Ka Yi Farin Ciki A Aikin Almajirantarwa
‘Ku tafi fa, ku almajirtar.’—MAT. 28:19.
1-3. (a) Yaya mutane da yawa suke ji game da zarafin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
WATA ’yar’uwa da take hidima a rukunin yaren Hindi a Amirka ta rubuta cewa: “Ina nazari da wata iyali daga Pakistan makonni goma sha ɗaya yanzu, kuma mun shaƙu. Ina hawaye idan na tuna cewa ba da daɗewa ba wannan iyalin za ta koma Pakistan. Ina baƙin ciki ba don kawai zan yi rashin abokantakarsu ba, amma don farin ciki da nake yi sa’ad da nake koya musu game da Jehobah.”
2 Kamar ’yar’uwar nan, ka taɓa shaida farin ciki da ake samu ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wani? Yesu da almajiransa na ƙarni na farko sun yi farin ciki sosai wajen yin aikin almajirantarwa. Sa’ad da almajirai saba’in da Yesu ya koyar da su suka dawo da rahoto mai kyau, Yesu da kansa “ya yi murna ta wurin Ruhu Mai-tsarki.” (Luk 10:17-21) Hakazalika, mutane da yawa a yau suna farin ciki sosai a aikin almajirtarwa. Hakika, a shekara ta 2007, masu shelar mulki da ƙwazo da suke farin ciki sun gudanar da aƙalla nazarin Littafi Mai Tsarki miliyan shida da rabi a kowane wata!
3 Amma, wasu masu shela ba su sa hannu a aikin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu ba tukuna. Wataƙila wasu ba su yi nazari da wani ba a shekaru na baya bayan nan. Waɗanne ƙalubale ne za mu iya fuskanta yayin da muke ƙoƙarin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu sha kan waɗannan ƙalubalen? Wace albarka ce za mu samu sa’ad da muka yi iyakar ƙoƙarinmu wajen yin biyayya da umurnin Yesu: ‘Ku tafi fa, ku almajirtar’?—Mat. 28:19.
Ƙalubalen da Za Su Iya Hana Mu Farin Ciki
4, 5. (a) Ta yaya mutane da yawa suke mai da martani a wasu ɓangarorin duniya? (b) Wane ƙalubale masu shela suke fuskanta a wasu wurare?
4 A wasu ɓangarorin duniya, mutane suna karɓan littattafanmu kuma suna ɗokin mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Wasu ma’aurata daga Australiya da suke hidima na ɗan lokaci a ƙasar Zambiya sun rubuta: “Labarin gaskiya ne. Mutane suna son a yi musu wa’azi sosai a Zambiya. Wa’azi na kan hanya ne ya fi ban sha’awa! Mutane suna zuwa wajenmu, wasu suna neman jaridu na musamman.” A wata shekara da ta wuce, ’yan’uwa a ƙasar Zambiya sun gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki fiye da 200,000, wato, aƙalla, mutum ɗaya yana gudanar da fiye da nazarin Littafi Mai Tsarki guda ɗaya.
5 Amma, a wasu wurare, yana yi wa masu shela wuya su ba da littattafai su kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Me ya sa? Sau da yawa, mutane ba sa gida sa’ad da mai shela ya ƙwanƙwasa ƙofarsu, yayin da waɗanda suke gida mai yiwuwa ba sa son su ji game da addini. Wataƙila an yi renonsu ne a iyalin da ba a bin addini ko kuma ba sa son munafuncin da ake yi a addinin ƙarya. Makiyayan ƙarya sun wahalar da mutane da yawa, kuma sun watsar da su. (Mat. 9:36) Saboda waɗannan dalilan, irin waɗannan mutanen ba sa son su tattauna game da Littafi Mai Tsarki.
6. Wane kasawa wasu suke fama da shi?
6 Wasu masu shela masu aminci suna fuskantar ƙalubale dabam da zai iya hana su farin ciki. Ko da yake akwai lokacin da suke da ƙwazo sosai a aikin almajirtarwa, yanzu rashin lafiya ko kuma tsufa ya hana su yin abubuwan da suke yi a dā. Yi la’akari kuma da wasu hani da muke iya ɗora wa kanmu. Alal misali, kana jin ba ka cancanci gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki ba? Kana iya jin yadda Musa ya ji sa’ad da Jehobah ya umurce shi ya yi wa Fir’auna magana. Musa ya ce: “Ya Ubangiji, ni ba mai-iya baki ba ne, ko dā, ko kuwa yanzu da ka yi magana da bawanka.” (Fit. 4:10) Tsoron kasawa yana da nasaba da jin rashin cancanta. Muna iya damuwa cewa mutum ba zai zama almajiri domin mu ba ƙwararrun malamai ba ne. Domin mu guji fuskantar wannan, muna iya ƙin gudanar da nazari. Ta yaya za mu sha kan waɗannan ƙalubalen da aka ambata?
Ka Shirya Zuciyarka
7. Menene ya motsa Yesu a hidimarsa?
7 Mataki na farko shi ne mu shirya zuciyarmu. Yesu ya ce: ‘Daga cikin yalwar zuciya baki ya ke zance.’ (Luk 6:45) Abin da ke motsa Yesu a hidimarsa ita ce damuwa da zaman lafiyar mutane. Alal misali, sa’ad da ya lura cewa ’yan’uwansa Yahudawa ba sa bin Allah, “ya yi juyayi a kansu.” Ya gaya wa almajiransa: “Girbi hakika yana da yawa, . . . Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata cikin girbinsa.”—Mat. 9:36-38.
8. (a) Yana da kyau mu yi tunanin menene? (b) Menene muka koya daga abin da wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki ta faɗa?
8 Sa’ad da muke yin aikin almajirtarwa, yana da kyau mu yi tunani sosai game da yadda muka amfana domin wani ya ba da lokaci sosai ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu. Ka yi tunanin mutanen da za mu sadu da su a hidima da kuma yadda za su amfana ta wajen jin saƙon da muke sanarwa. Wata mata ta rubuta wa ofishin reshe na ƙasar da take zama cewa: “Ina son na gaya muku yadda nake godiya ga Shaidu da suke zuwa su koyar da ni a gidana. Na san cewa wani lokaci suna gajiya da ni domin ina da tambayoyi da yawa kuma ina sa su daɗe sosai. Amma suna haƙuri da ni kuma suna ɗokin su koya mini abin da suka koya. Na gode wa Jehobah da Yesu cewa na san waɗannan mutanen.”
9. A kan menene Yesu ya mai da hankalinsa, ta yaya za mu yi koyi da shi?
9 Hakika, ba kowa ba ne ya karɓi koyarwar Yesu. (Mat. 23:37) Wasu sun ɗan bi shi amma suka ƙi amincewa da koyarwarsa kuma “ba su ƙara tafiya tare da shi ba.” (Yoh. 6:66) Amma, Yesu bai ƙyale hakan ya sa ya ji cewa saƙonsa ba shi da amfani ba. Ko da yake yawancin iri da ya shuka ba su ba da ’ya’ya ba, Yesu ya mai da hankali ga nagartar da yake yi. Ya ga cewa gonaki sun riga sun isa girbi kuma ya yi farin ciki sosai wajen ba da taimako a wannan girbin. (Karanta Yohanna 4:35, 36.) Maimakon mu yi ta kallon ƙasar da aka shuka hatsi kawai, ya kamata mu mai da hankali ga girbi da za mu iya yi a yankinmu. Bari mu mai da hankali ga yadda za mu kasance da irin wannan ra’ayi mai kyau.
Ka Yi Shuka da Shirin Girbi
10, 11. Menene za ka yi don ka ci gaba da farin ciki?
10 Manomi yana shuka da ra’ayin cewa zai yi girbi wata rana. Hakanan ma, muna bukatar mu yi wa’azi da ra’ayin soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan kana fita hidimar fage a kai a kai amma mutane kaɗan ne kawai kake samu a gida ko kuma ka kasa samun waɗanda ka koma ziyara a wurinsu fa? Hakan zai iya sa mutum baƙin ciki. Ya kamata ka daina fita hidimar ƙofa-ƙofa ne? A’a! Har ila ana saduwa da mutane da farko ta wannan hanyar wa’azi mai kyau da ake yi da daɗewa.
11 Amma, don ka ci gaba da yin farin ciki, kana iya faɗaɗa hanyoyin da kake yin wa’azi, wataƙila ta wajen neman wasu hanyoyi na samun mutane. Alal misali, ka taɓa gwada yi wa mutane wa’azi a kan titi ko kuma a wuraren aikinsu? Kana iya samun mutane ta wajen yin musu tarho ko kuma ka karɓi lambar wayar waɗanda ka yi wa wa’azin Mulki don ka riƙa kiransu. Ta wajen nacewa da kuma daidaitawa a hidimarka, za ka yi farin cikin samun mutanen da za su saurari saƙon Mulki.
Jimre wa Wariya
12. Menene za mu iya yi idan mutane da yawa a yankinmu ba sa son su ji wa’azi?
12 Idan mutane da yawa a yankinku ba sa son ji game da addini fa? Kana iya soma tattauna abubuwan da suke so da su! Manzo Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa masu bi a Koranti: “Na zama kamar Ba-yahudi ga Yahudawa . . . ga waɗanda ba su da shari’a, na zama kamar marar-shari’a, ba kuwa marar-shari’a ga Allah ba.” Menene manufar Bulus? Ya ce: “Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko da ƙaƙa in ceci waɗansu.” (1 Kor. 9:20-22) Muna iya neman batutuwan da mutanen da suke yankinmu za su so? Mutane da yawa da ba sa son addini suna son su kyautata dangantakar iyalinsu. Wataƙila suna neman rayuwa mai ma’ana. Muna iya yin wa’azin Mulki a hanyar da irin waɗannan mutanen za su so?
13, 14. Ta yaya za mu daɗa ga farin cikin da muke samu a aikin almajirtarwa?
13 Masu shela da yawa sun ƙara samun farin ciki a aikin almajirtarwa, har a wuraren da yawancin mutane ba sa son jin wa’azi. Ta yaya? Ta wajen koyan wani yare. Wasu ma’aurata ’yan shekara sittin da wani abu sun gano cewa akwai dubban ɗalibai ’yan ƙasar Sin da iyalinsu da suke da zama a yankin ikilisiyarsu. Maigidan ya ce: “Saboda haka, an ƙarfafa mu mu koyi yaren Sin. Ko da yake hakan na nufin ba da lokaci kowane rana wajen koyan yaren, mun yi farin ciki domin mun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen Sin masu yawa da ke yankinmu.”
14 Ko da ba ka iya koyan wani yare, za ka iya yin amfani da kyau da ƙasidar nan Good News for People of All Nations sa’ad da ka sadu da waɗanda suke wani yare. Kana kuma iya samun littattafai a yaren mutanen da ka sadu da su. Hakika, ana bukatar lokaci da ƙoƙari don a yi magana da waɗanda suke wani yare da al’ada. Amma ka tuna da ƙa’idar da ke cikin Kalmar Allah: “Wanda ya ke shuka da yalwa, da yalwa kuma zai girbe.”—2 Kor. 9:6.
Ya Shafi Dukan Ikilisiya
15, 16. (a) Me ya sa dukan ikilisiya ce take da hakkin yin almajirtarwa? (b) Wane matsayi ne tsofaffi suke da shi?
15 Hakika, samun almajirai ba aikin mutum ɗaya ba ne ba kawai. Maimakon haka, aikin dukan ikilisiya ce. Me ya sa? Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:35) Sa’ad da ɗaliban da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su suka halarci taro, ƙaunar da muke nunawa a taronmu sau da yawa tana burge su. Wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki ta rubuta: “Ina jin daɗin halartan taro sosai. Mutanen suna yi mini maraba sosai!” Yesu ya ce iyalan waɗanda suka zama mabiyansa za su iya yi musu hamayya. (Karanta Matta 10:35-37.) Amma, ya yi alkawari cewa za su samu “yan’uwa maza, da ’yan’uwa mata, da uwaye, da ’ya’ya” na ruhaniya masu yawa a cikin ikilisiya.—Mar. 10:30.
16 ’Yan’uwanmu tsofaffi musamman suna taimakawa sosai wajen taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki su sami ci gaba. A wace hanya? Ko da wasu cikin tsofaffin ba sa iya gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da kansu, kalaminsu a taron ikilisiya yana ƙarfafa bangaskiyar dukan waɗanda suka saurare su. Tarihinsu na yin tafiya “cikin hanyar adalci” ya daɗa sa ikilisiya ta yi kyau kuma hakan na jawo mutane masu zuciyar kirki zuwa ƙungiyar Allah.—Mis. 16:31.
Abin da Za Mu Yi Don Mu Daina Jin Ba Mu Cancanta Ba
17. Menene za mu yi don mu daina jin ba mu cancanta ba?
17 Menene za ka yi idan kana jin ba ka cancanta ba? Ka tuna cewa Jehobah ya taimaki Musa ta wajen ba shi ruhunsa mai tsarki da kuma abokin aiki, ɗan’uwansa, Haruna. (Fit. 4:10-17) Yesu ya yi alkawari cewa ruhun Allah zai tallafa wa aikinmu na wa’azi. (A. M. 1:8) Ƙari ga haka, Yesu ya aika da masu aiki su yi wa’azi bibbiyu. (Luk 10:1) Saboda haka, idan yana yi maka wuya ka gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki, ka yi addu’a don ruhun Allah ya ba ka hikima kuma ka nemi wanda za ku yi wa’azi tare da zai sa ka kasance da ƙarfin zuciya da kuma wanda zai taimake ka sosai. Yana da ban ƙarfafa mu tuna cewa Jehobah ya zaɓi ya yi amfani da mutanen da ba komi ba, wato, “raunana na duniya” don ya cim ma wannan aiki na musamman.—1 Kor. 1:26-29.
18. Ta yaya za mu sha kan tsoron kasa taimakon ɗalibin Littafi Mai Tsarki?
18 Ta yaya za mu sha kan tsoron kasa taimaka wa ɗalibin Littafi Mai Tsarki? Yana da kyau mu tuna cewa samun almajirai ba kamar dafa abinci ba ne, da daɗinsa ko rashin daɗinsa ya dangana ne kawai a kan mutum ɗaya, wato, wanda ya dafa abincin. Maimakon haka, samun almajirai ya ƙunshi fiye da mutum ɗaya. Jehobah ne ya fi yin aiki na musamman, da yake shi ne yake jawo mutane zuwa wurinsa. (Yoh. 6:44) Mu da kuma sauran mutane cikin ikilisiya muna iyakar ƙoƙarinmu mu koyar da kyau don mu taimaka wa ɗalibin ya samu ci gaba. (Karanta 2 Timothawus 2:15) Kuma ɗalibin yana bukatar ya aikata bisa abin da ya koya. (Mat. 7:24-27) Idan mutum ya daina nazarinsa na Littafi Mai Tsarki, hakan zai iya sa mu baƙin ciki. Muna sa rai cewa ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su yi zaɓi mai kyau, amma kowane mutum ne zai “kawo lissafin kansa ga Allah.”—Rom. 14:12.
Menene Sakamakon Haka?
19-21. (a) Waɗanne amfani za mu samu daga gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki? (b) Ta yaya Jehobah yake ɗaukan dukan waɗanda suke aikin wa’azi?
19 Gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na sa mu mai da hankali ga fara biɗan Mulkin Allah. Yana kuma sa gaskiyar Kalmar Allah ta yi jijiya sosai a cikin zuciyarmu. Me ya sa? Wani majagaba mai suna Barak ya yi bayani: “Gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki yana tilasta maka ka zama mai nazarin Kalmar Allah sosai. Na fahimci cewa dole ne na tabbatar wa kai na gaskiyar Kalmar Allah kafin na koya wa wani da kyau.”
20 Idan ba ka gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki, hakan yana nufin cewa hidimarka ga Allah ba ta da amfani ne? A’a! Jehobah yana ɗaukan duk wani ƙoƙarin da muke yi don mu yabe shi da tamani. Dukan waɗanda suke aikin wa’azi “abokan aiki na Allah ne.” Amma, gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na kawo mana ƙarin farin ciki sa’ad da muke ganin yadda Allah yake sa iri da muka shuka ya yi girma. (1 Kor. 3:6, 9) Wata majagaba mai suna Amy ta ce: “Sa’ad da kake ganin ɗalibi na Littafi Mai Tsarki ya samu ci gaba, hakan na sa ka yi godiya sosai ga Jehobah don ya yi amfani da kai ya ba wannan mutumin kyauta mai ban al’ajabi, wato, zarafin sanin Jehobah da kuma samun rai madawwami.”
21 Yin iyakacin ƙoƙarinmu mu soma da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu mai da hankali ga bauta wa Allah yanzu kuma mu ƙarfafa begenmu na tsira zuwa cikin sabuwar duniya. Da taimakon Jehobah, muna iya taimaka mu ceci waɗanda suka saurare mu. (Karanta 1 Timothawus 4:16.) Wannan zai zama abin farin ciki!
Ka Tuna?
• Waɗanne ƙalubale ne ke hana wasu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki?
• Menene za mu iya yi idan mutane da yawa a yankinmu ba sa son jin wa’azi?
• Waɗanne sakamako za mu iya samu daga gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki?
[Hotunan da ke shafi na 9]
Kana faɗaɗa hanyoyin da kake wa’azi don ka samu mutane masu zuciyar kirki?