Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/1 pp. 18-19
  • Allah Yana Sake Shawara ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Yana Sake Shawara ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Menene Ya Sa Aka Daina Yin Mu’ujizai?
  • Me Ya Sa Aka Ƙyale a Auri Mace Fiye da Guda?
  • Me Ya Sa Dokar Yin Assabaci na Ɗan Lokaci ne Kawai?
  • Allah Mai Aminci da Ƙauna
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/1 pp. 18-19

Allah Yana Sake Shawara ne?

GAME da Allah, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.” Kuma Allah da kansa ya ba da wannan tabbacin: “Ni Ubangiji ba mai-sākewa ba ne.” (Yaƙub 1:17; Malachi 3:6) Lallai Jehobah ya bambanta da mutanen da ba za a iya faranta wa rai ba kuma ba za a iya dogara da su ba domin suna sake shawara a koyaushe!

Amma, wasu masu karanta Littafi Mai Tsarki sukan yi mamaki, ko Allah ya sake shawara. Alal misali, a dā Jehobah Allah ya ba Kiristoci ikon yin mu’ujizai, amma yanzu ba ya yin hakan. A zamanin dā, Allah ya yarda a auri mace fiye da guda, amma a yanzu bai yarda da hakan ba. A ƙarƙashin Dokar Musa, Jehobah ya ce su yi Assabaci, amma a yanzu ba ya bukatar hakan. Shin waɗannan misalan ba su nuna ba ne cewa Allah ya sake shawara?

Na farko, mun tabbata cewa Allah ba ya sake mizanansa na ƙauna da shari’a. Kuma, ‘madawwamin nufinsa’ na yi wa ’yan adam albarka ta hanyar Mulkinsa bai taɓa canzawa ba. (Afisawa 3:11) Amma dai, kamar yadda za ka iya canja zuciyarka game da wanda halinsa yakan ɓata maka rai a kullum, Jehobah ma yakan canza rai bisa ga yadda yanayi ke canjawa.

Allah yana canza umurninsa ga mutanensa bisa ga yanayinsu da bukatunsu. Bai kamata hakan ya ba mu mamaki ba. Ka yi la’akari da abin da ƙwararren mai zagayawa da masu yawon shaƙatawa zai yi idan ya hangi haɗari a gaba. Zai gaya wa mutanen su bi wata hanyar da ba za ta kai su ga haɗarin ba. Hakan ba yana nufin cewa ya sake shawara game da wurin da za su, ko ba haka ba? Bari mu bincika misalai uku da muka ambata a baya, waɗanda wasu suka kasa fahimta.

Menene Ya Sa Aka Daina Yin Mu’ujizai?

Me ya sa Allah ya ba wasu cikin Kiristoci na ƙarnin farko ikon yin mu’ujizai? Wataƙila ka sani cewa sa’ad da Isra’ila take matsayin zaɓaɓɓiyar al’ummar Allah, Allah yakan yi amfani da mu’ujizai don ya nuna musu cewa yana tare da su. Ta hanyar Musa, Allah ya nuna ikonsa mai ban tsoro wajen ceto Isra’ilawa daga ƙasar Masar da kuma ja-gorar da ya yi musu daga jeji zuwa Ƙasar Alkawari. Abin baƙin ciki, Isra’ilawa sun ƙi su ba da gaskiya. Sa’ad da Jehobah ya ƙi Isra’ila kuma ya kafa ikilisiyar Kirista, ya ba manzani da waɗansu ikon yin mu’ujizai. Alal misali, manzo Bitrus da Yohanna sun warkar da wani mutumin da gurgu ne tun lokacin da aka haife shi, Bulus kuma ya ta da wani mutumi daga matattu. (Ayyukan Manzanni 3:2-8; 20:9-11) Mu’ujizan da suka yi ya taimaka wajen kafa Kiristanci a ƙasashe da yawa. To, menene ya sa aka daina yin mu’ujizai?

Manzo Bulus ya yi bayani ta hanyar kwatanci: “Sa’anda ina yaro, ni kan yi magana ta ƙuruciya, ni kan ji kamar mai-ƙuruciya, tunanina na ƙuruciya ne: amma yanzu da na zama namiji, na kawarda al’amuran ƙuruciya.” (1 Korintiyawa 13:11) Yadda iyaye suke bi da ƙaramin yaro ya bambanta da babba, hakazalika, yadda Jehobah yake bi da ikilisiyar Kirista ya canza sa’ad da ta wuce “ƙuruciya.” Manzo Bulus ya bayyana cewa “za a kawarda” ikon yin mu’ujizai da na furta harsunan baƙi.—1 Korintiyawa 13:8.

Me Ya Sa Aka Ƙyale a Auri Mace Fiye da Guda?

Yesu ya nuna cewa Allah ya kafa mizani game da aure sa’ad da Ya gaya wa mutane biyu na farko: ‘Namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne ma matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya?’ (Matta 19:5) Ya kamata aure ya zama dangantaka na dindindin tsakanin mutane biyu. Amma dai, sa’ad da Allah ya tsara Isra’ilawa su zama al’umma kuma ya ba su Doka, auren mace fiye da guda ya riga ya zama ruwan dare. Ko da yake Allah bai ce a auri mace fiye da guda ba ko kuma ya ƙarfafa yin hakan, ya ba da doka game da ita. Sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, Kalmar Allah ta bayyana dalla-dalla cewa haram ne a auri mace fiye da guda.—1 Timotawus 3:2.

Jehobah Allah yana ƙyale wasu abubuwa har sai lokacin da yake so ya daidaita su. (Romawa 9:22-24) Yesu ya nuna cewa Jehobah ya ƙyale al’adar aure da bai dace ba a ɗan lokaci ne a matsayin yarda don “taurin zuciyar” Isra’ilawa.—Matta 19:8; Misalai 4:18.

Me Ya Sa Dokar Yin Assabaci na Ɗan Lokaci ne Kawai?

Allah ya kafa dokar kiyaye Assabaci na mako-mako ne bayan ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Daga baya ya sa ya zama sashen Dokar al’ummar. (Fitowa 16:22-30; 20:8-10) Manzo Bulus ya bayyana cewa Yesu ya miƙa kansa hadaya kuma ya “kawas da . . . shari’a ta dokoki na cikin farillai” kuma “ya shafe shari’a.” (Afisawa 2:15; Kolosiyawa 2:14) Abin da aka “kawas” da kuma “shafe” ya haɗa da dokar Assabaci, don haka Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da cewa: “Kada kowanne mutum fa ya zarge ku a kan zancen ci, ko sha, ko zancen idi ko tsayawar wata ko ran asabar.” (Kolosiyawa 2:16) Menene ya sa Allah ya ba da Dokar, haɗe da ta Assabaci?

Manzo Bulus ya rubuta: “Shari’a ta zama mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi.” Sai ya daɗa: “Da bangaskiya ta zo yanzu, nan gaba ba mu ƙalƙashin mai-tsaro ba ne.” (Galatiyawa 3:24, 25) Maimakon ya canza shawara, Allah ya yi amfani da Assabaci a matsayin shiri na ɗan lokaci don ya koya wa mutane cewa su keɓe lokaci don yin bimbini a kan abubuwa na ruhaniya. Ko da yake dokar Assabaci na ɗan lokaci ne, ta yi nuni ne ga lokacin da ’yan adam za su samu hutu na har abada daga azaba ta zahiri da ta ruhaniya.—Ibraniyawa 4:10; Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.

Allah Mai Aminci da Ƙauna

Misalai na Littafi Mai Tsarki da muka tattauna a baya sun nuna cewa Jehobah Allah ya ba da umurni dabam-dabam a lokatai dabam-dabam. Amma hakan ba ya nufin cewa ya sake shawara ne. Maimakon haka, ya biya bukatun mutanensa a yanayi dabam-dabam, kuma ya yi hakan ne don amfaninsu. A yau ma haka.

Domin Jehobah baya sake mizaninsa, za mu ci gaba da sanin abubuwan da za mu yi don mu faranta masa rai. Bugu da ƙari, mu kasance da tabbaci cewa duk abubuwan da Allah ya yi alkawarinsu za su cika. Jehobah ya ce: “Zan kuma cika dukan nufina . . . Na ƙudurta, zan kuwa aika.”—Ishaya 46:10, 11.

[Bayanin da ke shafi na 18]

Allah bai taɓa canza mizanansa na ƙauna da shari’a ba

[Bayanin da ke shafi na 18]

Ya kamata aure ya zama dangantaka na dindindin tsakanin mutane biyu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba