Me Zan Bayar Ga Jehobah?
Ce ta ba da Babarin Ruth Danner
Da kalmomin ban dariya, Mama takan ce shekara ta 1933 shekara ce ta bala’o’i: Hitler ya soma sarauta, paparuma ya sanar cewa Shekara ce Mai Tsarki, kuma a wannan shekarar ce aka haife ni.
IYAYENA suna da zama a garin Yutz, a Lorraine, gari mai muhimmanci a tarihin Faransa da ke da iyaka kusa da Jamus. A shekara ta 1921, Mamata, wadda ta yi imani sosai da addinin Katolika, ta auri Babana, ɗan addinin Farostatan. An haifi yayata Helen, a shekara ta 1922, kuma iyayena suka sa aka yi mata baftisma a Cocin Katolika sa’ad da take jaririya.
Wata rana a shekara ta 1925, an ba Baba littafin nan The Harp of God da aka rubuta da yaren Jamus. Sa’ad da ya karanta wannan littafin, ya tabbata cewa ya samu gaskiya. Ya rubuta wa mawallafan littafin, kuma suka haɗa shi da Bibelforscher, yadda ake kiran Shaidun Jehobah a lokacin a Jamus. Nan da nan, Baba ya soma wa’azi game da abin da ya koya. Mama ba ta yi farin ciki ba cewa yana wa’azi. Ta gaya masa da yaren Jamus, “Ka yi duk abin da kake so, amma kada ka yi tarayya da waɗannan Bibelforscher!” Amma, Baba ya riga ya tsai da shawararsa, kuma a shekara ta 1927 aka yi masa baftisma a matsayin wanda yake tarayya da su.
Saboda haka, kakata ta soma zuga Mama ta kashe auren. Wata rana a Coci, firist ɗin ya gargaɗi mabiyansa su “guji Danner, annabin ƙarya.” Da kakata ta dawo gida ranar daga Coci, ta jefi Baba da tukunyar fure daga kan benen gidanmu. Babban tukunyar furen ta faɗo nan da nan kuma ta bugi kafaɗarsa, ta kusan samunsa a kai. Wannan abin ya sa Mama ta yi tunani, ‘Addinin da ke sa mutane su zama masu kisan kai ba zai zama mai kyau ba.’ Sai ta soma karanta littattafan Shaidun Jehobah. Ba da daɗewa ba, ta tabbata cewa ta samu gaskiya kuma aka yi mata baftisma a shekara ta 1929.
Iyayena sun yi iyaka ƙoƙarinsu su sa Jehobah ya kasance gaskiya a gareni da yayata. Sukan karanta mana labaran Littafi Mai Tsarki kuma su tambaye mu dalilin da ya sa waɗanda suke cikin Littafi Mai Tsarki suka aikata yadda suka yi. A lokacin, Baba ya ƙi yin aikin dare ko kuma na yamma, ko da yake hakan zai sa iyalinmu ta yi ƙarancin kuɗi sosai. Yana son ya samu lokaci don taron Kirista, hidima, da kuma lokacin nazari da yaransa.
Lokacin Wahala Yana Kusatowa
Iyayena sukan nuna karimci a kai a kai ga masu kula masu ziyara da waɗanda suke hidima a Bethel a Siwizalan da Faransa, waɗanda suka gaya mana game da wahala da ’yan’uwanmu da ke Jamus mil kaɗan daga gidanmu suke sha. Gwamnatin Nazi suna kai Shaidun Jehobah sansani, suna ɗaukan yara daga wurin iyayensu Shaidu.
Iyayenmu sun shirya ni da yayata Helen mu jimre wahala da ke gabanmu. Iyayenmu sun taimake mu mu haddace ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su yi mana ja-gora. Sukan ce: “Idan ba ku san abin da za ku yi ba, ku yi tunanin Misalai 3:5, 6. Idan kuna jin tsoron gwaje-gwaje a makaranta, ku yi amfani da 1 Korinthiyawa 10:13. Idan aka ɗauke ku daga wajenmu, ku maimaita Misalai 18:10.” Na haddace Zabura ta 23 da 91 a kaina, kuma na tabbata cewa Jehobah zai ci gaba da kāre ni.
A shekara ta 1940, Nazi da ke Jamus sun kwace garin Alsace-Lorraine, kuma sabuwar mulkin ta bukaci dukan mutanen da suka girma su shiga jam’iyyar Nazi. Baba ya ƙi, kuma ’Yan Sandan Ciki suka yi barazana za su tsare shi. Sa’ad da Mama ta ƙi ta riƙa ɗinka kayan sojoji, ’Yan Sandan Ciki suka soma yi mata barazana.
Makaranta ta zama abin tsoro a gare ni. A kowace rana, abin da ake soma yi a ajinmu ita ce yi wa Hitler addu’a, da take mai suna “Ku Ɗaukaka Hitler” da kuma taken ƙasar Jamus wadda za ka miƙar da hannunka na dama. Maimakon su gaya mini kada na sara wa Hitler, iyayena sun taimake ni ta wajen koyar da lamirita. Da kaina na tsai da shawara ba zan sara wa Nazi ba. Malaman suka mare ni kuma suka yi barazana za su kore ni daga makaranta. Sa’ad da nake ’yar shekara bakwai, na taɓa tsayawa sau ɗaya a gaban dukan malamai goma sha biyu a makarantan. Sun yi ƙoƙarin su tilasta mini na sara wa Hitler. Duk da haka, na yi tsayin daka da taimakon Jehobah.
Wata malama ta soma yi mini wasa da hankali. Ta gaya mini cewa ni ɗaliba ce mai kyau, tana so na sosai, kuma ba za ta so a kore ni daga makaranta ba. Ta ce: “Ba lallai sai kin miƙa hannunki ba. Ki ɗan ɗaga kaɗan kawai. Kuma ba sai kin furta ‘Ku Ɗaukaka Hitler’ ba. Kawai ki yi kamar kina magana.”
Sa’ad da na gaya wa Mamata abin da malamata take yi, ta tuna mini game da labarin Littafi Mai Tsarki na matasa Ibraniyawa uku a gaban gunkin da sarki Babila ya kafa. “Menene ya kamata su yi?” ta yi tambaya. Na amsa, “Su bauta masa.” “Idan a lokacin da ya kamata su yi bauta a gaban gunkin sun sunkuya su ɗaura igiyar takalmansu, hakan zai dace ne? Ki tsai da shawara da kanki, ki yi abin da kika ga ya yi daidai.” Kamar Shadrach, Meshach, da Abednego, na tsai da shawara na bauta wa Jehobah kaɗai.—Dan. 3:1, 13-18.
Malaman sun kore ni daga makaranta sau da yawa kuma sun yi barazanar cewa za su ɗauke ni daga iyayena. Na tsorata sosai, amma iyayena sun ci gaba da ƙarfafa ni. Kafin in tafi makaranta, Mamata takan yi addu’a da ni, ta gaya wa Jehobah ya kāre ni. Na san cewa Jehobah zai ƙarfafa ni na yi tsayin daka don gaskiya. (2 Kor. 4:7) Babana ya gaya mini cewa idan matsin ya yi yawa, kada na ji tsoron dawowa gida. Ya ce, “muna ƙaunarki. Za ki ci gaba da zama ’yarmu.” “Batun tsakanin ki da Jehobah ne.” Waɗannan kalmomin sun ƙarfafa ni na riƙe amincina.—Ayu. 27:5.
’Yan Sandan Ciki a koyaushe sukan zo gidanmu su nemi littattafai na Shaidu kuma su yi wa iyayena tambayoyi. Sai su ɗauki mamata su yi sa’o’i da yawa kuma su ɗauki babana da yayata daga wuraren aikinsu. Ban taɓa tsammani ko zan sami Mamata a gida ba idan na dawo daga makaranta. Wani lokaci wata maƙwabciyarmu ta gaya mini: “Sun ɗauki mamarki.” Sai na ɓoye a cikin gida, ina tambayar kaina: ‘Suna gana mata azaba ne? Zan sake ganinta kuwa?’
An Kai Mu Wata Ƙasa
A ranar 28 ga Janairu na shekara ta 1943, ’Yan Sandan Ciki suka ta da mu daga barci da ƙarfe uku da rabi na dare. Suka ce idan iyayena da yayata da ni muka shiga jam’iyyar Nazi, ba za a kai mu wata ƙasa ba. Suka ba mu sa’o’i uku mu yi shiri. Mamarmu ta riga ta yi shiri don wannan yanayin kuma ta cika jakunkunarmu da tufafi da Littafi Mai Tsarki, sai muka yi amfani da wannan lokacin muka yi addu’a kuma muka ƙarfafa juna. Baba ya tuna mana cewa ‘babu komi da zai iya raba mu da ƙaunar Allah.’—Rom. 8:35-39.
’Yan Sandan Ciki sun sake dawowa. Ba zan taɓa mance da ’yar’uwa tsohuwa mai suna Anglade sa’ad da take ɗaga mana hannu, idanunta cike da hawaye. ’Yan Sandan Ciki suka kai mu tashar jirgin ƙasa a garin Metz. Bayan kwanaki uku a cikin jirgi, muka kai Kochlowice, wani sansani da ke garin Auschwitz a ƙasar Poland. Bayan watanni biyu, aka mai da mu birnin Gliwice, wurin da mata masu zaman zuhudu ke zama a dā da aka mai da sansanin yin aiki. Mutanen Nazi suka gaya mana cewa idan kowannenmu ya saka hannu a wata takardar shaida na ƙin imaninmu, za su sake mu kuma su mayar mana da kayanmu. Mama da Baba suka ƙi, kuma sojojin suka ce, “Ba za ku taɓa koma gida ba.”
A watan Yuni aka kai mu Swietochlowice, inda na soma ciwon kai da yake damu na har yau. Na kamu da cuta a yatsu na, kuma wani likita ya cire yawancin ƙumba ta ba tare da ba ni maganin da zai hana ni jin zafi ba. Wani abu mai kyau da ya faru da ni shi ne cewa aikace-aikacen da nike yi wa masu gadin sau da yawa yana kai ni wani gidan burodi. Wata budurwa da ke wajen takan ba ni abin da zan ci.
A lokacin, an ware iyalinmu daga sauran fursunoni. A watan Oktoba na shekara ta 1943, aka kai mu wani sansani a birnin Ząbkowice. Muna kwana a kan gado a ɗaki da ke saman gida tare da mutane wajen sattin, maza, mata, da yara. Sojojin Nazi suna ba mu abincin da ya lalace, wanda kusan ba ya ciwuwa.
Duk da wahalar, ba mu yi sanyin gwiwa ba. Mun riga mun karanta cewa za a yi aikin wa’azi mai girma da bayan yaƙin a cikin Hasumiyar Tsaro. Saboda haka, mun san dalilin da ya sa muke shan wahala kuma ba da daɗewa ba wahalarmu za ta ƙare.
Sa’ad da muka ji cewa rundunar haɗin gwiwa suna zuwa, mun san cewa mutanen Nazi ba za su ci yaƙin ba. A farkon shekara ta 1945, sojojin Hitler suka bar sansaninmu. A ranar 19 ga Fabrairu, suka tilasta mana mu yi tafiya ta kusan mil ɗari da hamsin. Bayan makonni huɗu, mun kai garin Steinfels a Jamus, inda masu gadin suka shigar da fursunonin cikin mahaƙa. Mutane da yawa sun yi tsammanin cewa za a kashe mu. Amma a ranar, rundunar haɗin gwiwa ta iso, sojojin Nazi suka gudu, kuma wahalarmu ta ƙare.
Cimma Makasudaina
A ranar 5 ga Mayu, a shekara ta 1945, bayan kusan shekara biyu da rabi, muka kai gida a Yutz, cike da datti da kwarkwata. Ba mu canja tufafinmu ba tun watan Fabrairu, sai muka tsai da shawarar ƙone waɗannan tsofaffin tufafi. Na tuna mamarmu tana gaya mana cewa: “Bari wannan rana ta zama mafi kyau a rayuwarku. Ba mu da kome. Tufafin da muka saka ba ta mu ba ce. Duk da haka, dukanmu huɗu mun dawo gida da aminci. Mun riƙe amincinmu.”
Bayan watanni uku na samun sauƙi a Siwizalan, na koma makaranta, ba na jin tsoron cewa za a kore ni. Yanzu muna iya yin taro da ’yan’uwanmu na ruhaniya kuma muna yin wa’azi a fili. A ranar 28 ga Agusta, shekara ta 1947, sa’ad da nake shekara goma sha uku, na cika alkawarin da na yi shekaru da suka shige ga Jehobah a fili. Babana ya yi mini baftisma a Ƙogin Moselle. Ina son na zama majagaba nan da nan, amma Baba ya nace cewa na koyi aiki. Saboda hakan, na koyi ɗinki. A shekara ta 1951, sa’ad da nake ’yar shekara goma sha bakwai, na zama majagaba, kuma na soma hidima a wani garin Thionville da ke kusa.
A wannan shekarar, na halarci babban taro a ƙasar Paris kuma na cika takardar zama mai yin wa’azi a ƙasar waje. Ban kai shekarar da ake bukata ba tukuna, amma Ɗan’uwa Nathan Knorr ya ce zai riƙe takardar don “nan gaba.” A watan Yuni na shekara ta 1952, na samu gayyatar halartan aji na 21 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Giliyad a birnin Lansing na Kudu a New York na Amirka.
Makarantar Gilead da Rayuwata Bayan Hakan
Lallai na fuskanci abin ban mamaki! Yana yi mini wuya na yi magana a fili a yare na. Yanzu ya zama dole in yi Turanci. Duk da haka, waɗanda ke koya mini yaren sun taimake ni cikin ƙauna. Wani ɗan’uwa ya ba ni suna saboda irin murmushin da nake yi sa’ad da na ji kunya.
A ranar 19 ga Yuli ta shekara ta 1953, muka sauke karatu a Yankee Stadium a birnin New York, kuma aka aika ni zuwa ƙasar Paris tare da Ida Candusso (daga baya ta yi aure ta zama Ida Seignobos). Yin wa’azi ga mutanen Paris masu arziki ba shi da sauƙi, amma na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da masu tawali’u da yawa. Ida ta yi aure kuma ta tafi Afirka a shekara ta 1956, amma na tsaya a Paris.
A shekara ta 1960, na auri wani ɗan’uwa daga Bethel, kuma muka yi hidimar majagaba na musamman a garin Chaumont da Vichy. Bayan shekara biyar, na kamu da ciwon fuka kuma na daina hidimar majagaba. Na yi baƙin ciki sosai domin tun ina ƙaramar yarinya, makasudi na shi ne na yi hidima na cikakken lokaci kuma na kasance a ciki. Bayan wani lokaci, mijina ya ƙyale ni ya auri wata. Taimakon da na samu daga ’yan’uwana na ruhaniya ya taimake ni a waɗannan shekaru na baƙin ciki, kuma Jehobah ya ci gaba da ɗaukar nawayata.—Zab. 68:19.
Yanzu ina zaune a garin Louviers, Normandy, kusa da ofishin reshe na Faransa. Duk da rashin lafiya, ina farin cikin ganin cewa Jehobah yana tare da ni a rayuwata. Renon da aka yi mini yana taimako na har yau na kasance da ra’ayin da ya dace. Iyayena sun koya mini cewa Jehobah ne ainihin Wanda zan iya ƙauna, wanda zan iya yi wa magana, da wanda yake amsa addu’o’ina. Hakika “me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni?”—Zab. 116:12.
[Bayanin da ke shafi na 6]
“Ina farin cikin ganin cewa Jehobah yana tare da ni a rayuwata”
[Hotunan da ke shafi na 5]
Na rataye abin shaƙar iska sa’ad da nake ’yar shekara shida
[Hotunan da ke shafi na 5]
Tare da masu wa’azi a ƙasashen waje da majagaba a birnin Luxembourg don kamfen na wa’azi na musamman sa’ad da nake ’yar shekara goma sha shida
[Hotunan da ke shafi na 5]
Tare da Baba da Mama a taron gunduma a shekara ta 1953