuskantar Gwaji

Matsi daga masu hamayya, matsala na tattalin arziki, da rashin lafiya mai tsanani sun zama sanadin sanyin gwiwa ga wasu cikin bayin Allah. A wani lokaci, hakan ya shafi zuciyarsu sosai. Har ma Sarki Dauda ya fuskanci irin wannan gwaji: “Ruhuna ya yi suwu daga cikina, zuciyata a cikina tana zaman kaɗaici.” (Zab. 143:4) Menene ya taimaka masa ya sha kan irin wannan gwaji? Dauda ya yi bimbini a kan abin da Jehobah ya yi wa bayinsa da kuma yadda shi da kansa ya samu ceto. Ya yi bimbini a kan abin da Jehobah ya yi domin sunansa mai girma. Dauda ya ci gaba da yin bimbini game da ayyukan Allah. (Zab. 143:5) Haka nan ma, yin bimbini game da Mahaliccinmu da dukan abubuwan da ya yi kuma ya ci gaba da yi dominmu zai taimaka mana har a lokacin da muke fuskantar gwaji.

Sa’ad da aka yi mana laifi, ko muna jin an yi mana laifi, muna iya yin baƙin ciki. Yin tunani a kai a kai game da batun zai sa mu riƙa baƙin ciki game da ’yan’uwanmu. Muna iya daina yin tarayya da mutane, muna iya ware kanmu, kuma mu daina damuwa da wasu. Amma, shin aikata hakan zai jitu ne da sha’awarmu na kasance da “tsabtar zuciya”? Hakika, makasudin kasancewa da irin wannan zuciya ya ƙunshi yadda muke sha’ani da ’yan’uwanmu Kirista da yadda muke aikatawa idan akwai rashin jituwa.

A duniya da take ƙara lalacewa a ɗabi’a, mu a matsayin Kiristoci na gaskiya mun fita dabam domin muna ƙaunar “tsabtar zuciya.” Rayuwarmu tana samun tasiri mai kyau sa’ad da muke samun kwanciyar hankali da ake samu ta wajen yin nufin Allah. Fiye da kome, muna more dangantaka na kud da kud da Mahaliccinmu, Jehobah Allah, wanda yake ƙaunar waɗanda suke da “tsabtar zuciya.” (Zab. 73:1) Hakika, za a iya haɗa mu cikin waɗanda za su yi farin ciki, domin yadda Yesu ya yi alkawari, “za su ga Allah,” yayin da yake aikatawa domin waɗanda suke ƙaunar “tsabtan zuciya.”—Mat. 5:8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba