Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 3/15 pp. 12-16
  • Jehobah Yana Jin Kukanmu Na Neman Taimako

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Jin Kukanmu Na Neman Taimako
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ya San Matsalolinmu
  • Ka Dogara ga Taimakon Jehobah
  • Yadda Za Mu Iya Samun Ƙarfin Jimrewa
  • Ceto Daga Dukan Wahalolinmu
  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Jehovah ‘Mai Kiyaye Mu A Lokatan Wahala’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Cikakkiyar Dogara Ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za Ka Sami Salama Kuma Ka Yi Farin Ciki In Kana Cikin Damuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 3/15 pp. 12-16

Jehobah Yana Jin Kukanmu Na Neman Taimako

“Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.”—ZAB. 34:15.

1, 2. (a) Yaya yawancin mutane suke ji a yau? (b) Me ya sa hakan bai ba mu mamaki ba?

KANA baƙin ciki ne sosai? Idan haka ne, to ka san cewa ba kai kaɗai ba ne ba kawai kake fuskantar irin wannan yanayin. Miliyoyin mutane a yau suna fama da matsi na yau da kullum na yin rayuwa a wannan muguwar duniyar. Wasu suna ganin cewa su ba za su iya jimrewa ba. Suna ji kamar mai zabura Dauda wanda ya rubuta: “Na yi suwu, na ƙuƙuje ƙwarai: Na yi ruri domin rashin kwanciyar zuciyata. Zuciyata tana haki, ƙarfina ya rabu da ni: Hasken idanuna kuma, ya fice mani.”—Zab. 38:8, 10.

2 Mu Kiristoci, ba ma mamakin ganin wahalolin da ake sha a rayuwa. Mun fahimci cewa “mafarin wahala” yana cikin alamar bayyanuwar Yesu da aka annabta. (Mar. 13:8; Mat. 24:3) Kalmar yare na ainihi da aka fassara “mafarin wahala” tana nufin wahalar da ake sha a lokacin haihuwa. Wannan kwatancin ya dace da tsananin wahalar da mutane suke sha a wannan zamanin na ‘shan wuya.’—2 Tim. 3:1; Littafi Mai Tsarki.

Jehobah Ya San Matsalolinmu

3. Menene mutanen Allah suka sani?

3 Mutanen Jehobah sun san cewa za su fuskanci wahalolin duniyar nan, kuma daga dukan alamu, wahaloli za su ci gaba da ƙaruwa ne. Ƙari ga abubuwan da dukan mutane suke fuskanta, mu bayin Allah muna fuskantar ‘magabci Shaiɗan,’ wanda ya ƙudurta cewa zai halaka bangaskiyarmu. (1 Bit. 5:8) Hakan na iya sa mu ji kamar yadda Dauda ya ji: “Zargi ya karye zuciyata; cike ni ke da jin nauyi: Na biɗi waɗanda za su ji tausai; amma babu kowa; Masu-ta’aziya kuwa, amma ban samu ba.”—Zab. 69:20.

4. Menene ke ƙarfafa mu sa’ad da muke shan wahala?

4 Dauda yana nufin cewa ba shi da bege ne sam? A’a. Yi la’akari da waɗannan ƙarin kalaman da ya yi a wannan zabura: “Gama Ubangiji yana jin kukar masu-ƙunci, Ba ya kuwa rena ɗaurarrunsa ba,” wato, ba ya yin watsi da mutanensa da aka ɗaure. (Zab. 69:33) Gabaki ɗaya, a wasu lokatai muna iya jin cewa matsaloli ko wahalolin da muke sha sun ɗaure mu. Muna iya ganin cewa mutane ba su fahimci yanayinmu ba, kuma wataƙila ba su fahimta ba da gaske. Amma kamar Dauda, muna iya samun ƙarfafa ta wajen sanin cewa Jehobah yana sane da wahalolin da muke sha sosai.—Zab. 34:15.

5. Wane tabbaci ne Sarki Sulemanu yake da shi?

5 Ɗan Dauda, Sulemanu ya bayyana wannan gaskiyar a lokacin da yake keɓe haikali a Urushalima. (Ka karanta 2 Labarbaru 6:29-31, Littafi Mai Tsarki.) Ya roƙi Jehobah ya ji addu’ar duk wani mai zuciyar kirki da ya yi masa addu’a game da “irin wahalarsa, da baƙin cikinsa.” Menene Allah zai yi game da addu’o’in waɗannan masu baƙin ciki? Sulemanu ya bayyana tabbacinsa cewa Allah zai ji addu’o’insu kuma zai ɗauki mataki a kai. Me ya sa? Domin ya san ainihin abin da ke “zukatan mutane.”

6. Ta yaya ne za mu iya jimre wa alhini, kuma me ya sa?

6 Mu ma muna iya yin addu’a ga Jehobah game da ‘wahalarmu da baƙin cikinmu.’ Ya kamata mu ƙarfafa domin mun san cewa Jehobah ya fahimci wahalolin da muke sha kuma ya damu da mu. Manzo Bitrus ya tabbatar da hakan sa’ad da ya ce: ‘Ku zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.’ (1 Bit. 5:7) Jehobah yana damuwa da abin da ya same mu. Yesu ya nanata ƙaunar Jehobah sa’ad da ya ce: “Ba a kan sayarda gwarare biyu a bakin penny guda ba? ko ɗaya a cikinsu kuwa ba shi fāɗuwa a ƙasa ba sai da sanin Ubanku: amma har da gasussuwan kanku dukansu an ƙididdige su. Kada ku ji tsoro fa; kun fi gwarare masu-yawa daraja.”—Mat. 10:29-31.

Ka Dogara ga Taimakon Jehobah

7. Wane taimako ne za mu iya samu?

7 Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai iya taimaka mana a lokacin wahala. “Allah mafakanmu ne da ƙarfinmu, taimako ne na kurkusa cikin wahala.” (Zab. 34:15-18; 46:1) Ta yaya ne Allah yake yin tanadin wannan taimakon? Yi la’akari da abin da 1 Korinthiyawa 10:13 ta ce: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” Jehobah yana iya daidaita batutuwa don ya kawar da wahalarmu, ko kuwa yana iya ba mu ƙarfin da muke bukata don mu jimre. Ko ta yaya, Jehobah zai taimaka mana.

8. Ta yaya za mu iya samun taimakon Allah?

8 Ta yaya za mu iya samun wannan taimakon? Yi la’akari da shawarar da aka ba mu: ‘Ku zuba dukan alhininku a bisansa.’ Hakan na nufin cewa za mu miƙa wa Jehobah dukan damuwarmu a alamance. Za mu ƙoƙarta mu daina damuwa kuma mu dogara gare shi cewa zai biya bukatunmu. (Mat. 6:25-32) Irin wannan dogarar tana bukatar tawali’u, ba wai za mu dogara ga ƙarfinmu ko hikima ba. Idan muka ƙasƙantar da kanmu “a ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah,” hakan zai nuna cewa mun fahimci matsayinmu. (Ka karanta 1 Bitrus 5:6.) Kuma hakan zai taimaka mana mu jimre da duk wani abin da Allah ya ƙyale. Muna iya neman sauƙi na nan da nan, amma mun tabbata cewa Jehobah ya san ainihin lokacin da zai ɗauki mataki da kuma abin da zai yi domin mu.—Zab. 54:7; Isha. 41:10.

9. Wace irin nawaya ce Dauda yake bukatar ya zuba a kan Jehobah?

9 Ka tuna kalaman da Dauda ya rubuta a Zabura 55:22: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka: Ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.” Dauda ya rubuta waɗannan kalaman ne a lokacin da yake cike da baƙin ciki. (Zab. 55:4) Mun fahimci cewa an rubuta wannan zaburar ce a lokacin da ɗansa Absalom yake ƙulla maƙarƙashiya don ya ture shi daga kan sarauta. Ahitofel, wanda shi ne amintaccen mashawarcin Dauda, yana cikin waɗanda suka ci amanar Dauda. Hakan ya sa Dauda ya gudu daga Urushalima don kada a kashe shi. (2 Sam. 15:12-14) Har ma a waɗannan lokaci na wahala, Dauda ya dogara ga Allah, kuma Jehobah bai yashe shi ba.

10. Menene muke bukatar mu yi sa’ad da muke shan wahala?

10 Kamar Dauda, yana da muhimmanci mu yi addu’a ga Jehobah game da duk wata irin wahalar da muke sha. Bari mu duba abin da manzo Bulus ya ce mu yi game da wannan. (Ka karanta Filibiyawa 4:6, 7.) Menene zai kasance sakamakon irin wannan addu’ar? “Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatan[mu] da tunanin[mu] cikin Kristi Yesu.”

11. Ta yaya ne ‘salamar Allah’ take kāre zuciyarmu da kuma tunaninmu?

11 Addu’a za ta iya canja yanayin ka kuwa? Wataƙila. Amma muna bukatar mu san cewa Jehobah ba ya yawan amsa addu’o’i kamar yadda muke so. Duk da haka, addu’a tana taimaka mana mu yi tunanin kirki don kada wahalarmu ta sha kanmu. ‘Salamar Allah’ tana iya kwantar mana da hankali sa’ad da wahala ta nemi ta sha kanmu. Kamar rukunin sojojin da aka ce su je su kāre wani birni daga abokan gaba, ‘salamar Allah’ za ta kāre zuciyarmu da kuma tunaninmu. Za ta kuma sa mu kawar da shakkar da muke yi, tsoron da muke ji, da kuma tunani marar kyau kuma za ta hana mu ɗaukan mataki ba tare da mun yi tunani sosai ba.—Zab. 145:18.

12. Ka kwatanta yadda mutum zai iya samun kwanciyar hankali.

12 Ta yaya ne za mu iya samun kwanciyar hankali a lokacin wahala? Yi la’akari da wani misali da ya ɗan yi kama da yanayinmu. Wataƙila wani ma’aikaci yana aiki a ƙarƙashin manajan da ke yawan zagin mutane. Wannan ma’aikacin ya sami damar gaya wa mai kamfanin wanda mutumin kirki ne kuma mai sanin ya kamata yadda yake ji. Mai kamfanin ya tabbatar wa ma’aikacin cewa ya san abin da ke faruwa kuma ya gaya masa cewa nan ba da daɗewa ba za a cire manajan daga matsayinsa. Yaya wannan ma’aikacin zai ji? Domin ya gaskata da abin da aka gaya masa da kuma abin da ke gab da faruwa, hakan zai ƙarfafa shi ya ci gaba da yin aikinsa, ko da zai fuskanci ƙarin matsaloli na ɗan lokaci. Hakazalika, mun san cewa Jehobah ya san yanayinmu, kuma ya ba mu tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba “za a fitarda mai-mulkin wannan duniya.” (Yoh. 12:31) Hakan yana da ban ƙarfafa!

13. Ƙari ga yin addu’a, menene kuma muke bukatar mu yi?

13 Gaya wa Jehobah matsalolinmu a addu’a ne kawai muke bukata? A’a. Akwai wasu abubuwan da muke bukatar mu yi. Muna bukatar mu ɗauki matakin da ya jitu da addu’o’inmu. Sa’ad da Sarki Saul ya aika mutane su je gidan Dauda don su kashe shi, Dauda ya yi addu’a: “Ka cece ni daga hannun maƙiyana, ya Allahna: Ka cira ni nesa da waɗanda ke tasa mani. Ka fishe ni daga hannun masu-aika mugunta, Ka cece ni daga hannun masu-ƙishin jini.” (Zab. 59:1, 2) Ƙari ga addu’ar da ya yi, Dauda ya saurari abin da matarsa ta ce kuma ya ɗauki matakan da suka dace don ya tsira. (1 Sam. 19:11, 12) Hakazalika, muna iya yin addu’ar samun hikimar da za ta taimaka mana mu magance ko kuma mu kyautata yanayin mu na wahala.—Yaƙ. 1:5.

Yadda Za Mu Iya Samun Ƙarfin Jimrewa

14. Menene zai taimaka mana mu jimre sa’ad da muke shan wahala?

14 Wataƙila wahalolinmu ba za su ƙare nan da nan ba. Suna ma iya ci gaba har na wani ɗan lokaci. Idan haka ne, menene zai taimaka mana mu jimre? Na farko, ka tuna cewa idan muka ci gaba da bauta wa Jehobah cikin aminci duk da wahalolin da muke sha, hakan zai nuna cewa muna ƙaunarsa. (A. M. 14:22) Ka tuna zargin da Shaiɗan ya yi game da Ayuba: “A banza ne Ayuba ya ke tsoron Allah? Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowane sassa? Ka albarkaci aikin hannuwansa, dabbobinsa sun ƙaru a ƙasa. Miƙa hannunka kaɗai yanzu, ka taɓa dukan abin da yake da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!” (Ayu. 1:9-11) Domin amincinsa, Ayuba ya nuna cewa wannan zargin ƙarya ne. Idan muka jimre a lokacin da muke shan wahala, mu ma za mu sami damar ƙaryata Shaiɗan. Da haka, jimrewarmu za ta ƙarfafa begenmu da kuma tabbacinmu.—Yaƙ. 1:4.

15. Waɗanne misalai ne za su iya ƙarfafa mu?

15 Na biyu, ka tuna cewa “’yan’uwanku da ke cikin duniya suna shan waɗannan azabai da ku ke sha.” (1 Bit. 5:9) Hakika, “babu wata jaraba ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa.” (1 Kor. 10:13) Saboda haka, kana iya samun ƙarfi da gaba gaɗi ta wajen yin bimbini a kan misalan wasu maimakon ka mai da hankali ga matsalolinka. (1 Tas. 1:5-7; Ibran. 12:1) Ka yi tunani sosai a kan misalin waɗanda ka sani da suka jimre cikin aminci duk da muguwar wahalar da suka sha. Ka taɓa neman labaran da aka wallafa don ka sami labaran waɗanda suka taɓa fuskantar irin matsalar da kake fuskanta? Waɗannan labaran za su ƙarfafa ka sosai.

16. Ta yaya ne Allah yake ƙarfafa mu sa’ad da muka fuskanci ƙunci dabam dabam?

16 Na uku, ka tuna cewa Jehobah shi ne “Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu, har da za mu iya ta’azantarda waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci, ta wurin ta’aziyya wadda mu da kanmu muka ta’azantu da ita daga wurin Allah.” (2 Kor. 1:3, 4) Kamar dai Allah yana tsaye ne a kusa da mu don ya ƙarfafa mu kuma ya ba mu ƙarfi, ba wai kawai a matsalolinmu na yanzu ba amma ‘a cikin dukan ƙuncinmu.’ Hakan na sa mu ƙarfafa waɗanda suke ‘cikin kowane irin ƙunci.’ Bulus ya shaida gaskiyar waɗannan kalaman.—2 Kor. 4:8, 9; 11:23-27.

17. Ta yaya ne Littafi Mai Tsarki yake taimaka mana mu bi da matsaloli na rayuwa?

17 Na huɗu, muna da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, wanda “mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Tim. 3:16, 17) Ba wai Kalmar Allah tana mai da mu ‘shiryayyu domin kowane nagarin aiki’ ba ne ba kawai. Amma tana sa mu magance matsaloli na rayuwa. Tana sa mu zama ‘shiryayye sarai.’ Kalma ta ainihi da aka fassara “shiryayye sarai” tana nufin “lafiyayye.” Wataƙila an yi amfani da wannan kalmar ce a zamanin dā don lafiyayyen kwalekwalen da ke da duk wani abin da ake bukata don ya yi tafiya a teku ko kuwa na’urar da za ta iya yin duk abin da ake son ta yi. Hakazalika, ta hanyar Kalmarsa, Jehobah yana yi mana tanadin dukan abubuwan da muke bukata don mu magance duk wani abin da za mu fuskanta. Shi ya sa za mu iya cewa: “Idan Allah ya ƙyale wani abu, zan iya jimrewa da taimakonsa.”

Ceto Daga Dukan Wahalolinmu

18. Mai da hankali a kan menene zai taimake mu mu jimre da aminci?

18 Na biyar shi ne, ka ci gaba da tuna cewa nan ba daɗewa ba Jehobah zai kawar da dukan wahalolin mutane. (Zab. 34:19; 37:9-11; 2 Bit. 2:9) Idan hakan ya faru, Allah zai cece mu daga wahalolin da muke sha a yanzu kuma za mu sami damar samun rai na har abada, wataƙila a sama tare da Yesu ko kuwa a aljanna ta duniya.

19. Ta yaya ne za a iya jimrewa cikin aminci?

19 Har sai wannan lokacin ya zo, za mu ci gaba da bi da wahalolin da muke fuskanta a wannan muguwar duniya. Muna ɗokin ganin lokacin da wahala za ta ƙare! (Zab. 55:6-8) Bari mu tuna cewa idan muka jimre cikin aminci za mu mai da Iblis maƙaryaci. Bari mu ci gaba da samun ƙarfi daga addu’o’inmu da ta ’yan’uwanmu Kiristoci, kuma mu dinga tuna cewa ’yan’uwanmu suna fuskantar jarrabawa kamar mu. Ka ci gaba da kasancewa shiryayye sarai da ayyuka nagari ta wajen yin amfani da Kalmar Allah sosai. Kada ka yarda tabbacin da kake da shi a tanadin da “Allah na dukan ta’aziyya” yake yi ta yi ta kaɗawa. Ka tuna cewa “idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.”—Zab. 34:15.

Za ka Iya Amsawa?

• Yaya ne Dauda ya ji game da wahalar da ya sha?

• Wane tabbaci ne Sarki Sulemanu ya nuna?

• Menene zai iya taimaka mana mu jimre da abin da Jehobah ya ƙyale?

[Hoto a shafi na 13]

Sulemanu yana da tabbaci cewa Jehobah zai ɗauki mataki domin mutanensa da ke wahala

[Hoto a shafi na 15]

Dauda ya tura nawayarsa ga Jehobah a addu’a kuma ya yi abubuwan da suka jitu da addu’arsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba