Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/15 pp. 15-19
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Koyarwa Da Ƙauna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Koyarwa Da Ƙauna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙauna ta Fi Muhimmanci
  • Dole ne Mu Ƙaunaci Jehobah
  • Dole ne Mu Ɗauki Koyarwarmu da Muhimmanci
  • Dole Ne Mu Ƙaunaci Mutane
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/15 pp. 15-19

Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Koyarwa Da Ƙauna

“Babu mutumin da ya taɓa yin magana haka.”—YOH. 7:46.

1. Yaya mutane suka aikata game da yadda Yesu yake koyarwa?

KA YI tunanin yadda zai zama abin farin ciki ka saurari Yesu sa’ad da yake koyarwa! Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda koyarwarsa ta shafi waɗanda suka sadu da shi. Alal misali, Luka marubucin Linjila ya faɗi cewa mutane a garin su Yesu sun yi “mamaki da zantattukan alheri da suka fito bakinsa.” Matta ya ba da rahoto a Huɗuba a kan Dutse cewa waɗanda suka saurari Yesu sa’ad da yake koyarwa “suka yi mamaki da koyarwansa.” Kuma Yohanna ya lura cewa dogarai da aka tura su kamo Yesu sun koma ba tare da shi ba, suna cewa “babu mutumin da ya taɓa yin magana haka.”—Luk 4:22; Mat. 7:28; Yoh. 7:46.

2. Waɗanne hanyoyin koyarwa ce Yesu ya yi amfani da su?

2 Waɗannan dogarai sun faɗi gaskiya. Babu shakka, Yesu ne babban Malami da ya taɓa rayuwa. Koyarwarsa ta fita sarai, tana da sauƙin fahimta, kuma ba wanda zai yi gardama da hujjarsa. Ya yi amfani da misalai da tambayoyi da kyau. Ya sa koyarwarsa ta yi daidai da yanayin waɗanda yake wa magana, ko suna da matsayi mai girma ko kuma su talakawa ne. Koyarwarsa tana da sauƙin fahimta duk da haka yana da muhimmanci. Amma, ba waɗannan abubuwa kaɗai ba ne suka sa Yesu ya zama babban Malami.

Ƙauna ta Fi Muhimmanci

3. A matsayin malami, yaya Yesu ya bambanta da shugabannin addinai na zamaninsa?

3 Babu shakka, akwai mutane masu basira da suke da ilimi da iyawa na koyarwa tsakanin marubuta da Farisawa. Menene ya sa yadda Yesu yake koyarwa ya kasance dabam da nasu? Shugabannin addinai na lokacin ba sa ƙaunar talakawa. Maimakon haka, sun rena su, suna ɗaukansu a matsayin “la’anannu.” (Yoh. 7:49) Akasin haka, Yesu ya yi juyayinsu, domin “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Yana da fara’a, yana tausayi, kuma yana da kirki. Ƙari ga haka, shugabannin addinai ba su da ƙauna ta gaskiya ga Allah. (Yoh. 5:42) Amma, Yesu yana ƙaunar Ubansa kuma yana farin cikin yin nufinsa. Shugabannin addinai sun murguɗe maganar Allah don ta yi daidai da yadda suke so, amma Yesu ya ƙaunaci “maganar Allah,” ya koyar da ita, ya ba da ma’anarta, ya kāre ta, kuma ya yi rayuwa daidai da ƙa’idodinta. (Luk 11:28) Hakika, Kristi ya nuna yana son abin da ya koyar sosai, ya nuna ƙauna a yadda ya bi da mutane, da kuma yadda ya koyar da su.

4, 5. (a) Me ya sa yake da muhimmanci a koyar cikin ƙauna? (b) Me ya sa ilimi da iyawa suke da muhimmanci kuma sa’ad da ake koyarwa?

4 Mu kuma fa? Da yake mu mabiyan Kristi ne, yana da kyau mu yi koyi da shi a hidimarmu da kuma rayuwarmu. (1 Bit. 2:21) Saboda haka, manufarmu ba za ta zama ta koyar da sani na Littafi Mai Tsarki kaɗai ba amma mun bukatan mu nuna halayen Jehobah, musamman ƙaunarsa. Ko muna da ilimi sosai ko kaɗan, ko mun iya koyarwa sosai ko kuma ba mu iya sosai ba, ƙaunar da muke nunawa za ta taimake mu mu motsa zuciyar waɗanda muke yi wa wa’azi. Don mu yi aikin almajirantarwa da kyau, dole ne mu yi koyi da Yesu ta wajen koyarwa da ƙauna.

5 Hakika, don mu zama ƙwararrun malamai, muna bukatar mu san batun da muke koyarwa da kuma yadda za mu koyar da shi. Yesu ya taimaki almajiransa su koyi duka, kuma Jehobah yana taimaka mana mu yi hakan a yau ta hanyar ƙungiyarsa. (Karanta Ishaya 54:13; Luka 12:42.) Duk da haka, ya kamata burinmu ya koya wa mutane da hankalinmu da kuma zuciyarmu. Idan muna da ilimi, iyawa, da ƙauna, sakamakon zai fi gamsarwa. A waɗanne hanyoyi, za mu iya nuna ƙauna sa’ad da muke koyarwa? Ta yaya Yesu da almajiransa suka yi hakan? Bari mu gani.

Dole ne Mu Ƙaunaci Jehobah

6. Yaya muke magana game da wanda muke ƙauna?

6 Muna jin daɗin yin magana game da abubuwa da muke so, kuma sa’ad da muka yi hakan, mutane za su ga farin cikinmu da kuma himmarmu. Hakan gaskiya ne sa’ad da muke magana game da wanda muke ƙauna. Muna ɗokin gaya wa mutane abin da muka sani game da mutumin. Muna yaba masa, ɗaukaka shi, da kuma kāre shi. Muna hakan domin muna son mutane su so mutumin da halayensa kamar yadda muke so.

7. Menene ƙaunar Yesu ga Allah ta motsa shi ya yi?

7 Kafin mu sa mutane su ƙaunaci Jehobah, dole ne mu san shi kuma mu ƙaunace shi. Ballantana ma, bauta ta gaskiya ta dangana ga ƙaunar Allah. (Mat. 22:36-38) Yesu ya kafa misali mafi kyau. Yana ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsa, azancinsa, ransa, da ƙarfinsa. Da yake wataƙila yana sama shekaru biliyoyi tare da Ubansa na samaniya, Yesu ya san shi da kyau. Menene sakamakon haka? Yesu ya ce: “Ina ƙaunar Uba.” (Yoh. 14:31) Yesu ya nuna wannan ƙaunar a dukan abubuwan da ya yi da kuma abubuwan da ya faɗa. Ƙauna ta motsa shi a koyaushe ya yi abubuwan da ke faranta wa Allah rai. (Yoh. 8:29) Ƙauna ta motsa shi ya hukunta shugabannin addinai waɗanda da munafunci sun yi da’awar cewa suna wakiltar Allah. Ta kuma motsa shi ya yi magana game da Jehobah kuma ya taimaki mutane su san Allah kuma su ƙaunace shi.

8. Menene ƙauna ga Allah ta motsa almajiran Yesu su yi?

8 Kamar Yesu, almajiransa na ƙarni na farko sun yi ƙaunar Jehobah, kuma wannan ƙaunar ta motsa su su yi wa’azin bishara da gaba gaɗi da himma. Sun cika Urushalima da koyarwarsu, ko da yake shugabannin addinai masu iko sun yi hamayya da su. Almajiran ba za su iya daina faɗan abin da suka ji ba da kuma wanda suka gani. (A. M. 4:20; 5:28) Sun san cewa Jehobah yana tare da su kuma zai albarkace, kuma ya yi hakan da gaske! Hakika, kafin shekara talatin bayan mutuwar Yesu, manzo Bulus ya rubuta cewa an yi wa’azin bishara “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.”—Kol. 1:23.

9. Ta yaya za mu ƙarfafa ƙaunarmu ga Allah?

9 Idan muna son mu zama ƙwararrun malamai, muna bukatar mu tabbata cewa za mu ci gaba da ƙarfafa ƙaunarmu ga Allah. Ta yaya za mu yi hakan? Ta wajen addu’a ga Allah sau da yawa. Muna kuma ƙarfafa ƙaunarmu ga Allah ta nazarin Kalmarsa, karanta littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki, da kuma halartan taron Kirista. Yayin da muka ƙara sanin Allah, za mu ƙaunace shi sosai. Sa’an nan, yayin da muka nuna ƙaunarmu ga Allah ta kalmomi da ayyukanmu, wasu za su lura da hakan kuma za su kusaci Jehobah.—Karanta Zabura 104:33, 34.

Dole ne Mu Ɗauki Koyarwarmu da Muhimmanci

10. Menene ke sa mutum ya zama ƙwararren malami?

10 Mutum zai iya zama ƙwararren malami ne idan ya ɗauki abin da yake koyarwa da muhimmanci. Dole ne ya gaskata cewa abin da yake koyarwa gaskiya ne, yana da muhimmanci, kuma yana da amfani. Idan malami yana damuwa da abin da yake koyarwa, za a ga ƙwazonsa, kuma zai rinjayi waɗanda yake koyar da su sosai. A wani ɓangare kuma, idan malami ba ya nuna ƙwazo game da abin da yake koyarwa, yaya yake tsammanin cewa ɗalibansa za su ga amfanin abin da suke ji? Misalinka a matsayin mai koyar da Kalmar Allah yana da muhimmanci. Yesu ya ce: “Kowa sa’anda ya kamalta za shi zama kamar malaminsa.”—Luk 6:40.

11. Me ya sa Yesu ya ɗauki abin da yake koyarwa da muhimmanci?

11 Yesu ya ɗauki abin da yake koyarwa da muhimmanci. Ya san yana da abu mai tamani da zai ba mutane, wato, gaskiya game da Ubansa na samaniya, “zantuttukan Allah” da kuma “maganar rai na har abada.” (Yoh. 3:34; 6:68) Kamar wuta mai haske, gaskiyar da Yesu ya koyar ta fallasa abin da ba shi da kyau kuma ta nanata abin da yake da kyau. Wannan gaskiyar ta kawo bege da kwanciyar hankali ga masu tawali’u waɗanda shugabannin addinai suka ruɗa kuma Iblis ya zalunce su. (A. M. 10:38) Yesu yana nuna cewa yana son gaskiya a koyarwarsa da kuma dukan abubuwan da ya yi.

12. Yaya manzo Bulus yake ji game da bishara?

12 Kamar Yesu, almajiransa sun ɗauki abin da suke koyarwa da muhimmanci kuma sun daraja gaskiya game da Jehobah da Kristi sosai da har masu hamayya ba su iya hana su yi wa mutane magana game da gaskiya ba. Bulus ya rubuta ga Kiristoci masu bi a Roma: “Iyakacin ƙarfina, a shirye na ke in yi wa’azin bishara . . . Gama bishara ba abin kunya ba ce a gareni: gama ikon Allah ce zuwa ceto ga kowane mai-bada gaskiya.” (Rom. 1:15, 16) Bulus yana ganin daraja ne ya yi shelar gaskiya. Ya rubuta: “A gare ni aka ba da wannan alheri, in yi wa’azin wadatar Kristi wurin Al’ummai, wadata wadda ta fi ƙarfin a biɗa.” (Afis. 3:8) Ganin ƙwazon Bulus ba shi da wuya sa’ad da yake koya wa mutane game da Jehobah da nufe-nufensa.

13. Don waɗanne dalilai za mu so yin bishara?

13 Bisharar da take cikin Kalmar Allah tana taimaka mana mu san Mahalicci kuma mu ƙulla dangantaka ta ƙauna da shi. Wannan bishara tana ba da amsa mai gamsarwa ga tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa kuma tana da ikon canja rayuwarmu, tana ba mu bege, kuma tana ƙarfafa mu a lokacin wahala. Ƙari ga haka, tana nuna mana hanyar rayuwa mai ma’ana da ba za ta taɓa ƙarewa ba. Babu sani da ya fi tamani ko kuma muhimmanci da bishara ba. Kyauta ce mai tamani da aka ba mu, kuma tana sa mu farin ciki sosai. Kuma muna daɗa farin ciki sa’ad da muka raba wannan kyauta da mutane.—A. M. 20:35.

14. Yaya za mu ƙarfafa ƙaunarmu ga abin da muke koyarwa?

14 Menene za ka yi don ka ƙara ƙarfafa ƙaunarka don bishara? Sa’ad da kake karanta Kalmar Allah, ka dakata a wani lokaci ka yi tunani a kan abin da kake karantawa. Alal misali, ka yi tunani kana bin Yesu sa’ad da yake hidima a duniya ko kuma kana tafiya tare da manzo Bulus. Ka yi tunanin kana cikin sabuwar duniya, kuma ka ƙaga yadda rayuwa za ta kasance dabam. Ka yi bimbini a kan albarka da ka samu ta wurin yin biyayya ga bishara. Idan kana son yin bishara sosai, waɗanda kake koyar da su za su ga hakan. Saboda haka, yana da kyau mu yi bimbini sosai a kan abin da muka koya kuma mu mai da hankali a kan abin da muke koyarwa.—Karanta 1 Timotawus 4:15, 16.

Dole Ne Mu Ƙaunaci Mutane

15. Me ya sa ya kamata malami ya ƙaunaci ɗalibansa?

15 Ƙwararren malami yana sa ɗalibansa su saki jiki don su sa kai a abin da suke koya kuma su yi farin cikin faɗan abin da ke zuciyarsu. Malami mai ƙauna yana koyar da sani domin yana damuwa da ɗalibansa sosai. Yana sa koyarwarsa ta yi daidai da bukatunsu da kuma fahiminsu. Yana yin la’akari da iyawa da kuma yanayin ɗalibansa. Idan malamai suna da irin wannan ƙaunar, ɗaliban za su fahimci hakan, kuma koyarwa da koyo za su yi daɗi.

16. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna ƙauna ga mutane?

16 Yesu ya nuna irin wannan ƙaunar. Ƙauna mafi girma da ya nuna, ita ce, ba da kamiltaccen ransa domin ya ceci mutane. (Yoh. 15:13) A lokacin hidimarsa, a koyaushe Yesu yana shirye ya taimaki mutane a zahiri kuma musamman a ruhaniya. Maimakon ya jira mutane su zo wajensa, ya yi tafiya da ƙafa na ɗarurruwan miloli don ya yi musu wa’azin bishara. (Mat. 4:23-25; Luk 8:1) Shi mai haƙuri ne kuma mai fahimi. Sa’ad da almajiransa suke bukatar gyara, ya yi hakan da ƙauna. (Mar. 9:33-37) Ya ƙarfafa su ta wajen furta tabbacinsa cewa za su zama ƙwararrun masu wa’azin bishara. Babu mutumin da ya taɓa zama malami mai ƙauna kamar Yesu. Ƙaunar da ya nuna wa almajiransa ta motsa su su ƙaunace kuma su bi umurninsa.—Karanta Yohanna 14:15.

17. Yaya almajiran Yesu suka nuna ƙauna ga mutane?

17 Kamar Yesu, almajiransa sun nuna ƙauna sosai ga waɗanda suka yi wa wa’azi. Ta wurin jimre wa tsanantawa da kuma zaɓan su mutu, sun yi hidima ga wasu kuma sun yi nasarar yin wa’azin bishara. Hakika suna ƙaunar waɗanda suka yi na’am da bishara! Kalmomin manzo Bulus sun nuna ƙaunarsa sa’ad da ya rubuta: “Muka yi ladabi a wurinku, kamar reno wadda ta ke kiyayadda ’ya’yan kanta: haka nan mu kuma, domin muna marmarinku da soyayya, muka ji daɗin ba ku, ba bisharar Allah kaɗai ba, amma har da rayukanmu, gama kun zama abin ƙauna ƙwarai garemu.”—1 Tas. 2:7, 8.

18, 19. (a) Me ya sa muke a shirye mu yi sadaukarwa don mu yi aikin wa’azi? (b) Ka ba da misali da ya nuna cewa mutane suna lura da ƙaunar da muke nunawa.

18 Hakanan ma, Shaidun Jehobah a yau suna wa’azi a dukan duniya suna neman waɗanda suke son su san Allah kuma su bauta masa. A cikin shekaru goma sha bakwai da suka shige, muna ba da fiye da sa’o’i biliyan ɗaya kowace shekara wajen aikin wa’azi da almajirantarwa kuma mun ci gaba da yin wannan aikin. Muna yin hakan da yardan rai, ko da yake aikin wa’azi na bukatar lokaci, kuzari, da dukiyarmu. Kamar Yesu, mun fahimci cewa Ubanmu na samaniya mai ƙauna yana son mutane su samu sani da zai sa su sami rai madawwami. (Yoh. 17:3; 1 Tim. 2:3, 4) Ƙauna tana motsa mu mu taimaki mutane masu zuciyar kirki su san Jehobah kuma su ƙaunace shi yadda muke ƙaunarsa.

19 Mutane suna lura da ƙauna da muke nunawa. Alal misali, wata ’yar’uwa majagaba a Amirka ta rubuta wasiƙu don ta yi ta’aziyya ga waɗanda suka rasa ƙaunatattunsa a mutuwa. Wani mutum ya amsa cewa: “Da farko na yi mamaki cewa wata za ta yi irin wannan ƙoƙari ta rubuta wasiƙa zuwa ga wanda ba ta sani ba domin ta taimake shi ya jimre da lokacin wahala. Na kammala kawai cewa kina ƙaunar mutane da kuma Allah wanda yake ja-gorar mutane zuwa hanyar rayuwa.”

20. Me ya sa yake da muhimmanci mu koyar da mutane cikin ƙauna?

20 An faɗi cewa idan aka yi aiki da ƙauna da gwaninta, za a yi aiki mafi kyau. A aikinmu na koyarwa, muna son mu taimaki ɗalibanmu su san Jehobah kuma su ƙaunace shi da dukan zuciyarsu. Hakika, don mu zama ƙwararrun malamai, muna bukatar ƙauna mai riɓi uku, wato, mu ƙaunaci Allah, mu ƙaunaci gaskiya, kuma mu ƙaunaci mutane. Yayin da muka koyi irin wannan ƙauna kuma muka nuna ta a hidimarmu, za mu sami farin cikin bayarwa da kuma gamsuwar sanin cewa muna yin koyi da Yesu da kuma faranta wa Jehobah rai.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yayin da muke koya wa mutane bishara, me ya sa yake da muhimmanci . . .

mu yi ƙaunar Allah?

mu ɗauki abin da muke koyarwa da muhimmanci?

mu yi ƙaunar waɗanda muke koyar da su?

[Hotunan da ke shafi na 15]

Me ya sa yadda Yesu yake koyarwa ya yi dabam da na marubuta da Farisawa?

[Hotunan da ke shafi na 18]

Koyarwa da kyau tana bukatar sani, iyawa kuma fiye da kome ƙauna

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba