Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 5/15 pp. 26-28
  • Ka Yi Koyi da Amincin Ittai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Koyi da Amincin Ittai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Baƙo Ne Ɗan Gudun Hijira Kuma’
  • “Domin Koyarwarmu”
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • ‘Kai Kaɗai Ne Mai Aminci’
    Ka Kusaci Jehobah
  • Cikakkiyar Dogara Ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 5/15 pp. 26-28

Ka Yi Koyi da Amincin Ittai

“AYYUKANKA masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai. Wanene za ya rasa jin tsoro, ya rasa ɗaukaka sunanka, ya Ubangiji? gama kai kaɗai mai-tsarki ne.” Wannan waƙar da “waɗanda suka tafo masu-nasara da bisan, da gunkinsa,” suka rera a sama ta jawo hankali ga amincin Allah. (R. Yoh. 15:2-4) Jehobah yana son masu bauta masa su yi koyi da shi wajen nuna wannan halin mai kyau.—Afis. 4:24.

A wani ɓangare kuma, Shaiɗan Iblis yana iya ƙoƙarinsa ya raba bayin Allah a duniya daga ƙaunar Allah da suke bauta wa. Duk da haka, mutane da yawa sun kasance da aminci ga Allah, har a cikin yanayi mai wuya ƙwarai. Muna godiya cewa Jehobah yana ɗaukan irin wannan ibada da tamani sosai! Hakika, an tabbatar mana cewa: “Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba.” (Zab. 37:28) Don ya taimake mu mu kasance da aminci, ya haɗa labarin ayyukan amintattu da yawa a cikin Kalmarsa. Ɗaya daga cikin irin waɗannan labaran shi ne na Ittai Bagitti.

‘Baƙo Ne Ɗan Gudun Hijira Kuma’

Kamar dai Ittai ɗan Gath ne, sanannen birnin Filistiya, garin gwarzo Goliyat da wasu manyan magabtan Isra’ila. Lokaci na farko da muka soma ji game da wannan jarumi mai suna Ittai shi ne sa’ad da Absalom ya yi tawaye ga Sarki Dauda. Ittai da mazan Filistiya ɗari shida da suke bin sa suna gudun hijira ne a wuraren Urushalima a lokacin.

Mai yiwuwa yanayin Ittai da mabiyansa ya sa Dauda ya tuna da lokacin da yake zaman bauta sa’ad da shi da jarumai Isra’ilawa ɗari shida suka ƙaura zuwa yankin Filistiya kuma suka shiga unguwar Achish, sarkin Gath. (1 Sam. 27:2, 3) Menene Ittai da mutanensa za su yi yayin da Dauda yake fuskantar tawayen ɗansa Absalom? Za su goyi bayan Absalom ne, ko kuwa ba za su goyi bayan kowa ba, ko kuma su bi Dauda da mutanensa?

Ka ƙaga yanayin yayin da Dauda yake guduwa daga Urushalima, sai ya tsaya a wurin da ake kira Beth-merhak, wanda ke nufin “Gida Mai Nisa.” Wataƙila shi ne gida na ƙarshe a Urushalima ta wajen Dutsen Zaitun kafin a haye Kwarin Kidron. (2 Sam. 15:17) A nan Dauda ya bincika rundunarsa sa’ad da suke wucewa. Ba Isra’ilawa masu aminci ba ne ba kaɗai suke binsa, amma har da dukan Karitiyawa da Peritiyawa. Bugu da ƙari, har da dukan Gatiyawa, wato, Ittai da jarumansa ɗari shida.—2 Sam. 15:18.

Cike da tausayi, Dauda ya gaya wa Ittai: “Don mi kai kuma kana tafe tare da mu? ka koma, ka zauna tare da sarki [wato, Absalom]: gama kai baƙo ne, fitace kuma; ka koma wurinka. Da shi ke jiya kaɗai ka zo, yau ya yi kyau in sa ka ka kai da kawo tare da mu, da shi ke ni zan tafi inda na samu? Sai ka juya, ka koma da ’yan’uwanka; jinƙai da gaskiya su zama tare da kai.”—2 Sam. 15:19, 20.

Nan da nan Ittai ya nuna amincinsa. Ya amsa: “Na rantse da ran Ubangiji, da ran ubangijina sarki kuma, hakika wurinda ubangijina sarki ya ke, ko domin mutuwa ko domin rai, nan kuma bawanka za ya kasance.” (2 Sam. 15:21) Mai yiwuwa hakan ya tuna wa Dauda kalmomi makamancin wannan da kakarsa Ruth ta furta. (Ruth 1:16, 17) Domin furcin Ittai ya taɓa zuciyarsa, Dauda ya gaya masa: “Je ka, ka haye” Kwarin Kidron. Sai “Ittai Ba-gitti ya haye, da mutanensa duka, da dukan ƙanana da ke tare da shi.”—2 Sam. 15:22.

“Domin Koyarwarmu”

“Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu,” in ji Romawa 15:4. Yana da kyau mu tambayi kanmu, Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga misalin Ittai? Ka yi la’akari da abin da wataƙila ya motsa shi ya bi Dauda. Ko da yake shi baƙo ne kuma ɗan gudun hijira daga Filistiya, Ittai ya fahimci cewa Jehobah Allah ne mai rai kuma Dauda ne shafaffen Jehobah. Ittai bai mai da hankali ba ga ƙiyayyar da ke tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa. Ittai bai yi wa Dauda kallon wanda ya kashe Bafilisti Goliyat da ’yan’uwansa Filistiyawa da yawa ba. (1 Sam. 18:6, 7) Ittai ya ɗauki Dauda a matsayin mutumin da ke ƙaunar Jehobah kuma ya lura da halayen Dauda masu kyau. Dauda kuma ya daraja Ittai sosai. Dauda ya sa kashi ɗaya cikin uku na rundunarsa “a hannun Ittai Ba-gitti” a yaƙi na ƙarshe a kan rundunar Absalom.—2 Sam. 18:2.

Ya kamata mu ƙoƙarta mu guji nuna bambancin al’ada, kabila, ko kuma ƙasa, wato, nuna bambanci da ƙiyayya ga mutane, amma mu mai da hankali ga halayensu masu kyau. Dangantaka na kud da kud da Ittai ya ƙulla da Dauda ya nuna cewa sanin Jehobah da ƙaunarsa za su taimake mu mu sha kan waɗannan bambance-bambancen.

Yayin da muke tunani a kan misalin Ittai, muna iya tambayar kanmu: ‘Ina da irin wannan amincin ga Dauda Mafi Girma, Yesu Kristi? Ina nuna amincina ta wajen kasancewa da himma a aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa? (Mat. 24:14; 28:19, 20) Ina shirye na jimre sosai don in nuna amincina?’

Magidanta za su amfana idan suka yi bimbini a kan misalin aminci na Ittai. Amincinsa ga Dauda da shawarar da ya yanke na bin sarkin da Allah ya naɗa ya shafi mutanen Ittai. Hakazalika, shawarwarin da magidanta suka tsai da don tallafa wa bauta ta gaskiya suna shafan iyalinsu kuma suna iya jawo wahala na ɗan lokaci. Duk da haka, an tabbatar mana: “[Jehobah] mai aminci ne ga masu aminci.”—Zab. 18:25.

Bayan yaƙin da Dauda ya yi da Absalom, Nassosi ba su ƙara faɗin komi ba game da Ittai. Duk da haka, ɗan labarinsa a cikin Kalmar Allah ya yi tanadin fahimi mai ban al’ajabi game da halinsa a lokacin wahala a rayuwar Dauda. Da yake an ambata Ittai a cikin Littafi Mai Tsarki, hakan ya nuna cewa Jehobah yana lura da kuma saka wa waɗanda suka kasance da irin wannan amincin.—Ibran. 6:10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba