Alkawari Mai Muhimmanci Sosai
AKWAI alkawari mai muhimmanci da na ɗauka. Bari in bayyana maku dalilin da ya sa ni uwa matashiya ’yar Sfanisanci na ɗauki wannan alkawarin.
Babu kwanciyar hankali a gidan iyaye na. Iyalinmu ta yi baƙin ciki sosai sa’ad da ƙanina ya mutu a wani mugun haɗarin mota sa’ad da yake ɗan shekara huɗu. Bugu da ƙari, mugun halin da ubana yake da shi ya hana mamata samun farin ciki a aurensu. Wannan wahalar bai hana ta koya wa ni da yayana halaye masu kyau ba.
Bayan wani lokaci, yayana ya yi aure, sai ni ma na yi. Ba da daɗewa ba, an gwada mahaifiyata a asibiti kuma aka ce tana da cutar kansa wanda shi ne ya yi sanadin mutuwarta. Amma kafin ta mutu, ta ba mu wata dukiya.
Wata ƙawarta ta gaya mata begen da ke cikin Nassosi game da tashin matattu, kuma mamata ta yarda ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Sa’ad da take gab da mutuwa, saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya sa ta kasance da bege kuma hakan ya taimaka mata ta sami farin ciki.
Sa’ad da muka ga yadda saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya shafe ta sosai, sai ni da yayana muka soma nazarin Kalmar Allah. Na yi baftisma a matsayin ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah wata ɗaya kafin in haifi jaririyata ta biyu, yarinya mai kyau wadda muka sa wa suna Lucía.
Ranar baftismata rana ce mai muhimmanci a gare ni. Dalili na farko shi ne, yanzu na zama na Jehobah domin na keɓe masa kaina don na bauta masa har abada. Dalili na biyu shi ne, zan iya koya wa ɗana da ɗiyata da nike ƙauna bangaskiyata.
Wannan dalili na biyu da ke sa ni farin ciki ya sami cikas. Sa’ad da Lucía ta kai ’yar shekaru huɗu, ta soma samun ciwon ciki mai tsanani. Bayan an yi gwaje-gwaje masu yawa, likitan da ke yin gwajin ya gaya mana cewa akwai wani ɗan curi wanda ya kai girman lemun zaƙi da ke manne a jikin hantarta. Likitan ya bayyana cewa Lucía tana da wata irin muguwar cutar kansa wadda take saurin girma. Wannan shi ne mafarin neman maganin cutar kansa da aka yi ta yi wa Lucía har na tsawon shekaru bakwai, wanda ya haɗa da kwanciya a asibiti na kwanaki masu yawa.
Halin Sadaukar da Kai
A waɗannan shekaru masu wuya, Lucía ta kan ƙarfafa ni ta wajen rungume ni da kuma yi mini sumba. Yadda ta yi fama da wannan cutar ya burge ma’aikatan asibitin. A kowane lokaci tana son ta yi aiki da malaman asibitin, tana taimaka musu wajen rarraba kindirmo, ruwan ’ya’yan itace, da sauran abubuwa ga yaran da aka kwantar a ɗakunan asibiti da ke kusa da nata. Sai da ma malaman asibitin suka ba Lucía kayan ma’aikacin asibiti da kuma bajon da aka rubuta “mai taimaka wa malaman asibiti.”
“Lucía ta taɓa zuciyata,” in ji wata malamar asibiti. “Yarinya ce mai ƙwazo kuma tana son yin zane. Ta san yadda ake yin magana sosai kuma tana yin abubuwa kamar wadda ta yi girma sosai.”
Lucía ta sami ƙarfafa da kuma kwanciyar hankali daga Kalmar Allah. (Ibran. 4:12) Ta gaskata cewa a sabuwar duniya, kamar yadda Kalmar Allah ta yi alkawari, “mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba” ba. (R. Yoh. 21:4) Domin tana son mutane, ta yi amfani da kowace dama ta gaya musu saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Begen da Lucía take da shi na tashin matattu ne ya taimaka mata ta kasance da kwanciyar hankali kuma ta ci gaba da yin fara’a duk da cewa ta san ciwon na ajali ne. (Isha. 25:8) Ta ci gaba da nuna wannan halin har ranar da cutar kansar ta kashe ta.
A wannan ranar ce na ɗauki wannan alkawari mai muhimmanci. Da kyar Lucía take buɗe idanunta. Babanta ya riƙe hannunta ɗaya ni ma na riƙe ɗayan hannun. Sai na raɗa mata cewa, “kada ki damu, ba zan ƙyale ki ba. Ki yi numfashi a hankali. Sa’ad da ki ka tashi, za ki warke. Ba za ki ƙara shan wahala ba, kuma zan kasance tare da ke.”
Dole ne in cika wannan alkawarin. Na san cewa jiran tashinta daga matattu ba zai kasance da sauƙi ba. Amma na san cewa idan na ci gaba da dogara ga Jehobah kuma na kasance da aminci, zan kasance a wurin sa’ad da aka ta da ta daga matattu.
Abin da Lucía Ta Bar Mana
Gaba gaɗin da Lucía ta nuna da kuma yadda ikilisiya ta taimaka mana ya shafi mijina sosai, wanda ba Mashaidi ba ne. A ranar da Lucía ta mutu, ya gaya mini cewa zai sake bincika al’amuransa sosai. Bayan wasu ’yan makonni, ya gaya wa wani dattijon ikilisiya cewa ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ba da daɗewa ba, mijina ya soma halartar dukan taro. Da taimakon Jehobah, ya daina shan taba abin da ya kasa yi a dā.
Har yanzu na kan yi baƙin ciki saboda mutuwar Lucía, duk da haka ina godiya sosai ga Jehobah saboda abin da Lucía ta bar mana. Ni da mijina muna ƙarfafa juna da begen tashin matattu, a wasu lokatai mukan yi tunanin lokacin da za mu sake ganin Lucía, da idanunta dara-dara da kuma kumatunta da ke shigewa ciki sa’ad da ta yi murmushi.
Wannan mugun abu da ya sami ɗiyata ya shafi wata matar da muke zaune tare a unguwa ɗaya. A wata ranar Asabar da safe ana ruwan sama, wata mata wadda ɗanta ke makaranta ɗaya da Lucía ta zo gidanmu. Cutar kansa ta sake kashe wani ɗanta wanda ke ɗan shekara sha ɗaya a lokacin. Sa’ad da ta sami labarin abin da ya sami Lucía, matar ta nemi gidanmu kuma ta ziyarce mu. Tana son ta san yadda nike jimrewa da mutuwar Lucía kuma ta kawo shawarar cewa mu kafa rukuni na taimakon juna don ƙarfafa sauran matan da ke fuskantar irin wannan yanayin.
Na bayyana mata cewa na sami ƙarfafa ta gaske daga ɗaya cikin alkawuran Littafi Mai Tsarki, wanda ya ɗara duk wani irin ƙarfafawar da mutane za su bayar. Fuskarta ta cika da bege sa’ad da nike karanta mata kalaman Yesu da ke Yohanna 5:28, 29. Ta yarda na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma ba da daɗewa ba ta soma samun “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa.” (Filib. 4:7) A yawancin lokaci idan muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare, mu kan ɗan dakata mu yi tunanin cewa ga mu a cikin sabuwar duniya, muna marabtar ƙaunatattunmu da aka ta da daga matattu.
Hakika, ɗan rayuwar da Lucía ta yi ya bar abin da ba za a taɓa mancewa da shi ba. Bangaskiyarta ta taimaka wajen haɗa kan iyalinmu a bautar Allah, kuma ta sa na ƙara ƙudurta cewa zan riƙe bangaskiyata sosai. Babu shakka, mu duka da muka rasa waɗanda muke ƙauna waɗanda wataƙila za a ta da su daga matattu, muna da alkawari mai muhimmanci da za mu cika.
[Hoto a shafi na 20]
Aljannar da Lucía ta zana