Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/1 pp. 15-17
  • Duk Yadda Muka Bauta Wa Allah Babu Damuwa Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Duk Yadda Muka Bauta Wa Allah Babu Damuwa Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misalai na Dā
  • Salon Gaurayayyar Bauta ta Isra’ilawa
  • Abin da Allah Ya Yi Domin Gauraya Bauta
  • Wane Darassi Za Mu Koya?
  • Yin Ibada ta Gaskiya Za Ta Sa Ka Daɗa Yin Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Yadda Ya Dace a Bauta wa Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Me Za Ka Yi don Allah Ya Amince da Bautarka?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Bauta da Allah Ya Amince da Ita
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/1 pp. 15-17

Duk Yadda Muka Bauta Wa Allah Babu Damuwa Ne?

“ADDINI sashen rayuwar mutane ne.” Haka Farfesa Alister Hardy ya ce a littafinsa The Spiritual Nature of Man (Yanayin Ruhaniya na Mutum). Sakamakon wani binciken da aka yi kwanan nan ya tabbatar da gaskiyar abin da ya ce. Ya gano cewa kashi 86 na dukan mutane da ke duniya sun yi imani da wani addini.

Binciken kuma ya nuna cewa mutanen suna bauta ne cikin manyan addini 19 kuma waɗanda suke da’awar su Kiristoci ne sun rabu har wajen gida 37,000. Wannan ba ya sa ka yi tunani ne ko Allah yana karɓan dukan waɗannan irin bauta dabam dabam? Hakika, duk yadda muka bauta wa Allah babu damuwa ne?

Game da wannan batu mai muhimmanci, ba zai yiwu a ce mun bi namu ra’ayi ba ko kuma yadda muke tunani. Daidai ne mu biɗi abin da Allah da kansa ya ce game da wannan batu. Saboda haka, bari mu ji abin da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ya ce. Me ya sa? Domin Yesu Kristi kansa ya ce cikin addu’a ga Allah: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Kuma manzo Bulus mai aminci ya tabbatar da haka: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa.”—2 Timothawus 3:16.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba dukan bauta ba ce Allah yake karɓa. Mun sami misalai cikin tarihi na ire-iren bauta da Allah ya karɓa da kuma waɗanda ya ƙi. Ta wajen bincika irin waɗannan misalan, za mu fahimci abin da wajibi ne mu yi da kuma waɗanda dole ne mu guje su domin bautarmu ta karɓu wurin Allah.

Misalai na Dā

Ta bakin annabi Musa, Jehobah Allah ya bai wa Isra’ilawa wasu dokoki da suka koya musu yadda za su bauta wa Allah yadda zai karɓa. Sa’ad da mutanen suka yi abin da waɗannan dokoki, waɗanda ake kira Dokar Musa, suka umurce su, Allah ya karɓe su kuma ya albarkace su. (Fitowa 19:5, 6) Duk da waɗannan tagomashi daga Allah, al’ummar Isra’ila ba ta riƙe irin addinin da Allah yake karɓa ba. Sau da yawa, sun juya wa Jehobah baya kuma suka bi ayyukan addini na mutanen ƙasashen da suke kusa da su.

A zamanin annabawa Ezekiel da Irmiya a ƙarni na bakwai K.Z., Isra’ilawa da yawa sun ƙi bin Dokar Allah kuma suka ƙulla abota da mutanen al’ummai na kusa da su. Ta wajen bin al’adun mutanen da kuma bukukuwansu, Isra’ilawa suna yin gaurayayyan addini. Isra’ilawa da yawa suna cewa: “Mu zama kamar sauran al’ummai, kamar kabilan ƙasashen duniya, mu bauta ma itace da.” (Ezekiel 20:32; Irmiya 2:28) Suna da’awar suna bauta wa Jehobah Allah, amma kuma suna girmama “gumaka,” har ma suna yin hadayar ’ya’yansu ga gumakan.—Ezekiel 23:37-39; Irmiya 19:3-5.

Masana tarihi ta wajen tonon ƙasa sun kira irin wannan salon addinin gauraya, wato, bauta wa alloli masu yawa a lokaci guda. Suna kiran irin wannan bauta ta jama’a, ko kuma addinin yawancin mutane. A yau, yawanci suna ganin cewa a wannan zamaninmu da mutane da suke da ra’ayi dabam dabam, ya kamata mu buɗe zuciyarmu ga dukan abu, har da addini. Saboda haka, suna jin cewa babu laifi a bauta wa Allah a dukan wata hanya da mutum ya ga dama. Amma hakan gaskiya ne? Batu ne kawai na ƙyale kowa ya yi addinin da ya ga dama? Ka yi la’akari da wasu ayyukan addinin jama’a da Isra’ilawa marasa aminci suke yi, kuma ka ga abin da waɗannan ayyukan suka kai ga.

Salon Gaurayayyar Bauta ta Isra’ilawa

Cibiyar gaurayayyar bauta ta Isra’ilawa ta haɗa da “masujadai,” ko kuma wuraren bauta a yankuna da suka ƙunshi bagadi, wuraren ƙona turare, dutse mai tsarki, da kuma alama ta katako ta abin bautar Kan’anawa Asherah, allahiyar haihuwa. Da irin waɗannan wuraren bauta da yawa a Yahuda. Sarakuna na biyu 23:5, 8 sun ambaci “masujadai na cikin biranen Yahuda, da cikin wurare na kewayen Urushalima; . . . tun daga Geba [kan iyaka ta arewa] har zuwa Beth-sheba [kan iyaka ta kudu].”

A waɗannan masujadai, Isra’ilawa suka “ƙona turare ga Baal, da rana, da wata, da manyan tamrari, da dukan rundunar sama.” Sun gina gidaje domin “sodomawa da ke cikin gidan Ubangiji” suna kuma ba da ’ya’yansu “su ratsa wuta zuwa Molech.”—2 Sarakuna 23:4-10.

Masana tarihi ta tonon ƙasa sun sami gumaka da yawa da aka yi da yumɓu a Urushalima da Yahuda, yawanci a gidajen mutane. Yawancinsu na mace ce tsirara mai manyan nono. Masana sun ce waɗannan gumaka na allahiya ce Ashtoreth da Asherah. Gumakan an yi imani cewa “gumaka ne domin taimako wajen ɗaukan ciki da kuma haihuwa.”

Yaya Isra’ila suka ɗauki irin waɗannan wurare domin gaurayayyar bauta? Farfesa Ephraim Stern na Jami’ar Hebrew ya lura cewa wataƙila yawancin irin waɗannan wuraren an “keɓe su ne domin Yahweh [Jehobah].” Rubutu da aka samu a inda ake tonon ƙasa ya tabbatar da wannan ra’ayi. Alal misali, wani ya ce, “Na albarkace ka da Yahweh na Samariya da kuma asherah tasa,” wani kuma ya ce, “Na albarkace ka da Yahweh na Teman da kuma asherah tasa!”

Waɗannan misalai sun nuna yadda Isra’ilawa suka yi ridda ta wajen gauraya bauta ta gaskiya ta Jehobah Allah da kuma abin kunya da arna suke yi. Sakamakon haka kuma shi ne lalata da kuma duhunta na ruhaniya. Yaya Allah ya ɗauki irin wannan bautar?

Abin da Allah Ya Yi Domin Gauraya Bauta

Allah ya furta fushinsa da la’anarsa bisa irin wannan bautar ta Isra’ilawa ta bakin annabi Ezekiel, yana cewa: “Dukan inda ku ke zaune za a maida birane kangaye, za a bar masujadansu kufai; domin a yi kufai da bagadanku, su zama kangaye, a parpashe gumakanku su ƙare, a sassare sifofinku na rana, ayukan da kuka yi a shafe su sarai.” (Ezekiel 6:6) Babu shakka cewa Jehobah bai yarda da irin wannan bauta ba ko kaɗan kuma ya ƙi ta.

Jehobah Allah ya sanar da yadda halakar za ta faru. “Ga shi, sai in aike . . . Nebuchadrezzar sarkin Babila, bawana, in kawo su su yi yaƙi da wannan ƙasa da mazaunanta, da dukan al’ummai na wajen nan; in halaka su sarai . . . Ƙasan nan duka kuwa za ta zama kango.” (Irmiya 25:9-11) Kamar yadda aka faɗa, a shekara ta 607 K.Z., Babiloniyawa suka kai wa Urushalima hari kuma suka halaka birnin da haikalinta gaba ɗaya.

Game da halakar Urushalima, Farfesa Stern, da aka yi ƙaulinsa daga baya, ya lura cewa abubuwan da suka rage “hakika sun jitu da abin da Littafi Mai Tsarki suka faɗa a (2 Sarakuna 25:8; 2 Labarbaru 36:18, 19) game da halaka, ƙonawa, da rushewar gidaje da garu.” Ya ci gaba da cewa: “Tabbaci daga tono na wannan ɓangare na tarihin Urushalima . . . za a iya ƙirga shi cikin waɗanda suke da ban mamaki.”

Wane Darassi Za Mu Koya?

Babban darassi shi ne cewa Allah bai yarda da bauta da ta so ta gauraya koyarwar Littafi Mai Tsarki da koyarwa, al’adu, da kuma bukukuwan wani addinai ba. Wannan shi ne darassi da manzo Bulus bai manta ba. An koyar da shi ya zama Bafarisa na Yahudawa. Sa’ad da a ƙarshe ya koyi kuma ya karɓi Yesu Almasihu, menene ya yi? “Abubuwan da su ke ribobi a gareni, waɗannan na lissafa su hasara sabili da Kristi,” in ji shi. Ya yi watsi da hanyoyinsa na dā kuma ya zama mabiyin Kristi mai ƙwazo.—Filibbiyawa 3:5-7.

Da yake mai wa’azi ne a ƙasashen waje, Bulus ya san ayyukan addini da kuma ra’ayin mutane da yawa. Duk da haka, ga Kiristoci a Korinthi, ya rubuta: “Wace zumunta ke tsakanin adalci da zunubi? ko kuwa wace tarayya haske ya ke da duhu? Ina gamin haikalin Allah da gumaka? . . . Domin wannan, Ku fito daga cikinsu, ku ware, in ji Ubangiji, Kada ku taɓa kowane abu mara-tsarki; Ni ma in karɓe ku.”—2 Korinthiyawa 6:14-17.

Da yake muna fahimci cewa yadda muke bauta wa Allah yana da muhimmanci a gare shi, mu tambayi kanmu: Wace irin bauta ce Allah ya yarda da ita? Ta yaya zan kusaci Allah? Kuma menene zan yi domin in bauta wa Allah a hanyar da ya yarda da ita?’

Shaidun Jehobah za su yi farin ciki su taimake ka ka sami amsar waɗannan tambayoyi da kuma wasu daga Littafi Mai Tsarki. Muna gayyatarka ka tuntuɓi Shaidun Jehobah a Majami’ar Mulkinsu ko kuma ka rubuta wa masu wallafa wannan jaridar ka nemi a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai a lokaci da kuma wurin da kake so.

[Hoto a shafi na 16]

Ɗakin bautar gumaka na dā, Tel Arad, Isra’ila

[Inda aka Dauko]

Garo Nalbandian

[Hoto a shafi na 16]

Siffar Ashtoreth daga gidan dā na Yahudiya

[Inda aka Dauko]

Photograph © Israel Museum, Jerusalem; courtesy of Israel Antiquities Authority

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba