Iri Na Gaskiya Ya Kai Wurare Masu Nisa
JAMHURIYAR Tuva a ƙasar Rasha tana iyakan kudancin Siberiya, kuma Mongolia tana ɓangare na kudu da gabas. Da yake mutane da yawa da ke Tuva suna zama a wurare masu nisa, yana da wuya a kai musu saƙon Mulki. Amma, akwai lokacin da rukunin mutane suka yi tafiya daga ɓangarori dabam-dabam na Tuva suka je Kyzyl, babban birninta domin su halarci wani taron ƙara wa juna sani. Maria wata majagaba da ke zama a Kyzyl, ta ji game da isowarsu, kuma ta fahimci cewa wannan zarafi ne na yi musu wa’azin bishara.
Maria ta faɗi abin da ya faru: “Makarantar da na nake koyarwa ta tsara taro a kan yadda za a kawar da yin amfani da miyagun ƙwayoyi. Misalin mutane hamsin daga wurare masu nisa na Tuva sun halarta. Rukunin ya haɗa da malamai, masanan halin ɗan adam, masu kula da zaman lafiyar yara da sauransu.” Ga Maria wannan taron zarafi ne da kuma ƙalubale. Ta ce: “Ni mai jin kunya ce, kuma yana mini wuya na yi wa’azi babu shiri. Amma, na roƙi Jehobah cikin addu’a ya ba ni ƙarfin zuciya da zai sa kada na ji tsoro kuma in yi amfani da wannan zarafi na yi wa’azi. Ta ci nasara kuwa?
Maria ta ci gaba: “Na sami mujallar Awake! da ta tattauna game da batun mugun jin tsoro. Na yi tunani: ‘Masanin halin ɗan adam zai so ya karanta wannan talifin,’ sai na kai mujallar makaranta. A ranar, ɗaya cikin malaman da suka halarci taron ta shigo cikin ofishi na, sai na ba ta mujallar. Ta karɓa da farin ciki. Ta ce tana mugun jin tsoro. Washegari, na kawo mata littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na ɗaya. Ta karɓi wannan littafin da farin ciki na yi tunani cewa wasu malaman za su so wannan littafin. Sai na ɗauki katan na littafin nan Young People Ask da wasu littattafai na kai makaranta.” Kafin ka sani, babu kome a cikin katan ɗin. Maria ta faɗi abin da ya faru: “Abokan aikin wannan malamar da na ba littafin nan Young People Ask suka shigo cikin ofishi na suna tambaya, ‘A ina ake raba littattafan?’” Sun zo wurin da ya dace!
Ranar Asabar ce ranar ƙarshe na taron. Kuma ranar hutun Maria ce, sai ta ajiye littattafan a kan tebura da yawa a cikin ofishin ta. Ta rubuta a kan allo: “Malamai ƙaunatattu! Kuna iya ɗaukan littattafai ma kanku da abokanku da za su so su karanta. Waɗannan littattafai masu kyau za su taimaka muku ku yi nasara a aikinku kuma su ƙarfafa iyalanku.” Menene ya faru? “Da na shiga ofishi na sai na ga cewa an ɗauki yawancin littattafan. Nan take na kawo wasu littattafai da mujallu. “A ƙarshen taron, Maria ta ba da jaridu 380, littattafai 173, da mujallu 34. Sa’ad da waɗanda suka halarci taron suka koma yankunansu da ke a ware inda suke zama da kuma aiki, sun tafi da littattafan. Maria ta ce, “Ina farin ciki sosai cewa yanzu iri na gaskiya ya kai wurare masu nisa a Tuva!”—M. Wa. 11:6.
[Taswira da ke shafi na 32]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
RASHA
JAMHURIYAR TUVA