Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 6/15 pp. 16-17
  • Kana Shirye Ka Kāre Bangaskiyarka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Shirye Ka Kāre Bangaskiyarka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka Faranta Ran Malaminka
    Tambayoyin Matasa
  • Matasa—Jehovah Ba Zai Manta Da Aikinku Ba!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 6/15 pp. 16-17

Kana Shirye Ka Kāre Bangaskiyarka?

K A TAƁA fuskantar yanayin da ka ga ya kamata ka kāre bangaskiyarka? Ka yi la’akari da abin da ya faru da Susana, wata ’yar’uwa ’yar shekara 16 a ƙasar Paraguay. A cikin ajinsu na koyar da tarbiyya, an ambata cewa Shaidun Jehobah ba su amince da “Tsohon Alkawari ba,” Yesu Kristi, da Maryamu. Wasu kuma sun yi da’awar cewa Shaidun Jehobah mutane ne masu tsattsauran ra’ayi waɗanda suka gwammace su mutu da su kula da lafiyar jikinsu. Menene za ka yi?

Susana ta yi addu’a ga Jehobah kuma ta ɗaga hannunta. An kusan tashi ajin koyar da tarbiyya, sai ta gaya wa malamarsu ta ba ta izinin tattauna imaninta a matsayin ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah. Malamar ta yarda. A cikin makonni biyu, Susana ta shirya abin da za ta tattauna da ’yan ajin ta wajen yin amfani da mujallar nan mai suna Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su? Menene Suka Gaskata?

Ranar da za ta tattauna batun ya kai. Susana ta bayyana tushen sunan nan Shaidun Jehobah. Kuma ta bayyana begenmu na nan gaba da kuma dalilin da ya sa ba ma karɓan ƙarin jini. Bayan haka, ta gayyaci ’yan ajin su yi tambayoyinsu. Yawancin ɗaliban sun ɗaga hannunsu. Yadda yar’uwa ta bada amsa daga Nassi ya burge malamar.

Wani ɗalibi ya ce, “Na taɓa zuwa Majami’ar Mulki sau ɗaya kuma babu siffa ko ɗaya a ciki.” Malamar tana son ta san dalilin hakan. Susana ta karanta Zabura 115:4-8 da kuma Fitowa 20:4. Cike da mamaki, malamar ta ce, “Me ya sa cocinmu suke cike da siffofi bayan Littafi Mai Tsarki ya haramta hakan?”

Wannan tattaunawa ta wajen yin tambaya da ba da amsa ta ci gaba har tsawon minti 40. Sa’ad da Susana ta tambayi ’yan ajin ko za su so su kalli bidiyon nan No Blood—Medicine Meets the Challenge, sai dukansu suka ce e. Sai malamar ta ce za su ci gaba da tattauna batun a wan shekare. Bayan sun gama kallon bidiyon, Susana ta bayyana wasu hanyoyin jinya da ba su ƙunshi ƙarin jini ba da wasu cikin Shaidun Jehobah suka amince da su. Game da hakan, malamar ta ce: “Ban san cewa akwai wasu hanyoyin yin jinya masu yawa kamar haka ba; kuma ban taɓa sanin amfanin yin jinya ba tare da ƙarin jini ba. Shaidun Jehobah ne kawai ake yi wa wannan jinyar?” Sa’ad da ta ji cewa ba Shaidun Jehobah kaɗai ba ne ake yi wa irin wannan jinyar, malamar ta ce, “A duk lokacin da Shaidun Jehobah suka ƙara zuwa gidana, zan saurare su.”

Tattaunawa na minti 20 da Susana ta shirya ya kai tsawon awa uku. Bayan mako ɗaya, wasu ɗaliban sun ba da jawabi game da imaninsu a matsayin masu zuwa coci. Bayan sun kammala, an yi musu tambayoyi masu yawa, amma ɗaliban da suka ba da jawabin sun kasa kāre imaninsu. Sai malamar ta tambaye su, “Me ya sa kuka kasa kāre imaninku kamar yadda ’yar ajinku wadda Mashaidiyar Jehobah ce ta yi?”

Amsar ita ce: “Da gaske suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma mu ba ma yi.”

Malamar ta kalli Susana, kuma ta ce: “Hakika kina yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma kina iya ƙoƙarinki ki yi abin da ya ce. Kin cancanci a yaba maki.”

Susana za ta iya yin shiru. Amma, ta wajen yin magana, ta bi misali mai kyau na wata yarinya ƙarama ’yar Isra’ila wadda aka kai ta bauta a Suriya. Yarinyar tana zaune a gidan janar Naaman na Suriya, wanda ke da cutar kuturta. Ba’isra’iliyar ta ce wa uwargijiyarta: “Da ma ubangijina yana tare da annabin da ke a Samariya! da ya warkadda kuturtarsa.” Yarinyar ta ga cewa ya kamata ta yi shelar bisharar Allah na gaskiya. Hakan ya sa ubangijinta Naaman, ya zama mai bauta wa Jehobah.—2 Sar. 5:3, 17.

Hakazalika, Susana ba ta daina yin wa’azi game da Jehobah da mutanensa ba. Ta wajen yin magana don ta kāre imaninta, Susana tana yin biyayya ne ga umurnin da ke cikin Nassi: “Cikin zukatanku ku tsarkake Kristi kamar Ubangiji: kullum a shirye ku ke ku amsa ma kowane mai-tambayanku dalilin begen da ke cikinku, amma dai da ladabi da tsoro.” (1 Bit. 3:15) Kana shirye ka kāre bangaskiyarka a duk lokacin da ka za sami zarafi?

[Hoto a shafi na 17]

Waɗannan abubuwan za su taimake ka ka kāre imaninka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba