“Waƙar Teku” Littafin Tarihi da Aka Rubuta Tsakanin Littattafan Tarihi Biyu
A RANAR 22 ga Mayu, a shekara ta 2007, an kai sashe na naɗaɗɗen littafin Ibrananci da aka rubuta daga ƙarni bakwai ko takwas A.Z., zuwa ma’adanar kayayyakin tarihi na Isra’ila da ke Urushalima. Wannan sashe ne na littafin Fitowa 13:19–16:1. Ya haɗa da abin da ake kira “Waƙar Teku,” wato, waƙar cin nasara da Isra’ilawa suka rera bayan an cece su ta hanyar mu’ujiza a Jan Teku. Me ya sa nuna wannan littafin ya zama abu mai muhimmanci?
Yana da muhimmanci ne domin lokacin da aka rubuta littafin. An rubuta naɗaɗɗun littattafan Tekun Gishiri ne tsakanin ƙarni na uku K.Z., da ƙarni na farko A.Z. Kafin a gano su kusan shekaru 60 da suka shige, littafin Ibraniyawa da ya fi daɗewa shi ne Aleppo Codex, wanda aka rubuta a shekara ta 930 A.Z. Ban da wasu sashe, babu wasu littattafan Ibrananci da aka gano cikin waɗannan ɗarurruwan shekaru suka shige.
James S. Snyder shugaban ma’adanar kayayyakin tarihi na Isra’ila ya ce: “Littafin Waƙar Teku littafin tarihi ne da aka rubuta tsakanin Dead Sea Scrolls (Naɗaɗɗen Littafi na Tekun Gishiri) da Aleppo Codex.” In ji shi, wannan littafin da wasu sashen Littafi Mai Tsarki na dā “misali ne na musamman da ya nuna yadda aka adana littafin kuma ba a canja kalmomin ba.”
Sashen littafin yana cikin littattafai masu yawa da aka gano a ƙarshen ƙarni na 19 a majami’a da ke Kairo, a ƙasar Masar. Amma, wani mai tara littattafan Ibrananci bai san muhimmancinsa ba sai da ya je ya tuntuɓi wani masani a ƙarshen shekarun 1970. An rubuta kwanan watan a wannan lokacin kuma aka adana shi har sai lokacin da aka kai shi ma’adanar kayayyakin tarihi a Isra’ila.
Da yake magana a kan muhimmancin sashen littafin, Adolfo Roitman shugaban Ɗakin Ajiye Kayayyakin Tarihi a Isra’ila kuma mai kula da Dead Sea Scrolls (Naɗaɗɗen Littafi na Tekun Gishiri) ya ce: “Littafin tarihi na Waƙar Teku ya bayyana tabbacin yadda aka fassara juyin Ibrananci na Littafi Mai Tsarki a ƙarnuka da yawa da suka shige. Abin mamaki ne cewa Waƙar Teku ta kasance kamar yadda take a ƙarnuka na 7 da 8 da suka wuce.”
Littafi Mai Tsarki hurarriyar Kalmar Allah ce, kuma Jehobah shi ne ya adana shi. Bugu da ƙari, marubutan Nassosi sun yi hakan da kyau. Babu shakka, Littafi Mai Tsarki da muke amfani da shi a yau tabbatacce ne.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 32]
Courtesy of Israel Museum, Jerusalem