Yin Wa’azi A Kasuwa
A BIRNIN Atina, kowace rana manzo Bulus yana zuwa kasuwa ya yi wa’azin bishara game da Yesu. (A. M. 17:17) Bulus ya zaɓi kasuwa saboda mutanen Atina suna yawan zama a kasuwa.
Bayan kusan shekara 2,000, har ila mutanen Jehobah suna yin wa’azin Mulkin Allah a kasuwa. Me ya sa? Saboda za a sami mutane da yawa a kasuwa. A yau, kasuwa tana iya zama manyan kantuna inda mutane suke yin sayayya. Bayan da suka sami zarafi a wajen mai kantin, wasu Shaidu suna yin amfani da teburi su ajiye littatafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki.
Alal misali, a wani babban kanti da ke New Jersey a Amirka, an baza wasu littatafai da suke tattauna “Yadda Za a Daraja Iyali.” Menene sakamakon? A rana guda, an ba da littatafai guda 153 a harsuna shida.
Wata mata da ta je wajen da aka ajiye littattafan ta saurari bayanin da wata Mashaidiya take yi. Matar ta yarda cewa yana da muhimmanci mu kasance da ra’ayin Allah a rayuwarmu da kuma iyalinmu. Ta karɓi waɗannan littattafan: Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, Asirin Farin Ciki na Iyali da kuma Questions Young People Ask—Answers That Work.
Da rana, wani mutum ya wuce wajen da aka ajiye littattafan sa’ad da yake son ya shiga shagon da ke kusa da wajen. Sai idonsa ya je wajen littafin Young People Ask. ’Yar’uwar da take wajen ta lura cewa mutumin yana sha’awar littafin. Sai ta tambaye shi, “Akwai littafin da kake so a cikin waɗannan ne?” Ya ce e, kuma ya nuna littafin nan Young People Ask. Mutumin ya rigaya ya miƙa hannu ya ɗauki littafin. Ya ce wai yana da yara uku. Da suka ci gaba da tattaunawa, sai ya ce wai yana tattaunawa da yaransa sau ɗaya a sati. Yaransa guda biyu matasa ne. Sa’ad da yake duba littafin, ya ce zai amfane shi a wajen tattaunawa da iyalinsa. Mashaidiyar kuma ta nuna masa littafin nan Asirin Farin ciki na Iyali, ta ce shi da matarsa za su sami wasu shawarwari masu kyau da za su shafi rayuwar iyalinsu. Mutumin ya yi farin ciki kuma ya ba da nasa gudummawa, ya kuma yarda wani Mashaidi ya ziyarce su.
Yaya Shaidun suka ji game da wa’azinsu a manyan kantuna? Wata ’yar’uwa ta ce, “Na ji daɗin irin wannan wa’azi, yana da kyau.” Wata ’yar’uwa kuma ta ce: “Jehobah ya ce za a yi wa’azin bishara a dukan duniya. A Paramus da ke New Jersey, yau, wannan bisharar ta motsa zuciyar mutane daga harsuna dabam dabam. Ina farin ciki da yake ina cikin wannan shirin. Dukan waɗanda suka yi wa’azin suna farin ciki. Babu wanda yake so ya tafi da muka gama wa’azin.”
Za ka iya yin shelar bishara a hanyoyin dabam dabam? Ainihin yadda muke yin wa’azi shi ne zuwa gida gida. (A. M. 20:20) Amma, za ka so ka yi wa’azi a kasuwa ko kuma manyan kantuna?