Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 9/15 pp. 16-20
  • Ka Riƙe “Igiya Riɓi Uku” Cikin Aure

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Riƙe “Igiya Riɓi Uku” Cikin Aure
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sa Jehobah ya Kasance Cikin Aurenka
  • Sa’ad da Matsaloli Suka Taso
  • Ƙarin Albarkatai
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 9/15 pp. 16-20

Ka Riƙe “Igiya Riɓi Uku” Cikin Aure

“Igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.”—M. WA. 4:12.

1. Wanene ya haɗa mutane biyu na farko a aure?

BAYAN ya halicci itatuwa da dabbobi, Jehobah Allah ya halicci mutum na farko, Adamu. Daga baya Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zurfi sai ya yi amfani da ɗaya cikin haƙarƙarin Adamu ya yi masa mataimakiya ta ƙwarai. Da ya ganta sai Adamu ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.” (Far. 1:27; 2:18, 21-23) Jehobah ya nuna ya amince da halittar mace ta farko, ya haɗa mutane biyu na farko a aure kuma ya albarkace su.—Far. 1:28; 2:24.

2. Ta yaya Shaiɗan ya kawo rabuwa tsakanin Adamu da Hauwa’u?

2 Abin baƙin ciki, ba da daɗewa ba aka lalata auren da Allah ya haɗa. Ta yaya? Mugun ruhu da ake kira Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u ta ci ’ya’yan itace da aka hana su ci. Ba da daɗewa ba, Adamu ya bi matarsa suka yi tawaye ga ikon Allah na yin sarauta da kuma ja-gora mai kyau. (Far. 3:1-7) Sa’ad da Jehobah ya tambayi ma’auratan abin da suka yi, ya zama a bayyane cewa dangantakarsu ta riga ta lalace. Adamu ya ga laifin matarsa, ya ce: “Macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.”—Far. 3:11-13.

3. Wane irin ra’ayi da bai dace ba ne wasu Yahudawa suka gabatar?

3 Cikin ƙarnuka da suka wuce, Shaiɗan ya yi amfani da hanyoyi dabam dabam don ya kawo rashin jituwa cikin aure. Alal misali, wani lokaci ya yi amfani da shugabannin addinai don su gabatar da ra’ayi game da aure da bai yi daidai da Nassi ba. Wasu shugabannan Yahudawa suna rage amfanin mizanan Allah, sun bar magidanta su kashe aure da matarsu don abubuwa da ba su da muhimmanci kamar sa gishiri da yawa a abinci. Amma Yesu ya ce: “Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi.”—Mat. 19:9.

4. Menene ya lalata tsarin aure a yau?

4 Har ila Shaiɗan yana ƙoƙarin ya lalata gami na aure. Auren ’yan daudu, mutane biyu da suke zama tare da ba su auri juna ba, da kuma saurin kashe aure sun nuna cewa yana yin nasara sosai wajen raba aure. (Ka karanta Ibraniyawa 13:4.) A matsayinmu na Kiristoci, menene za mu yi don kada ra’ayin da bai dace ba game da aure da ke ko’ina ya shafe mu? Bari mu bincika wasu abubuwa da ke sa a yi farin ciki a aure.

Ka Sa Jehobah ya Kasance Cikin Aurenka

5. Menene furci “igiya riɓi uku” yake nufi a cikin aure?

5 Don a yi nasara a aure, ya kamata a haɗa Jehobah cikin dangantakar. Kalmarsa ta ce: “Igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.” (M. Wa. 4:12) “Igiya riɓi uku” furci ne na alama. Wannan kwatanci a cikin aure ya ƙunshi mata da miji, wato, igiya biyu na farko da ta haɗu da igiya na musamman, Jehobah Allah. Haɗa kai da Allah na ƙarfafa ma’aurata su jimre da matsaloli, kuma hakan zai sa su yi farin ciki sosai a aurensu.

6, 7. (a) Menene Kiristoci za su iya yi don su tabbata cewa Allah yana cikin aurensu? (b) Menene wata ’yar’uwa take so game da maigidanta?

6 Menene ma’aurata za su yi don su tabbata cewa aurensu yana kama da irin wannan igiya riɓi uku? Mai zabura Dauda ya rera waƙa: “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, Hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” (Zab. 40:8) Haka nan ma, ƙaunarmu ga Allah tana motsa mu mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Saboda haka, ya kamata ma’aurata su ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah kuma su yi farin ciki wajen yin nufinsa. Ya kamata ma’aurata su yi ƙoƙari su ƙarfafa ƙaunar abokin aurensu da Allah.—Mis. 27:17.

7 Idan da gaske dokar Allah tana cikin zuciyarmu, za mu kasance da halaye kamar bangaskiya, bege, da ƙauna kuma za su taimaki gamin aurenmu. (1 Kor. 13:13) Sandra wata ’yar’uwa da ta yi shekara 50 da yin aure ta ce: “Abin da maigidana yake yi da na fi so shi ne shawarwari da umurnin da yake bayarwa daga cikin Littafi Mai Tsarki da kuma ƙaunarsa ga Jehobah wanda ya fi ƙaunar da yake yi mini.” Magidanta, za a iya yin irin wannan furcin game da ku?

8. Menene ake bukata don a sami “amfani” mai kyau a aure?

8 Ma’aurata, kuna sa dangantakarku da Jehobah da kuma ayyuka na Mulki su zama na farko a rayuwarku kuwa? Kuna ɗaukan abokin aurenku a matsayin ’yan’uwanku a hidimar Jehobah kuwa? (Far. 2:24) Sarki Sulemanu ya rubuta: “Biyu sun fi ɗaya, gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu.” (M. Wa. 4:9, 10; LMT) Hakika, dole ne mata da miji su yi ƙoƙari don su samu “amfani” mai kyau a aurensu, hakan zai kawo dangantaka na dindindin da Allah ya sa albarka.

9. (a) Wane hakki ne magidanta suke da shi? (b) Bisa abin da Kolosiyawa 3:19 ta ce, yaya ya kamata miji ya bi da matarsa?

9 Ƙoƙarin da mata da miji suke yi don su cika farillan Allah ne zai nuna ko yana cikin aurensu. Magidanta ne ainihi suke da hakkin yin tanadi na zahiri da na ruhaniya a iyalinsu. (1 Tim. 5:8) An ƙarfafa su su yi la’akari da yadda matansu suke ji. Kolosiyawa 3:19 ta ce: “Ku mazaje, ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi [sosai] da su.” Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ba da bayanin wannan furcin cewa fushi “sosai” ya ƙunshi “yi musu baƙar magana, ko dūka, da kuma ƙin kula da su, yi musu tanadi, kāriya da taimako.” Hakika, irin wannan halin bai dace da iyalin Kirista ba. Maigida da yake shugabancinsa a hanya mai kyau na sa matarsa ta kasance a shirye ta yi masa biyayya.

10. Wane irin hali ne ya kamata mata Kirista su nuna?

10 Ya kamata mata Kirista da suke so su sa Jehobah cikin aurensu su cika farillansa. Manzo Bulus ya rubuta: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji. Gama miji kan mata ya ke, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne, shi da kansa fa mai-ceton jiki ne.” (Afis. 5:22, 23) Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u ta wajen yin ƙarya cewa ’yanci daga Allah zai kawo farin ciki na dindindin. Hakika, ana ganin halin ’yancin kai a cikin aure masu yawa. Amma, ga mata masu ruhaniya yin biyayya ga shugabansu abin farin ciki ne. Sun tuna cewa Jehobah ya sa Hauwa’u ta zama mataimakiya “mai-dacewa” ga mijinta, kuma Allah ya ɗauki wannan matsayin da daraja. (Far. 2:18) Hakika, mace Kirista da ta ba da haɗin kai ga wannan tsarin “kambi” ce ga mijinta.—Mis. 12:4.

11. Menene wani ɗan’uwa ya ce ya taimaki aurensa?

11 Wani abu da zai taimaki ma’aurata su sa Allah ya kasance cikin aurensu shi ne su yi nazarin Kalmar Allah tare. Gerald da ya yi shekara 55 da yin aure kuma yana farin ciki ya ce: “Abu mafi muhimmanci cikin aure da zai yi nasara shi ne karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki tare.” Ya daɗa, “Yin abubuwa tare, musamman abubuwa na ruhaniya, na sa ma’aurata su kusaci juna da kuma Jehobah.” Yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare na taimakon iyali su riƙa tuna da mizanan Jehobah, su ƙarfafa ruhaniyarsu da shi, kuma su sami cin gaba.

12, 13. (a) Me ya sa yake da muhimmanci ma’aurata su yi addu’a tare? (b) Waɗanne ayyuka na ruhaniya ne suke ƙarfafa aure?

12 Ma’aurata masu farin ciki suna addu’a tare. Sa’ad da miji ya ‘zazzage zuciyarsa’ yana roƙo da ya yi daidai da yanayinsu, hakan zai ƙarfafa gamin aurensu. (Zab. 62:8) Alal misali, zai fi kyau ka kawar da kowane rashin jituwa da abokiyar aurenka bayan kun yi wa Maɗaukaki addu’a don ja-goranci! (Mat. 6:14, 15) Cikin jituwa da wannan addu’a, zai dace kowannensu ya tsai da shawara ‘yana haƙuri da juna, yana gafarta ma juna.’ (Kol. 3:13) Ka tuna cewa addu’a tana nuna cewa kana dogara ga Allah. Sarki Dauda ya ce: “Idanun dukan mutane suna sauraro a gareka.” (Zab. 145:15) Idan muka dogara ga Allah cikin addu’a, ba za mu yi alhini ainun ba, mun san cewa ‘yana kula da mu.’—1 Bit. 5:7.

13 Wata hanya ta musamman na sa Jehobah ya kasance cikin aure ita ce ta wajen halartar taron ikilisiya da kuma fita hidimar fage tare. A taronmu, ma’aurata suna koyan yadda ake ƙin “makamai” da Shaiɗan yake amfani da su don ya raba iyalai. (Afis. 6:11) Mata da miji da suke fita hidima tare a kai a kai suna koyan su ‘kafu yadda ba sa kawuwa.’—1 Kor. 15:58.

Sa’ad da Matsaloli Suka Taso

14. Waɗanne abubuwa ne ke kawo matsala a aure?

14 Hakika, shawarwari na sama ba sabon abu ba ne, amma yana da kyau ka tattauna su da abokin aurenka. Ka ga ko da akwai wurin da kake bukata ka mai da wa hankali a cikin aurenka. Amma Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa waɗanda Allah yake cikin aurensu “za su sha wahala a cikin jiki.” (1 Kor. 7:28) Domin ajizancin ’yan adam, mugun tasiri na wannan muguwar duniya, da tarkunan Iblis, auren bayin Allah masu aminci za su iya fuskantar matsi sosai. (2 Kor. 2:11) Amma Jehobah yana taimakonmu mu jimre da irin wannan matsin. Hakika, za a iya yin hakan. Ayuba mutum mai aminci ya yi hasarar dabbobinsa, bayinsa, da yaransa. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Cikin wannan duka Ayuba ba ya yi zunubi ba, ba ya kuwa saɓi Allah ba.”—Ayu. 1:13-22.

15. Ta yaya matsi zai sa mutane su aikata, kuma ta yaya ma’aurata za su bi da wannan?

15 Matar Ayuba kuma ta ce masa: “Har yanzu kana riƙe da gaskiyarka?” Ka la’anta Allah, ka mutu.” (Ayu. 2:9) Hakika, sa’ad da masifu ko wasu yanayi masu wuya suka taso, alhini da ke tattare zai iya sa mutum ya aikata da garaje. Mutum mai hikima ya ce: “Zalumci ya kan maida mai-hikima wawa.” (M. Wa. 7:7) Idan abokiyar aurenka ta yi baƙar magana don wahala ko kuma “zalunci” ka yi ƙoƙari ka natsu. Amsawa da baƙar magana zai sa ɗaya ko dukanku ku faɗi wani abu da zai sa yanayin ya daɗa muni. (Ka karanta Zabura 37:8.) Saboda haka, ka ƙyale kowane “magana da rashin hankali” da za a yi don baƙin ciki ko kuma sanyin gwiwa.—Ayu. 6:3.

16. (a) Ta yaya ma’aurata za su yi amfani da kalmomin Yesu da ke Matta 7:1-5? (b) Me ya sa daidaitawa yake da muhimmanci a aure?

16 Ya kamata ma’aurata su yi tsammanin abin da zai yiwu. Wani zai lura da wasu halaye da ɗayan yake da shi kuma ya ce, ‘Zan iya canja ta ko kuma in canja shi.’ Za ka iya taimakon abokiyar aurenka ta yi gyara a hankali ta wajen nuna ƙauna da kuma yin haƙuri. Amma kada ka manta cewa Yesu ya kwatanta wanda yake kallon ɗan kuskuren wani da “haki” a cikin idon ɗan’uwansa amma ya kasa ganin “gungumen” da ke cikin idonsa ba. Yesu ya aririce mu: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku.” (Ka karanta Matta 7:1-5.) Hakan ba ya nufin cewa su rufe ido ga kasawa mai tsanani na juna ba. Robert, wanda ya yi aure na kusan shekaru 40 ya ce: “Gaya wa juna gaskiya da kuma kasancewa a shirye mu yarda da inda ake bukatar gyara zai bukaci ma’aurata su yi canje-canje a rayuwarsu.” Saboda haka, maimakon mu riƙa fushi don halayen da abokin aurenmu ba shi da su, mu koyi amincewa kuma mu yi farin ciki don halaye masu kyau da yake ko take da shi a yanzu.—M. Wa. 9:9.

17, 18. Sa’ad da matsaloli suka yi yawa, daga ina za mu samu taimako?

17 Ana iya fuskantar gwaji sa’ad da yanayi ya canja a rayuwa. Ma’aurata suna iya fuskantar kaluɓale sa’ad da suka haifi yara. Abokin aure ko kuma ɗa yana iya yin ciwo mai tsanani. Iyayensu da suka tsufa suna iya bukatar a kula da su sosai. Yara da suka yi girma suna iya zama nesa da gida. Kula da hakkin ikilisiya yana iya kawo wasu canje-canje. Dukan waɗannan suna iya kawo matsi da alhini ga dangantaka.

18 Idan matsala a aurenka ya sa ka ji ba za ka ci gaba da auren ba, menene za ka yi? (Mis. 24:10) Kada ka kasala! Shaiɗan zai fi so ɗaya cikin bayin Allah ya bar bauta ta gaskiya. Zai fi yin farin ciki idan ma’aurata suka yi haka. Saboda haka, ka yi iyakar ƙoƙarinka ka tabbata cewa ka riƙe igiya riɓi uku a cikin aurenka. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da labarai masu yawa na waɗanda suka kasance da aminci duk da gwaji mai tsanani. Alal misali, a wani lokaci, Dauda ya gaya wa Jehobah zuciyarsa yana cewa: “Ka yi mani jinƙai, ya Allah; gama mutum yana so . . . yana wahalshe ni yana faɗa da ni.” (Zab. 56:1) “Mutum” ya taɓa tsananta maka? Ko idan matsalarka daga wurin wani da nisa ko kuma wanda ya yi kusa da kai, ka tuna cewa Dauda ya jimre kuma kai ma za ka iya yin hakan. Dauda ya ce: “Na biɗi Ubangiji, ya amsa mini, ya kuma tsamarda ni daga dukan yawan tsorona.”—Zab. 34:4.

Ƙarin Albarkatai

19. Ta yaya za mu guji farmakin Shaiɗan?

19 A wannan lokaci na ƙarshe, ma’aurata suna bukatar su yi ‘ma junansu ta’aziya, su gina juna.’ (1 Tas. 5:11) Kada ku manta cewa, Shaiɗan ya ce muna kasancewa da aminci ga Jehobah don abubuwan da muke samu daga wajensa. Zai yi amfani da kowace hanya, har da raba aure don ya karya amincinmu ga Allah. Don mu hana farmakin Shaiɗan, muna bukatar mu dogara sosai ga Jehobah. (Mis. 3:5, 6) Bulus ya rubuta: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filib. 4:13.

20. Waɗanne albarkatai ne za a samu idan aka sa Allah cikin aure?

20 Albarka da ake samu wajen sa Allah ya kasance cikin aure tana da yawa. Hakan ya kasance gaskiya ga Joel da matarsa cikin shekaru 51 na aurensu. Ya ce: “Ina gode wa Jehobah koyaushe don matata da dangantakarmu na farin ciki. Mataimakiya ta ƙwarai ce.” Menene ya taimake su? “Mun yi ƙoƙari koyaushe mu riƙa nuna wa juna alheri, haƙuri, da kuma ƙauna.” Babu kowannenmu da zai yi hakan da kyau a wannan zamanin. Duk da haka, bari mu yi aiki tuƙuru mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma mu sa Jehobah ya kasance cikin aurenmu. Idan muka yi hakan, aurenmu zai zama kamar “igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.”—M. Wa. 4:12.

Ka Tuna?

• Menene yake nufi Jehobah ya kasance cikin aure?

• Menene ya kamata ma’aurata su yi idan matsala ta taso?

• Ta yaya za mu sani cewa Allah yana cikin aure?

[Hotuna a shafi na 18]

Yin addu’a tare na taimakon ma’aurata su fuskanci yanayi mai wuya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba