Yaya Za Ka Jimre a Hidima?
KA TAƁA jin ka gaji har kana son ka daina yin aikin wa’azi? Hamayya mai tsanani, alhini, rashin lafiya, matsi na tsara, ko kuma rashin samun sakamako mai kyau daga mutanen da muke yi wa wa’azi suna iya sa ya kasance da wuya mu jimre. Amma, ka yi tunanin misalin Yesu. Ya jimre gwaje-gwaje mafi tsanani “domin farinzuciya da aka sa gabansa.” (Ibran. 12:2) Ya san cewa ta wajen ƙaryata zargin da aka yi wa Allah, yana sa Jehobah farin ciki.—Mis. 27:11.
Ta wajen jimrewa a hidima, kai ma za ka sa Jehobah farin ciki. Amma, idan wasu tangarɗa suna son su hana ka yin wa’azi fa? Krystyna, wadda ta tsufa kuma tana rashin lafiya, ta ce: “Ba sabon abu ba ne na ji na gaji kuma na yi baƙin ciki. Matsaloli da ke tattare da tsufa, kamar rashin lafiya da alhini game da rayuwa na yau da kullum suna iya rage ƙwazo da nake yi na ɗan lokaci.” Ta yaya za ka ci gaba a hidima duk da irin waɗannan matsaloli?
Ka Yi Koyi da Annabawa
Don su ci gaba a aikin wa’azi, masu shelar Mulki masu aminci suna iya ƙoƙarta su kasance da irin halin annabawa na dā. Alal misali, Irmiya. Sa’ad da aka gaya masa ya yi hidima na annabi, da farko ya yi jinkiri. Duk da haka, Irmiya ya jimre a aikinsa mai wuya fiye da shekara 40 domin ya koyi ya dogara ga Allah sosai.—Irm. 1:6; 20:7-11.
Misalin Irmiya ya ƙarfafa Henryk. Ya ce: “A cikin shekaru fiye da 70 da na yi ina hidima, a wani lokaci na kan yi sanyin gwiwa don halin mutane, ƙiyayyarsu, ko kuma rashin son jin wa’azi. A irin wannan lokaci, ina tuna wa kaina misalin Irmiya. Ƙaunarsa ga Jehobah da kuma ruhaniyar da yake da ita sosai sun ƙarfafa shi ya ci gaba da yin annabci.” (Irm. 1:17) Misalin Irmiya ya kuma ƙarfafa Rafał. Ya ce: “Irmiya ya dogara ga Allah maimakon ya mai da hankali ga kansa da kuma yadda yake ji. Ya ci gaba da nuna gaba gaɗi duk da ƙiyayya. Ina tuna wa kaina hakan.”
Wani annabi da misalinsa ya taimaka wa mutane da yawa su jimre a hidima shi ne Ishaya. Allah ya gaya masa cewa ’yan’uwansa ba za su saurare shi ba. Jehobah ya ce: “Ka sa zuciyar al’umman nan ta yi kitse, a nawaitadda kunnuwansu.” Ishaya zai ci nasara ne? E, da taimakon Allah! Sa’ad da aka ba shi aikin zama annabi, ya ce: “Ga ni; ka aike ni.” (Isha. 6:8-10) Ishaya ya nace wa aikinsa. Haka kake aikatawa ga umurnin yin wa’azi?
Don mu ci gaba a hidima duk da cewa mutane ba sa saurarawa, kamar yadda Ishaya ya yi, muna bukatar mu guji mai da hankali ga lokacin da mutane suka ƙi saƙonmu. Rafał ya sha kan sanyin gwiwa a wannan hanya: “Na guji mai da hankali ga baƙar maganar da mutane suke yi. Mutanen da ke yankinmu suna da damar aikatawa yadda suke so.” Anna ta daɗa: “Ina ƙoƙarin kawar da duk wani tunani marar kyau ko kuma mai sa sanyin gwiwa. Abin da ya taimake ni na yi hakan shi ne addu’a da yin nazarin nassosin yini kafin na fita hidimar fage. Duk wani tunani marar kyau yana ɓacewa nan da nan.”
Annabi Ezekiel ya yi hidima a tsakanin Yahudawa ’yan tawaye da suke zaman bauta a Babila. (Ezek. 2:6) Da a ce annabin bai gaya wa mutanen saƙon Allah ba kuma wani mugu ya mutu ba tare da jin gargaɗin ba, da Ezekiel ya ɗauki alhakin mutuwar wannan mutum. Jehobah ya gaya wa Ezekiel: “Zan ja jininsa a hannunka.”—Ezek. 3:17, 18.
Henryk ya yi ƙoƙari ya kasance da irin halin Ezekiel: “Ina son na kuɓuta daga jinin dukan mutane. Rayuka masu tamani na ’yan adam yana bakin halaka.” (A. M. 20:26, 27) Zbigniew shi ma yana da irin wannan ra’ayin: “Ezekiel ya ci gaba duk da irin tunanin mutane. Haka ya taimake ni na ɗauki aikin wa’azi yadda Mahalicci yake ɗaukansa.”
Akwai Mai Goyon Bayanka
Akwai wanda yake tare da kai sa’ad da kake aikin wa’azi. Kamar manzo Bulus, muna iya cewa: “Mu abokan aiki na Allah ne.” (1 Kor. 3:9) Krystyna, wadda ta ce wani lokaci tana baƙin ciki ta ce: “Shi ya sa na ci gaba da roƙon Jehobah ya ba ni ƙarfi. Bai taɓa yasar da ni ba.” Hakika, muna bukatar ruhun Allah ya tallafa mana a hidimarmu!—Zech. 4:6.
Sa’ad da muke wa’azi, ruhu mai tsarki yana taimakonmu mu nuna halayen da suka ƙunshi “ɗiyan Ruhu.” (Gal. 5:22, 23) Hakan na taimaka mana mu ci gaba a aikin wa’azi, ko da yaya mutane suka aikata. Henryk ya ce: “Aikin wa’azi yana taimako na na gyara hali na. Na koyi kasancewa mai haƙuri da mai yin la’akari da mutane ba mai fid da rai da sauri ba.” Jimrewa a hidima duk da tangarɗa dabam dabam zai iya taimaka maka ka kasance da ɗiyan ruhu a yawalce.
Jehobah yana yin amfani da mala’ikunsa su yi wa wannan aiki na musamman ja-gora. (R. Yoh. 14:6) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa akwai ‘zambar goma, zambar goma, da kuma dubban dubbai’ na mala’iku. (R. Yoh. 5:11) A ƙarƙashin ja-gorancin Yesu, mala’iku suna tallafa wa bayin Allah a duniya. Kana tuna hakan a duk lokacin da kake hidima?
“Tuna cewa mala’iku suna tare da mu sa’ad da muke hidima yana ƙarfafa ni,” in ji Anna. “Ina daraja taimakon da suke ba mu a ƙarƙashin kulawar Jehobah da Yesu.” Daraja ne mai tamani mu yi aiki tare da mala’iku masu aminci!
’Yan’uwa masu shelar Mulki kuma fa? An albarkace mu da sanin taron Shaidu masu aminci da yawa. Babu shakka, ka ga gaskiyar karin maganar Littafi Mai Tsarki: “Ƙarfe ya kan wasa ƙarfe: Hakanan kuma mutum ya kan wasa yanayin abokinsa.”—Mis. 27:17.
Fita hidima tare da wasu yana ba mu zarafi mai kyau mu lura da hanyoyin yin wa’azi da kyau da ba mu sani ba. Elżbieta ta ce: “Fita hidima da masu shela dabam dabam ya ba ni zarafin nuna ƙauna ga ’yan’uwana a ikilisiya da kuma mutanen da muke saduwa da su.” Ka yi ƙoƙari ka riƙa yin wa’azi da masu shela dabam dabam. Zai sa hidimarka ta zama mai kyau.
Ka Kula da Kanka Sosai
Don mu ci gaba da ƙwazo a hidima, dole ne mu yi shiri da kyau, mu kafa tsari mai kyau na nazari na kanmu kuma mu samu isasshen hutu. A wata sassa kuma, muna bukatar mu kula da kanmu a ruhaniya da kuma a zahiri.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tunanin mai-himma zuwa yalwa kaɗai su ke nufa.” (Mis. 21:5) Zygmunt, wanda a yanzu ɗan shekara 88 ne, ya ce: “Kasancewa da tsari mai kyau a hidimata yana taimako na na cim ma wasu makasudai. Na tsara lokaci na da kyau don na samu isashen lokacin yin wa’azi.”
Sanin Nassosi da kyau yana ƙarfafa mu da kuma shirya mu don hidimar. Kamar yadda muke bukatar mu ci abinci don mu ci gaba da rayuwa, dole ne mu ci abinci na ruhaniya a kai a kai don mu ci gaba da aikin wa’azi. Karanta Kalmar Allah a kullum da kuma cin ‘abinci a lotonsa’ zai iya ba mu ƙarfi a hidima.—Mat. 24:45-47.
Elżbieta ta yi canje-canje masu muhimmanci a salon rayuwarta don ta kyautata hidimarta. Ta ce: “Na rage lokacin da nake kallon talabijin sosai don na samu ƙarin lokaci na shirya hidima. Sa’ad da na karanta Littafi Mai Tsarki a kowane, ina tunanin mutanen da nake saduwa da su a yankin. Sai na duba nassosi da talifofi da za su iya taimakonsu.”
Samun isashen hutu zai taimake ka ka samu ƙarfi sosai kuma ya taimake ka ka yi hidimar iya ƙoƙarinka. A wani ɓangare kuma, yawan nishaɗi zai iya kasance da lahani ga aikinka. Andrzej, wani mai shela da himma, ya lura: “Rashin hutu na kawo yawan gajiya kuma da hakan a hankali mutum zai yi sanyin gwiwa. Ina yin iya ƙoƙarina na guji hakan.”—M. Wa. 4:6.
Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu, mutane kaɗan ne kawai suke amincewa da bishara. Amma, Jehobah ba zai taɓa manta aikinmu ba. (Ibran. 6:10) Ko da mutane da yawa ba sa son su yi magana da mu, suna iya yin magana game da ziyararmu bayan mun bar gidansu. Sakamakon yana iya zama kamar abin da muka karanta game da Ezekiel: Mutane “za su sani da annabi a cikinsu.” (Ezek. 2:5) Hakika, hidimarmu ba mai sauƙi ba ce, amma muna samun amfani ta wurin yin ta kuma mutane da suka saurara su ma za su amfana.
“Fita hidima yana sa mu yafa sabon hali kuma mu nuna ƙauna ga Allah da kuma maƙwabtanmu,” in ji Zygmunt. “Gata ne mu sa hannu a wannan aiki mai ceton rai.” Andrzej ya daɗa, “ba za a sake wannan aikin sosai haka ko kuma a irin wannan yanayin ba.” Kai ma za ka samu albarka mai yawa ta wurin nacewa a hidimar a yau.—2 Kor. 4:1, 2.
[Hotunan da ke shafi na 31]
Kula da bukatunmu na ruhaniya da na zahiri na taimakonmu mu jimre a hidimar