Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 pp. 22-25
  • Yadda Tarurrukan Gunduma Guda Uku Suka Shafi Rayuwata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Tarurrukan Gunduma Guda Uku Suka Shafi Rayuwata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Darassi Game da Kasancewa da Gaba Gaɗi
  • Na Koyi Kasancewa da Wadar Zuci
  • An Motsa Mu Mu Ƙara Ba da Kanmu
  • Mun Sake Saduwa da Abokai Ƙaunatattu
  • Jehobah Ya Taimaka Mini Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Me Zan Bayar Ga Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ban Taba Daina Koyan Abubuwa Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Na Ji Dadin Koya da Kuma Koyar da Wasu Game da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 pp. 22-25

Yadda Tarurrukan Gunduma Guda Uku Suka Shafi Rayuwata

Ne ya ba da Labarin George Warienchuck

ABIN da ka ji a taronmu na gunduma ya taɓa shafanka sosai da har ka motsa ka yi canje-canje sosai a rayuwarka? Hakan ya faru da ni. Na tuna cewa tarurrukan gunduma guda uku musamman sun shafi rayuwata. Na farkon ya taimaka mini na daina jin kunya; na biyun ya sa ni na kasance da wadar zuci; na ukun kuma ya sa na riƙa bayarwa. Amma, kafin na gaya maka game da waɗannan canje-canje, bari na bayyana maka wasu abubuwa da suka faru shekaru da yawa kafin a yi waɗannan tarurrukan, abubuwa game da yarantaka na.

An haife ni a shekara ta 1928, ni ne auta a cikin yara uku. An yi reno na da ’yan’uwana mata, Margie da Olga a garin South Bound Brook, New Jersey, a ƙasar Amirka, a lokacin garin na da mazauna misalin dubu biyu. Ko da yake mu talakawa ne, Mamarmu mai karimci ce. Duk lokacin da take da kuɗi, tana dafa abinci na musamman kuma ta raba wa maƙwabtanmu. Sa’ad da nake shekara tara, wata Mashaidiya wadda take yaren Hungary, wato, yaren mamarmu ta ziyarce ta, wannan ya motsa ta ta saurari saƙon Littafi Mai Tsarki. Daga baya, Bertha, wata ’yar’uwa matashiya ta ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta taimaki Mama ta zama baiwar Jehobah.

Ba kamar Mama ba, ina jin kunya kuma ba ni da gaba gaɗi. Abin da ya fi sa ni baƙin ciki shi ne cewa, Mama takan ƙasƙanta ni. Da hawaye na tambaye ta, “Me ya sa a koyaushe kina zargi na?” ta gaya mini cewa tana ƙaunata amma ba ta son na ga kamar na fi sauran. Mama tana da manufa mai kyau, amma rashin yaba mini ya sa na ga kamar na kasa ainun.

Wata rana, wata maƙwabciya wadda takan yi mini magana da ladabi ta gaya mini na bi ’ya’yanta maza zuwa makarantar cocinsu a ranar Lahadi. Na san cewa zan ɓata wa Jehobah rai idan na je, amma ba na son na ɓata wa wannan maƙwabciya mai kirki rai. Saboda haka, na je coci watanni da yawa ko da yake na san cewa hakan bai dace ba. A makaranta, tsoron mutum ya sa na yi abin da ya saɓa wa lamiri ta. Shugaban makarantar, mamallaki ne kuma yakan tabbata cewa malaman sun sa dukan yaran su sara wa tutar. Ni ma na sara wa tuta. Na ci gaba da yin hakan na kusan shekara guda, sai na yi canji.

Darassi Game da Kasancewa da Gaba Gaɗi

A shekara ta 1939, aka soma yin taron rukunin nazarin littafi a gidanmu. Ben Mieszkalski, wani matashi majagaba ne ke gudanar da nazarin. Muna kiransa Ben Babba, wanda ya dace. A gare ni, ya kai tsawo da kuma faɗin ƙofar gaban gidanmu. Ko da yake girmansa na sa mutane su ji tsoronsa, mutumin kirki ne kuma murmushinsa na sa na saki jiki nan da nan. Saboda haka, sa’ad da Ben ya gaya mini in fita hidimar fage tare da shi, na yarda da farin ciki. Muka zama abokai. Sa’ad da nake baƙin ciki, sai ya yi mini magana yadda wa zai yi magana da ƙanensa da yake ƙauna. Hakan yana da muhimmanci sosai a gare ni, kuma na ƙaunace shi sosai.

A shekara ta 1941, Ben ya gaya wa iyalinmu mu bi shi a cikin motarsa zuwa taron gunduma a birnin St. Louis, Missouri. Na yi farin ciki sosai! Ban taɓa tafiya fiye da mil hamsin daga gida ba, amma yanzu zan yi tafiya fiye da mil ɗari tara! Amma, da akwai matsaloli a birnin St. Louis. Ko da yake mutane sun yi alkawari za su ba Shaidu masauki, limaman sun gaya wa mabiyansu kada su ƙyale Shaidu su zauna a gidansu. Yawancinsu sun yi hakan. An yi wa iyalin da aka ce mu zauna tare da su barazana. Duk da haka, sun marabce mu. Sun ce za su cika alkawari da suka yi cewa za su ba mu ɗaki. Gaba gaɗinsu ya burge ni.

An yi wa ’yan’uwana mata baftisma a wannan taron gunduma. A ranar nan, Ɗan’uwa Rutherford, daga Bethel na Brooklyn, ya ba da jawabi mai motsawa kuma ya gaya wa dukan yara da suke son su yi nufin Allah su tashi tsaye. Yara kusan dubu goma sha biyar suka tashi tsaye. Ni ma na yi hakan. Sai ya gaya wa dukanmu da muke son mu yi iyakar ƙoƙarinmu a aikin wa’azi mu ce, “Aye.” Tare da sauran yaran, sai na ce, “Aye!” da babban murya. Bayan hakan aka yi tafi sosai. Hakan ya motsa ni sosai.

Bayan taron, muka ziyarci wani ɗan’uwa a birnin West Virginia. Ya gaya mana cewa a wani lokaci da yake aikin wa’azi, taron ’yan iska da suka fusata sun yi masa duka sosai kuma suka rufe shi da kwalta da gasu. Na saurara gabana na faɗiwa. “Amma zan ci gaba da yin wa’azi” in ji ɗan’uwan. Sa’ad da muka bar wannan ɗan’uwan, sai na ji kamar Dauda. Ina shirye na fuskanci shugaban makarantarmu da gaba gaɗi yadda Dauda ya fuskanci Goliyat.

Da na koma makaranta, sai na tuntuɓi shugaban makarantar. Sai ya kalle ni da fushi. Na yi addu’a ga Jehobah ya taimake ni. Sai na faɗa da sauri: “Na halarci taron gunduma na Shaidun Jehobah. Ba zan ƙara sara wa tuta ba!” Sai ya yi shuru na dogon lokaci. Sai ya tashi a hankali daga teburinsa kuma ya zo waje na. Ya yi fushi sosai. Sai ya yi ihu: “Ka sara wa tutar ko kuma a kore ka!” A wannan lokacin ban karya aminci na ba, kuma na yi farin ciki da ban taɓa yi ba.

Na yi farin ciki sosai har ina son na gaya wa Ben abin da ya faru nan da nan. Sa’ad da na gan shi a Majami’ar Mulki, na faɗa da babban murya: “An kore ni daga makaranta! Ban sara wa tuta ba!” Ben ya saka hannunsa a kafaɗa ta, ya yi murmushi, ya ce: “Babu shakka, Jehobah yana ƙaunarka.” (K. Sha 31:6) Waɗannan kalaman sun ƙarfafa ni! Na yi baftisma a ranar 15 ga Yuni, 1942.

Na Koyi Kasancewa da Wadar Zuci

Bayan Yaƙin Duniya na biyu, tattalin arziki na ƙasar ya gyaru farat ɗaya, kuma abubuwan mallaka ya cika ƙasar. Ina yin aikin da nake samun kuɗi sosai kuma ina iya sayan abubuwa da a dā ba zan iya sayensu ba. Wasu cikin abokai na suka saye babura; wasu kuma suka gyara gidansu. Na sayi sabuwar mota. Ba da daɗewa ba son na ƙara sayan abubuwa ya sa na daina mai da hankali ga bauta wa Jehobah. Na san ina mai da hankali ga abubuwa da ba su dace ba. Abin farin ciki, a shekara ta 1950, taron gunduma da aka yi a New York ya taimaka mini na daidaita ra’ayina da ayyuka na.

A wannan taron gunduma, masu jawabi sun ƙarfafa masu sauraro su ci gaba da aikin wa’azi. Wani mai jawabi ya aririce mu: “Ku koma wa abubuwan da kuke bukata kuma ku yi tseren.” Kamar da ni yake maganar. Na kuma ga saukar karatu na makarantar Gileyad, wanda ya sa ni tunani, ‘Idan waɗannan Shaidu tsarana sun yi watsi da abubuwan mallaka don su yi hidima a ƙasar waje, ya kamata na kasance a shirye na yi hakan a gida.’ Bayan da aka gama taron, na tsai da shawara na zama majagaba.

Kafin lokacin, na soma fita zance da Evelyn Mondak, wata ’yar’uwa mai ƙwazo a ikilisiyar da na tafi. Mamar Evelyn wadda ta yi renon yara shida su bi hanyar Jehobah, mata ce mai gaba gaɗi. Tana son yin hidima na kan titi a gaban wani babban Cocin Roman Katolika. Duk da cewa, sau da yawa firistoci da suka fusata sun gaya mata ta tafi, ba ta matsa ba ma. Kamar mamarta, Evelyn ba ta jin tsoron mutum.—Mis. 29:25.

A shekara ta 1951, ni da Evelyn muka yi aure, muka yi murabus daga wajen aikinmu kuma muka soma hidimar majagaba. Mai kula da da’ira ya ƙarfafa mu mu ƙaura zuwa Amagansett, wani ƙauye da ke gaɓar Atalantiya, misalin mil ɗari daga Birnin New York. Sa’ad da ikilisiyar ta gaya mana cewa ba su da masauki da za su ba mu, muka nemi tirela amma muka kasa samun wadda za mu iya saya. Sai muka ga tirela da ta lalace. Mai tirelar ya ce mu biya dalla 900, kuma hakan ya yi daidai da kyautar kuɗin da muka samu lokacin da muka yi aure. Muka saye ta, muka gyara ta, kuma muka kai ta sabon yankinmu. Amma, mun isa wurin ba mu da ko kobo, muna tunani yadda za mu kula da kanmu a matsayin majagaba.

Evelyn ta soma aikin sharan gida, ni kuma na samu aikin shara na tsakar dare a gidan abinci na ’yan Italiya. “Duk wani abinci da ya rage,” mai gidan abinci yakan gaya mini, “ka kai wa matarka.” Idan na kai gida da ƙarfe biyu na safe, tirelarmu sai ta cika da ƙamshin waina da kuma taliya. Waɗannan abinci da muke ɗumama suna sa mu farin ciki, musamman a lokacin sanyi da muke rawar ɗari cikin tirela mai sanyi sosai. Bugu da ƙari, ’yan’uwa da suke cikin ikilisiyar wani lokaci sukan bar babban kifi a matakalar tirelar. A waɗannan shekaru da muka yi hidima tare da waɗannan ’yan’uwa ƙaunatattu a ƙauyen Amagansett, mun koyi cewa kasancewa da wadar zuci da ainihin abubuwan da muke bukata na kawo rayuwa mai gamsarwa. Mun yi farin ciki a waɗannan shekarun.

An Motsa Mu Mu Ƙara Ba da Kanmu

A Yuli ta shekara ta 1953, mun gai da ɗarurruwan masu wa’azi a ƙasar waje da suka zo daga wasu ƙasashe inda suke hidima don su halarci taro na ƙasashe a New York. Sun ba da labarai masu ban sha’awa. Farin cikinsu ya shafe mu. Ban da haka, sa’ad da wani mai jawabi ya nanata cewa ƙasashe da yawa ba su ji saƙon Mulki ba tukuna, mun san ya kamata mu ƙara ba da kanmu ta wajen faɗaɗa hidimarmu. A wurin taron nan ne muka saka takardar zuwa makarantar koyar da masu hidima a ƙasar waje. A wannan shekarar, aka gayyace mu mu halarci aji na 23 na Makarantar Gileyad, wanda aka soma a watan Fabrairu ta shekara ta 1954. Wannan gata ce mai girma!

Mun yi farin ciki sosai sa’ad da aka tura mu hidima a Brazil. Kafin mu tashi tafiyarmu na kwanaki 14 da jirgin ruwa, wani ɗan’uwa da ya manyanta a Bethel ya gaya mini: “’Yan mata guda tara da ba su yi aure ba da suke hidima a ƙasashen waje za su tafi tare da kai da matarka zuwa Brazil. Ka kula da su!” Mai tuƙa jirgin ya yi murmushi sa’ad da ya gan ni ina shigowa jirgin da ’yan mata guda goma. Amma, ’yan’uwa matan ba su da matsala wajen bi da wannan yanayin. Duk da haka, zuciya ta ta kwanta sa’ad da muka isa ƙasar Brazili lafiya.

Bayan da na koya yaren da ake yi a Portugal, an tura ni hidimar mai kula da da’ira a birnin Rio Grande do Sul, wata jiha a kudancin Brazil. Mai kula da da’ira da na ɗauki matsayinsa da bai yi aure ba ya gaya wa ni da matata: “Na yi mamaki cewa an aiko da ma’aurata zuwa nan. Wannan wurin yana da manyan duwatsu.” Ikilisiyoyi sun bazu a cikin karkara masu yawa, kuma za a iya isa wasu ta wurin babbar mota kawai. Idan ka saya wa direban abinci, zai ƙyale ku ku hau motarsa. Kamar masu hawan doki, muna zama a kan kaya, mu riƙe igiyar da aka ɗaure kayan da ita da hannu biyu. Sa’ad da motar ta sha kwana, sai mu riƙe igiyar sosai don kada mu faɗi idan motar ta karkata kuma muna ganin kwari masu zurfi. Amma, ganin ’yan’uwa masu farin ciki da suke jiranmu yana sa tafiya na kwana ɗaya ta zama kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu.

Muna zama a gidajen ’yan’uwan. Talakawa ne sosai, amma hakan ba ya hana su bayarwa. A wani yanki da ke a ware, dukan ’yan’uwan suna aiki a kamfani inda ake aikin nama. Tun da yake kuɗin da ake biyansu ba shi da yawa, suna cin abinci sau ɗaya a rana. Ba a biyansu, idan ba su yi aiki rana ɗaya ba. Duk da haka, a lokacin ziyararmu, suna ɗaukan hutu na kwanaki biyu don su tallafa wa ayyukan ikilisiya. Sun dogara ga Jehobah. Waɗannan ’yan’uwan masu tawali’u sun koya mana darussa da ba za mu taɓa mantawa ba game da yin sadaukarwa domin Mulkin Allah. Ta wurin zama tare da su, mun sami koyarwa da babu makarantar da za ta iya koyar da mu hakan. Idan na tuna da waɗannan ’yan’uwan, har ila ina hawayen farin ciki.

A shekara ta 1976, muka koma Amirka don mu kula da mamata da ke rashin lafiya. Mun yi baƙin ciki da muka bar Brazil, amma mun yi farin ciki ganin cewa an sami ƙaruwa na masu shela da ikilisiyoyi a wannan ƙasar. Duk lokacin da muka samu wasiƙu daga Brazil, da farin ciki muna tuna dukan abubuwa da suka faru a rayuwarmu a wannan lokacin.

Mun Sake Saduwa da Abokai Ƙaunatattu

Sa’ad da muke kula da Mamata, mun yi hidimar majagaba kuma muka karɓi aikin shara. A shekara ta 1980, Mamata ta mutu da amincinta ga Jehobah. Bayan hakan, aka gayyace ni na yi hidimar mai kula da da’ira a Amirka. A shekara ta 1990, matata da ni muka ziyarci wata ikilisiya a birnin Connecticut, a wajen mun sadu da wani ƙaunatacce ƙwarai. Ben yana cikin dattawan ikilisiyar, wato, Ben da ya taimaka mini na manne wa Jehobah shekaru 50 da suka shige. Mun rungumi juna da farin ciki?

Tun shekara ta 1996, ni da Evelyn muna hidima a matsayin majagaba na musamman marasa ƙarfi a ikilisiya da ake yaren Portugal a birnin Elizabeth, a New Jersey. Ina rashin lafiya, amma da taimakon matata ƙaunataciya, ina fita hidimar fage yadda ya kamata. Evelyn tana kuma taimaka wa wata maƙwabciya tsohuwa marar ƙarfi. Sunanta Bertha ce, wadda ta taimaka wa mamata ta zama baiwar Jehobah shekaru 70 da suka shige! Mun yi farin cikin samun zarafin nuna mata godiyarmu ga dukan abubuwan da ta yi don ta taimaka wa iyalinmu mu koyi gaskiya.

Na yi godiya cewa waɗannan tarurrukan gunduma sun motsa ni na manne wa bauta ta gaskiya, na sauƙaƙa rayuwata, kuma na faɗaɗa hidimata. Hakika, waɗannan taron sun shafi tafarkin rayuwata.

[Hotunan da ke shafi na 23]

Mamar Evelyn (ta hagu) da mamata

[Hotunan da ke shafi na 23]

Abokina Ben

[Hotunan da ke shafi na 24]

Sa’ad da muke ƙasar Brazil

[Hotunan da ke shafi na 24]

Ni da Evelyn a yau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba