Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 pp. 16-20
  • Aure Da Renon Yara A Wannan Zamanin Ƙarshe

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Aure Da Renon Yara A Wannan Zamanin Ƙarshe
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Aure Mai Daraja
  • Iyaye Masu Daraja
  • Ba Su Haifi ’Ya’ya ba Domin Kyakkyawar Manufa
  • “Wahala a Cikin Jiki”
  • “Sa’annan Za a Yi Ƙunci Mai-Girma”
  • Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Zaman Aure?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ka Kasance Da Farin Ciki A Aurenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 pp. 16-20

Aure Da Renon Yara A Wannan Zamanin Ƙarshe

“An gajertadda kwanaki.”—1 KOR. 7:29.

1. (a) Waɗanne canje-canje ne suke cikin “miyagun” abubuwa a yau? (b) Me ya sa canje-canje a ɗabi’ar iyali za su dame mu?

KALMAR Allah ta annabta cewa a “zamanin ƙarshe” za a yi yaƙe-yaƙe, girgizan ƙasa, yunwa, da kuma annoba. (Dan. 8:17, 19; Luk 21:10, 11) Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi cewa wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin ’yan adam zai kasance lokacin canji ne ƙwarai a dangantakar ’yan adam. Matsaloli a rayuwar iyali za su kasance cikin “miyagun” abubuwa da za su zo a wannan “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1-4) Me ya sa waɗannan canje-canje za su dame mu? Domin sun zama ruwan dare gama gari kuma za su iya rinjayar yadda Kiristoci suke ɗaukan aure da renon yara. Ta yaya?

2. Menene ra’ayin galibin mutane a duniya game da aure da kuma kisan aure?

2 A yau kisan aure ya zama da sauki da kuma gama gari, kuma yawan kisan aure yana ƙaruwa a ƙasashe masu yawa. Amma, ya kamata mu tuna cewa ra’ayin Jehobah Allah game da aure da kuma kisan aure ya bambanta ƙwarai da ra’ayin galibin mutane a duniya. To, menene ra’ayin Jehobah?

3. Menene ra’ayin Jehobah da Yesu Kristi game da aure?

3 Jehobah yana bukatar ma’aurata su kasance da aminci ga alkawarin da suka yi. Sa’ad da Jehobah ya ɗaura wa namiji da ta mace na fari aure, ya ce “namiji . . . zai manne ma matatasa; su zama nama ɗaya.” Daga baya Yesu Kristi ya maimaita wannan furcin kuma ya daɗa: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” Yesu kuma ya daɗa cewa: “Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi.” (Far. 2:24; Mat. 19:3-6, 9) Saboda haka, ga Jehobah da Yesu aure ya kamata ya kasance na tsawon rayuwa ne da zai ƙare sa’ad da ɗaya daga cikin ma’auratan ya rasu. (1 Kor. 7:39) Tun da aure tsari ne mai tsarki, kisan aure ba abin wasa ba ne. Hakika, Kalmar Allah ta ce Jehobah ya ƙi jinin kisan aure da ba shi da ka’ida bisa Nassi.a—Ka karanta Malachi 2:13-16; 3:6.

Aure Mai Daraja

4. Me ya sa wasu matasa Kiristoci sukan yi da na sani bayan sun yi saurin aure?

4 Duniyar da muke ciki marar tsoron Allah tana da jarabar jima’i. A koyaushe ana nuna hotuna masu tada sha’awa. Ba za mu rufa ido ga yadda waɗannan za su shafe mu ba, musamman ma matasanmu da muke ƙauna a ikilisiya. Me ya kamata matasa su yi game da irin wannan rinjaya marar kyau, wadda za ta iya tada musu sha’awa ba da son ransu ba? Waɗansu sun yi ƙoƙari su magance matsalar ta wajen yin aure sa’ad da suke ƙanana. Ta haka, suna begen cewa za su guji yin lalata. Amma, ba da daɗewa ba bayan haka waɗansu sun yi da na sani. Me ya sa? Da zarar an gama angonci, sai su fahimci cewa hankalinsu bai zo ɗaya ba a al’amuran yau da kullum. Domin haka, waɗannan ma’aurata sun fuskanci matsala mai tsanani.

5. Menene zai taimaki ma’aurata su kasance da aminci ga alkawarin aurensu? (Ka dubi hasiya.)

5 Auren wani ko ma Kirista ne wanda ya kasance ba yadda ki ka yi tsammani ba, hakika yana iya zama matsala. (1 Kor. 7:28) Duk da haka, komin wuyar matsalar, Kiristoci na gaske sun san cewa kashe auren da ba bisa Nassi ba, ba ita ba ce hanyar magance matsalolin aure da babu zaman lafiya ba. Saboda haka, waɗanda suka ci gaba da yin ƙoƙari don su tsare aurensu don suna son su kasance da aminci ga alkawarin aurensu sun cancanci a daraja su kuma a taimake su a ikilisiya ta Kirista.b

6. Yaya ya kamata matasa Kirista su ɗauki aure?

6 Kai matashi ne marar aure? Yaya ya kamata ka ɗauki aure? Za ka iya kauce wa matsaloli masu yawa idan ka jira har sai ka isa aure a zahiri, a tunaninka, da kuma a ruhaniya kafin ka fara soyayya da wata Kirista. Hakika, Nassosi ba su bada iya shekarun da mutum zai kai kafin ya yi aure ba.c Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya kamata ka jira har sai ka wuce lokacin da sha’awar jima’i take da ƙarfi sosai. (1 Kor. 7:36) Me ya sa? Domin sha’awar jima’i mai ƙarfi za ta iya sa ka ka yanke shawarar da bata dace ba kuma ta kai ga matsaloli daga baya. Ka tuna, shawarar Jehobah game da aure a cikin Littafi Mai Tsarki don amfaninka da farin cikinka ne.—Ka karanta Ishaya 48:17, 18.

Iyaye Masu Daraja

7. Menene wasu matasa da suka yi aure suke fuskanta, kuma me ya sa hakan zai iya kawo damuwa a aure?

7 Wasu ma’aurata sukan zama iyaye sa’ad suke ƙanana. Ba su sami zarafin fahimtar junansu sosai ba kafin su haifi yaron, wanda zai bukaci kulawa koyaushe. Sa’ad da matar ta suma mai da hankalinta ga jaririn, mai yiwuwa matashi mai-gidan sai ya soma kishi. Bugu da ƙari, sa’ad da iyayen suka kasa barci saboda jaririn, hakan zai iya kawo damuwa ga dangantakar ma’auratan. Matasa ma’aurata za su fahimci cewa ba su da ’yanci sosai kamar dā. Yanzu ba za su iya zuwa wurare ba kuma ba za su iya yin wasu abubuwa da suke yi ba a dā. Yaya ya kamata su ɗauki canjin yanayinsu?

8. Yaya ya kamata a ɗauki renon yara, kuma me ya sa?

8 Kamar yadda aka ɗauki aure da daraja, haka ma ya kamata a fahimci cewa renon yara hakki ne kuma gata ce daga Allah. Kowane irin gyare-gyare haihuwar jaririn za ta kawo a rayuwar ma’aurata Kiristoci, ya kamata su yi ƙoƙari su gyara rayuwarsu a hanya da ta dace. Tun da Jehobah ne ya ba wa ’yan adam ikon haihuwa, ya kamata iyaye su fahimci cewa jaririn “gādo ne daga wurin Ubangiji.” (Zab. 127:3) Uwa da uba Kiristoci za su yi ƙoƙari su cika hakkinsu na iyaye “cikin Ubangiji.”—Afis. 6:1.

9. (a) Menene reno yara ya ƙunsa? (b) Menene maigida zai yi don ya taimaki matarsa ta ƙarfafa a ruhaniya?

9 Renon yaro ya ƙunshi shekaru masu yawa na saɗaukar da kai. Yana bukatar lokaci da kuzari wajen iyaye. Maigida Kirista yana bukatar ya fahimci cewa shekaru da yawa bayan matarsa ta haihu, mai yiwuwa ne ba za ta iya mai da hankalinta wuri ɗaya a taro ba kuma ba za ta sami lokacin yin nazari da bimbini na kanta ba. Hakan zai iya raunana ruhaniyarta. Hakkin maigidan ne ya yi iya ƙoƙarinsa ya taimaka wajen kula da yaron. A gida zai yi ƙoƙari ya tattauna wasu abubuwa da aka faɗa a taro da matarsa ba ta samu ta saurara ba. Mai yiwuwa zai iya kula da yaron domin matarsa ta sami zarafin fita wa’azi.—Ka karanta Filibiyawa 2:3, 4.

10, 11. (a) Yaya ake renon yara a “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa”? (b) Me ya sa iyaye Kirista da yawa suka cancanci a yaba musu?

10 Renon yara ya ƙunshi fiye da yin tanadin abinci, sutura, wurin kwana, da kuma kula da lafiyar jiki. Musamman ma a wannan zamani na ƙarshe, matasa suna bukatar su koyi ɗabi’a da za su bi tun suna ƙanana. Ya kamata a reni yara a “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Wannan ‘gargaɗi’ ya ƙunshi saka tunanin Jehobah a zuciyar yara tun suna ƙanana har zuwa lokacin da suka zama matasa.—2 Tim. 3:14, 15.

11 Sa’ad da Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su “almajirtadda dukan al’ummai,” hakika yana nufin cewa iyaye su taimaki yaransu su zama almajirai. (Mat. 28:19, 20) Hakan na da wuya saboda irin matsi da wannan duniya take yi wa matasa. Saboda haka, iyaye da suka yi nasara a wurin renon ’ya’yansu har suka zama Kiristoci da suka keɓe kansu sun cancanci a yabe su a ikilisiya. Bangaskiya da amincin iyaye ya sa sun yi “nasara” bisa rinjaya ta duniya.—1 Yoh. 5:4.

Ba Su Haifi ’Ya’ya ba Domin Kyakkyawar Manufa

12. Me ya sa wasu Kiristoci suka tsai da shawara ba za su yi aure ba na wasu shekaru?

12 Tun da an “gajertadda kwanaki,” kuma tun da “ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa,” Kalmar Allah ta aririce mu mu yi la’akari da muhimmanci kasancewa marasa aure. (1 Kor. 7:29-31) Saboda haka, wasu Kiristoci sun zaɓi ba za su yi aure ba a rayuwarsu ko kuma su kasance ba su da aure na wasu shekaru. Ba su yi amfani da yancin da suka samu daga rashin aure su biɗi abin kansu ba. Mutane da yawa ba su yi aure ba don suna so su yi hidimar Jehobah “ba da raba hankali ba.” (Ka karanta 1 Korinthiyawa 7:32-35.) Wasu Kiristoci marasa aure suna hidima na majagaba ko kuma a Bethel. Wasu sun yi ƙoƙari su kyautata amfaninsu ga ƙungiyar Jehobah ta wajen cancanta su halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima. Hakika, waɗanda suka yi hidima na cikakken lokaci sa’ad ba su da aure kuma daga baya suka yi aure sau da yawa suna ganin aurensu yana amfana daga abubuwa da suka koya sa’ad da ba su yi aure ba.

13. Me ya sa wasu Kiristoci suka tsai da shawara ba za su haifi ’ya’ya ba?

13 A wasu wurare a duniya, wani canji ya auku a rayuwar iyali, wato, ma’aurata da yawa sun tsai da shawara ba za su haifi ’ya’ya ba. Wasu sun yi haka ne don rashin kuɗi; wasu kuma domin su nemi kuɗi. A tsakanin Kiristoci ma akwai ma’aurata da suka tsai da shawara ba za su haifi ’ya’ya ba. Amma, sun yi haka ne don su bauta wa Jehobah. Hakan ba ya nufin cewa waɗannan ma’aurata ba sa jin daɗin aure yadda ya kamata ba. Suna jin daɗi. Duk da haka, sun sa hidimar Mulki a gaba fiye da wasu gatar da aure yake bayarwa. (1 Kor. 7:3-5) Wasu cikin waɗannan ma’aurata suna bauta wa Jehobah ta wajen yi wa ’yan’uwansu hidima a da’ira, gunduma ko kuma a Bethel. Wasu kuma suna yin hidima na majagaba ko kuma wa’azi a ƙasashen waje. Jehobah ba zai manta da aikinsu da kuma ƙauna da suka nuna masa ba. —Ibran. 6:10.

“Wahala a Cikin Jiki”

14, 15. (a) Wane “wahala a cikin jiki” ne iyaye Kiristoci za su fuskanta?

14 Manzo Bulus ya ga ya wa ma’aurata Kiristoci cewa za su sha “wahala a cikin jiki.” (1 Kor. 7:28) Hakan ya ƙunshi rashin lafiyar ma’aurata, yaransu, ko kuma iyayensu tsofaffi. Ya kuma ƙunshi wahalar renon yara. Kamar yadda aka ambata a farkon wannan talifi, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa “kwanaki na ƙarshe” zai jawo “miyagun” abubuwa. Miyagun abubuwa za su ƙunshi yara “marasa-bin iyaye.”—2 Tim. 3:1-3.

15 Renon yara matsala ce sosai ga iyaye Kiristoci. “Miyagun zamanu” za su iya shafansu. Saboda haka, iyaye Kiristoci dole su yaƙi muguwar rinjayar da “zamanin wannan duniya” zai yi a kan ’ya’yansu. (Afis. 2:2, 3) Kuma ba koyaushe ake yin nasara a yaƙin ba. Idan ɗa ko ’ya daga iyalin Kirista ta ko ya bar bautawa Jehobah, hakika wannan “wahala” ce ga iyayen da suka yi ƙoƙari su yi renon sa ko ta a cikin gaskiyar Allah.—Mis. 17:25.

“Sa’annan Za a Yi Ƙunci Mai-Girma”

16. Wace ‘wahala’ ce Yesu ya annabta?

16 Duk wata ‘wahalar’ aure da kuma renon yara ba za ta kai na ƙunci mai girma tsanani ba. A annabcinsa game da bayyanuwarsa da kuma ƙarshen zamani Yesu ya ce: “Za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.” (Mat. 24:3, 21) Daga baya Yesu ya nuna cewa taro mai girma za su tsira daga wannan “ƙunci mai-girma.” Amma kuma, duniyar Shaidan za ta ci gaba da yaƙan Shaidun Jehobah masu salama. Babu shakka zai kasance lokaci ne mai wuya a gare mu yara da manya.

17. (a) Me ya sa ya kamata mu fuskanci abin da ke zuwa a nan gaba da gaba gaɗi? (b) Menene ya kamata ya shafi tunaninmu game da aure da kuma renon yara?

17 Duk da haka, kada mu ji tsoron abin da zai faru a nan gaba. Iyaye masu aminci su kasance da bege cewa Jehobah zai ƙare su tare da ’ya’yansu. (Ka karanta Ishaya 26:20, 21; Zeph. 2:2, 3; 1 Kor. 7:14) A yanzu, bari fahiminmu game da miyagun zamani ya shafi tunaninmu game da aure da kuma renon yara a wannan zamani na ƙarshe. (2 Bit. 3:10-13) A haka, rayuwarmu ko mun yi aure ko ba mu yi ba, ko muna da ’ya’ya ko ba mu da su, za ta yabi Jehobah da kuma ikilisiya ta Kirista.

[Hasiya]

a Ga dubi littafin nan Live With Jehovah’s Day in Mind ƙarƙashin kan magana nan “He Has Hated a Divorcing,” a shafi na 125.

b Waɗanda suke fama da matsalar aure za su sami ƙarfafa idan suka yi nazarin waɗannan talifofi game da aure da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Satumba, 2003 na Turanci, da Awake! na 8 ga Janairu, 2001 na Turanci.

c Ka dubi babi na 30, mai jigo “Am I Ready for Marriage?” a cikin littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work.

Domin Maimaitawa

• Me ya sa bai kamata Kiristoci matasa su yi saurin aure ba?

• Menene renon yaro ya ƙunsa?

• Me ya sa Kiristoci da yawa suka tsai da shawara cewa ba za su yi aure ba, kuma idan suka yi aure ba za su haifi ’ya’ya ba?

• Wace “wahala” ce Kiristoci za su iya fuskanta?

[Hoto a shafi na 17]

Me ya sa yana da kyau matasa Kiristoci su jira kafin su yi aure?

[Hoto a shafi na 18]

Maigida zai iya yin abubuwa da yawa ya taimaki matarsa domin ta saka hannu cikin ayyuka na ruhaniya

[Hoto a shafi na 19]

Me ya sa wasu ma’aurata Kiristoci suka tsai da shawara ba za su haifi ’ya’ya ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba