Shagala da Kuma Yin Farin Ciki a Hidimar Allah
JEHOBAH yana son ka yi farin ciki. (Zab. 100:2) A matsayin ɗaya daga cikin bayinsa, wataƙila kana da aiki da yawa. Wataƙila ba ka da aiki da yawa sa’ad da ka keɓe kanka ga Allah, amma yanzu hakkoki na zahiri da na ruhaniya suna iya sa ka ji kana cikin matsi. Kana iya yin baƙin ciki idan ka kasa cim ma dukan abubuwa da kake son ka yi. Ta yaya za ka kasance da daidaituwa kuma ka ci gaba da shaida “farinciki na Ubangiji”?—Neh. 8:10.
Kana zama a miyagun lokatai kuma za ka iya fuskantar matsi masu yawa, saboda haka kana bukatar ka kasance da tsari sosai. Game da wannan, wasu cikin hurarrun shawarwari da manzo Bulus ya ba da suna da muhimmanci: “Ku duba fa a hankali yadda kuke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi, tun da ya ke miyagun kwanaki ne.”—Afis. 5:15, 16.
Saboda wannan shawara mai kyau, ta yaya za ka kafa wa kanka makasudai masu yiwuwa kuma ka daidaita nazari na kanka, kula da iyali, hidimar fage, aiki, da wasu ayyuka da suka dace?
Ka tuna farin cikin da ka yi sa’ad da ka keɓe kanka ga Allah kuma ka yi baftisma? Ana yin farin ciki ta wajen sanin Jehobah da kuma nufe-nufensa. Wataƙila ka yi watanni kana yin nazari kafin ka samu irin wannan fahimi da kuma farin ciki. Amma kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu. Wannan nazarin ya kyautata rayuwarka.
Don ka ci gaba da farin ciki, kana bukatan ka ci gaba da cin abinci na ruhaniya. Idan kana famar samun lokacin karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki, ka bincika tsarinka. Yin nazari da bimbini ko na ’yan mintoci kaɗan ne a rana zai sa ka ƙara kusantar Jehobah, kuma hakan zai daɗa sa ka farin ciki.
Yawancin bayin Allah suna iya fid da lokaci domin su yi ayyuka masu muhimmanci daga lokacin da suke yin abubuwa da ba su da muhimmanci sosai. Ka tambayi kanka, ‘Menene yawan lokacin da nake ba da wa wajen karanta jaridu, kallon talabijin, sauraron waƙa, ko kuma yin abubuwa da nake so?’ Irin waɗannan ayyuka suna da kyau sa’ad da aka daidaita su. (1 Tim. 4:8) Idan ka fahimci cewa ba ka yin amfani da lokacinka da kyau, ka ɗauki matakai ka gyara tsarinka.
Adam, wanda magidanci ne, mai yara uku, kuma dattijo ne, ya bayyana abin da ya taimake shi: “Ina ƙoƙari na yi rayuwa mai sauƙi. Ina guje wa ayyuka jin daɗi masu cinye lokaci da kuma abubuwan mallaka da ke bukatan lokaci sosai. Ba wai ina hana wa kaina abubuwa masu kyau ba ne, amma na zaɓi na more nishaɗi mai sauƙi ne kawai.”
Yin bimbini a kan sakamako mai kyau na shawarwarinka zai sabonta farin cikinka kuma ya taimake ka ka kasance da ra’ayin da ya dace. Alal misali, Mariusz, wani dattijo wanda yake da yara uku, ya ce: “Sa’ad da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, na kasance da bege da ra’ayi mai kyau game da nan gaba. Lokaci lokaci, ina fuskantar matsaloli, yawancinsu Jehobah ne kaɗai ya san game da su. Amma ina godiya don taimakonsa, ina sauraron nan gaba da farin ciki.”
Kamar Mariusz, kasancewa da ra’ayi mai kyau ba zai kawar da dukan alhini ba. Amma zai iya taimaka maka ka samu sauƙi kuma ka bi da ƙalubale na rayuwa da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan kwanakin masu-shan wuya da cuta su ke: amma mai-farin zuciya yana da buki tuttur.” (Mis. 15:15) Ka yi bimbini kuma, a kan ƙauna da Allah ya riga ya nuna maka. Irin wannan bimbini zai sa ka ƙaunace shi sosai kuma ka zurfafa farin cikinka ga Allah.—Mat. 22:37.
Saka Jehobah da al’amuransa farko a rayuwa yana ƙara sa iyali farin ciki. Nuna halaye masu kyau na Kirista na rage saɓani kuma yana sa iyali ta yi cuɗanya mai kyau. Ta hakan, salama za ta kasance a gidanka kuma iyalinka gaba ɗaya za ta kasance da haɗin kai.—Zab. 133:1.
Yin ayyuka na ruhaniya tare a matsayin iyali na kawo farin ciki na gaske. Mariusz ya ce: “Ina ɗaukan lokacin da muke kasancewa tare a matsayin iyali da tamani. Matata tana taimaka mini sosai. Duk lokacin da ya yiwu, tana tare da ni ko da ina hidimar fage ne ko kuma ina share filin wasa kafin taron gunduma, kuma tana bi na sa’ad da nake ba da jawabai a wasu ikilisiyoyi. Hakan yana ƙarfafa ni.”
Littafi Mai Tsarki ya umurci Kiristoci su yi tanadin bukatun iyalansu. (1 Tim. 5:8) Amma idan aiki yana cinye yawancin lokaci da kuzarinka, hakan yana iya hana ka samun farin ciki a hidimar Allah. Ka yi addu’a ga Jehobah game da batun. (Zab. 55:22) Wasu sun ga cewa domin su saka Mulkin Allah farko suna bukatan su nemi wani aikin. Bai kamata kowane Kirista ya ƙyale kuɗin da yake samu a aikin da ke ɗaukan lokacinsa da kuzari ya hana shi mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya da suka fi muhimmanci ba.—Mis. 22:3.
Yana iya kasance da taimako idan ka rubuta dukan amfani da illa na aikin da kake yi a yanzu ko wanda kake son ka soma. Albashi mai tsoka da kuma aiki mai gamsarwa suna da kyau. Duk da haka, aikinka na yanzu yana taimaka maka ka kula da ruhaniyar iyalinka? Ka bincika dukan abubuwan da aikin ya ƙunsa, kuma ka tsai da shawarwarin da za su sa dangantakarka da Jehobah ta zama abu na farko.
Idan yanayinka ba ya taimaka maka ka samu ci gaba a ruhaniya, kana bukatan ka daidaita yanayinka. Kiristoci da yawa sun yi canje-canje sosai domin su samu lokacin yin al’amura na ruhaniya. Wani ɗan’uwa a ƙasar Poland ya ce: “Akwai lokacin da ya zama dole in bar kamfanin da nake aiki domin sau da yawa ina tafiya don aiki. Ba ni da isasshen lokaci da zan kula da al’amura na ruhaniya ko kuma iyalina.” Yanzu yana yin aikin da ba ya ɗaukan lokacinsa da kuzari sosai.
Ka Yi Farin Ciki Wajen Taimakon Mutane
Yesu ya ce “bayarwa ta fi karɓa albarka.” (A. M. 20:35) Kiristoci suna da zarafi da yawa na bayarwa. A wani lokaci, yin murmushi, shan hannu, ko kuma yin godiya don aiki tuƙuru da mutum ya yi a tsari na Allah zai iya zama abin da ake bukata don ku yi farin ciki.
Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci masu bi: “Ku ƙarfafa masu-raunanan zukata, ku tokare marasa-ƙarfi.” (1 Tas. 5:14) Masu raunanan zukata suna iya jin cewa ba za su iya jimre matsalolinsu da ƙarfinsu ba. Za ka iya taimaka wa irin waɗannan mutanen? Idan ka ga cewa wani cikin ’yan’uwanka ya daina farin ciki a hidimar Jehobah, ka yi ƙoƙari ka ƙarfafa shi. Yin hakan zai ƙarfafa ka. Akwai matsalolin da ɗan Adam ba zai iya magance su ba. Amma, za ka iya nuna juyayi na gaske kuma ka aririce ɗan’uwanka ya dogara ga Jehobah don taimako. Waɗanda suka yi hakan ba za su taɓa yin sanyin gwiwa ba.—Zab. 27:10; Isha. 59:1.
Wani mataki mai kyau shi ne ka gayyaci wanda ba ya farin ciki ku fita hidimar fage tare. Sa’ad da Yesu ya aika da almajirai 70, ya yi hakan “biyu biyu.” (Luk 10:1) Ba ka gaskata ba cewa abin da Yesu ya yi ya taimaki mutane biyun su ƙarfafa juna? Za ka yi amfani da wannan misalin ka taimaki wani ya dawo da farin cikinsa a yau?
A yau muna da dalilai na damuwa. Duk da haka, Bulus ya shawarce mu: “Ku yi farinciki cikin Ubangiji kullayaumi: sai in sake cewa, ku yi farinciki.” (Filib. 4:4) Domin kana ƙaunar Allah, kana yi masa biyayya, kuma kana yin aikin da ya ba ka da himma, rayuwarka tana da ma’ana. Hakan yana sa ka farin ciki. Ballantana ma, Jehobah yana taimaka maka ka magance matsi da matsaloli da kake fuskanta.—Rom. 2:6, 7.
Muna da bangaskiya cewa mun yi kusa sosai da sabuwar duniya da Jehobah ya yi alkawarinta. Hakan zai kawo albarka masu yawa da dalilin yin farin ciki! (Zab. 37:34) Saboda haka muna yin farin ciki, ba tare da manta da yawan yadda Jehobah yake mana albarka a yanzu ba. Saboda haka, muna iya “bauta wa Ubangiji da farinzuciya.”—Zab. 100:2.
[Hotunan da ke shafi na 8]
Wataƙila kana bukatan ka daidaita yadda kake amfani da lokacinka idan za ka ci gaba da farin ciki
YAWON SHAƘATAWA da NISHAƊI
GIDA da kuma KULA Da IYALI
AIKI
TARON KIRISTA
NAZARI NA KAI
HIDIMA
[Hotunan da ke shafi na 10]
Za ka iya taimaka wa wasu su dawo da farin cikinsu?