Yesu Kristi, Mai Wa’azi Mafi Girma Na Ƙasashen Waje
“Daga wurinsa ni ke, shi kuwa ya aiko ni.”—YOH. 7:29.
1, 2. Wanene Mai wa’azi mafi girma na ƙasashen waje?
MENENE zai zo zuciyarka idan ka ji kalaman nan “masu wa’azi a ƙasashen waje”? Wasu za su yi tunanin cewa masu wa’azi ne da Kiristendom suka tura ƙasashen waje, waɗanda yawancinsu suke saka hannu a siyasa da kuma al’amuran da suka shafi tattalin arzikin ƙasashen da suke hidima. A matsayinka na Mashaidin Jehobah, za ka yi tunanin masu wa’azi a ƙasashen waje da Hukumar Mulki ta tura su je su yi wa’azin bishara a ƙasashe dabam dabam na duniya. (Mat. 24:14) Waɗannan masu wa’azi a ƙasashen waje suna ba da lokacinsu da kuma ƙarfinsu babu son kai ga aikin taimaka wa mutane don su kusanci Jehobah Allah kuma su more dangantaka mai kyau da shi.—Yaƙ. 4:8.
2 Kalaman nan “mai wa’azi a ƙasashen waje” da kuma “masu wa’azi a ƙasashen waje” ba sa cikin Litafi Mai-Tsarki. Amma kalmar Helenanci da aka fassara “masu-wa’azin bishara” a Afisawa 4:11, za a iya kiranta “masu wa’azi a ƙasashen waje.” Jehobah shi ne Mai Bishara mafi girma, amma ba za a iya kiransa Mai wa’azi mafi girma a ƙasashen waje ba, domin babu wanda ya aike shi yin wa’azi. Game da Ubansa na samaniya, Yesu Kristi ya ce: “Ni na san shi; gama daga wurinsa ni ke, shi kuwa ya aiko ni.” (Yoh. 7:29) Domin ya nuna ƙaunarsa ga mutane, Jehobah ya aiko Ɗansa makaɗaici zuwa duniya. (Yoh. 3:16) Za a iya kiran Yesu Mai wa’azi mafi girma a ƙasashen waje wanda ya fi ƙwarewa, domin dalili guda da ya sa aka turo shi duniya shi ne ya “bada shaida ga gaskiya.” (Yoh. 18:37) Ya yi nasara sosai a bisharar Mulkin da ya yi, kuma har yanzu muna amfana daga hidimar da ya yi. Alal misali, muna iya yin amfani da hanyoyin koyarwarsa a hidimarmu, ko da mu masu yin wa’azi ne a ƙasashen waje ko a’a.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
3 Abin da Yesu ya yi a matsayin mai wa’azin Mulki ya ta da tambayoyi kamar haka: Menene Yesu ya fuskanta a duniya? Me ya sa koyarwarsa take da amfani? Kuma me ya sa ya yi nasara a hidimarsa?
Yesu Ya Nuna Son Rai Sa’ad da Yake Wa’azi
4-6. Waɗanne canje-canje ne Yesu ya yi sa’ad da aka turo shi duniya?
4 Masu wa’azi a ƙasashen waje na zamani da kuma wasu Kiristocin da suka ƙaura zuwa wuraren da ake bukatar masu wa’azin Mulki sosai, suna bukatar su saba da yanayin rayuwar da ta bambanta da irin wanda suke yi a dā. Bambancin da ke tsakanin yanayin Yesu a duniya da kuma a sama ba ƙarami ba ne, domin a can yana zaune ne tare da Ubansa da kuma mala’iku waɗanda suke bauta wa Jehobah da muradi mai kyau. (Ayu. 38:7) Hakan ya bambanta da kasancewa a tsakanin mutane ajizai a lalatacciyar duniya. (Mar. 7:20-23) Yesu ya jimre kishin da ke tsakanin manzanninsa na kud da kud. (Luk 20:46; 22:24) Kuma ya bi da dukan al’amuran da ya fuskanta a duniya yadda ya kamata.
5 Ba wai Yesu ya soma yin yaren mutane ba ne a hanya ta mu’ujiza, amma ya soma koyan yaren ne tun yana jariri. Wannan ya bambanta da ba da umurni ga mala’ikun da ke sama. Sa’ad da yake duniya, aƙalla Yesu yana yin “harsunan mutane” guda ɗaya. Wannan ya bambanta sosai da ‘harsunan mala’iku.’ (1 Kor. 13:1) Idan kuwa ya zo ga kalamai masu jan hankali, babu mutumin da ya taɓa faɗin irin waɗannan kalaman kamar Yesu.—Luk 4:22.
6 Yi la’akari da wasu hanyoyin da abubuwa suka canja sosai ga Ɗan Allah sa’ad da ya zo duniya. Ko da yake Yesu bai gaji zunubi daga Adamu ba, ya zama mutum, kamar waɗanda za su zama “’yan’uwansa,” ko kuwa mabiya shafaffu. (Ka karanta Ibraniyawa 2:17, 18.) Duk da cewa yana da iko a kan mala’iku a matsayinsa na Miƙa’ilu Shugaban mala’iku, a darensa na ƙarshe a duniya, Yesu bai roƙi Ubansa na samaniya ya aiko da “rundunan mala’iku [da] ya fi goma sha biyu” ba. (Mat. 26:53; Yahu. 9) Hakika, Yesu ya yi mu’ujizai, duk da haka, abin da ya yi sa’ad da yake duniya bai kai abin da zai iya cim ma a sama ba.
7. Menene Yahudawa suka yi game da Doka?
7 Kafin ya zo duniya a matsayinsa na “Kalma,” wataƙila Yesu ne Kakakin Allah wanda ya yi wa Isra’ilawa ja-gora a cikin jeji. (Yoh. 1:1; Fit. 23:20-23) Duk da haka, sun “karɓi Attaurat, wadda malaiku suka bayas, ba [su kuwa] kiyaye ta ba.” (A. M. 7:53; Ibran. 2:2, 3) Shugabannin addinai Yahudawa na ƙarni na farko sun ƙi su fahimci ainihin ma’anar Doka. Alal misali, yi la’akari da dokar Assabaci. (Ka karanta Markus 3:4-6.) Marubuta da Farisawa sun “ƙyale matsaloli mafiya girma na Attaurat, shari’a, da jinƙai da bangaskiya.” (Mat. 23:23) Duk da haka, Yesu bai daina gaya musu gaskiya ba.
8. Me ya sa Yesu zai iya taimaka mana?
8 Yesu yana son ya taimaka wa mutane. Ƙaunar da yake yi wa mutane ta motsa shi kuma yana son ya taimaka musu. Bai taɓa yin sanyin gwiwa wajen yin bishara ba. Domin ya riƙe amincinsa ga Jehobah sa’ad da yake duniya, Yesu “ya zama dalilin ceto na har abada ga dukan waɗanda su ke yi masa biyayya.” Ƙari ga haka, “yayinda shi da kansa ya sha wahala ana jarabtassa, yana da iko ya taimaki [irin mu] waɗanda a ke jarabtassu.”—Ibran. 2:18; 5:8, 9.
Ƙwararren Malami
9, 10. Wace irin koyarwa ce Yesu ya samu kafin a aiko shi duniya?
9 Kafin a tura Kiristoci na zamani su je su yi wa’azi a ƙasashen waje, Hukumar Mulki tana sa a koyar da su. Yesu Kristi ya sami koyarwa kuwa? Yesu bai halarci makarantun manyan malamai na zamaninsa ba kafin ya zama Almasihu; kuma bai sami koyarwa daga fitattun shugaban addinai ba. (Yoh. 7:15; ka gwada Ayukan Manzanni 22:3.) Ta yaya ne Yesu ya ƙware don koyarwa?
10 Duk da abubuwan da Yesu ya koya daga mamarsa, Maryamu, da kuma mijinta, Yusufu, ya sami ainihin koyarwarsa ce ta hidima daga Jehobah. Game da wannan, Yesu ya ce: “Ban yi magana bisa kaina ba; amma Uba wanda ya aiko ni, shi ne ya ba ni umurni, abin da zan faɗi, da magana da zan yi kuma.” (Yoh. 12:49) Ka lura cewa an gaya wa Ɗan ainihin abin da zai koyar. Kafin ya zo duniya, Yesu ya daɗe yana sauraron umurnin Babansa. Babu wata koyarwar da zai samu da ta fi wannan.
11. Ta yaya ne Yesu ya nuna irin halayen Ubansa ga mutane?
11 Tun daga lokacin da aka halicce shi, Ɗan yana da dangantaka na kud da kud da Ubansa. Kafin ya zo duniya, Yesu ya fahimci irin halayen da Allah yake nuna wa mutane ta wajen kallon yadda Jehobah yake bi da su. Ɗan ya ƙaunaci mutane kamar yadda Allah yake ƙaunarsu, shi ya sa ya ce: “Daulata tana wurin ’yan adam.”—Mis. 8:22, 31.
12, 13. (a) Ta yaya ne Yesu ya koyi abubuwa ta wajen lura da yadda Ubansa ya bi da Isra’ilawa? (b) Ta yaya ne Yesu ya yi amfani da koyarwar da ya samu?
12 Koyarwar da Ɗan ya samu ta haɗa da kallon yadda Ubansa ya bi da matsaloli. Alal misali, yi la’akari da yadda Jehobah ya bi da Isra’ilawa masu taurin kai. Nehemiah 9:28 ta ce: “Amma bayanda suka huta, sai suka sake yin mugunta a gabanka: domin wannan ka bar su a cikin hannun maƙiyansu, har suka sami ikon mulkinsu: duk da hakanan, sa’anda suka komo suka yi kuka gareka, ka ji daga sama; so nawa kuma ka cece su bisa ga jinƙanka.” Domin ya yi aiki tare da Jehobah kuma yana lura da abubuwan da yake yi, Yesu ya nuna irin wannan tausayin ga mutanen da ke yankinsa.—Yoh. 5:19.
13 Yesu ya yi amfani da waɗannan abubuwan da ya koya yayin da yake bi da almajiransa cikin juyayi. A darensa na ƙarshe, dukan manzannin da yake ƙauna sosai “suka yashe shi, suka yi ta kansu.” (Mat. 26:56; Yoh. 13:1) Manzo Bitrus ma ya musunci sanin Kristi har sau uku! Duk da haka, Yesu ya ba manzanninsa damar koma masa. Ya gaya wa Bitrus: “Na yi maka addu’a kada bangaskiyarka ta kāsa: kai ma lokacin da ka sāke juyowa, sai ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” (Luk 22:32) An kafa Isra’ila ta ruhaniya a kan “manzanni da annabawa,” kuma duwatsun harsashin da aka ɗora bangon Sabuwar Urushalima a kai suna ɗauke ne da sunayen manzanni sha biyu masu aminci na Ɗan rago, Yesu Kristi. Har yanzu, shafaffun Kiristoci tare da keɓaɓɓun abokansu, “waɗansu tumaki,” suna samun ci gaba a matsayin ƙungiyar masu wa’azin Mulki a ƙarƙashin ikon Allah da kuma shugabancin ƙaunataccen Ɗansa.—Afis. 2:20; Yoh. 10:16; R. Yoh. 21:14.
Yadda Yesu ya Koyar da Mutane
14, 15. A waɗanne hanyoyi ne koyarwar Yesu ta bambanta da ta marubuta da Farisawa?
14 Ta yaya ne Yesu ya yi amfani da abubuwan da ya koya sa’ad da yake koyar da mabiyansa? Idan muka gwada koyarwar Yesu da ta shugabannin addinan Yahudawa, za mu ga cewa yadda Yesu yake koyarwa ya fi nasu kyau. Marubuta da Farisawa sun ‘maida maganar Allah wofi saboda al’adarsu.’ Akasin haka, Yesu bai koyar da ra’ayinsa ba amma ya manne wa maganar Allah, ko kuma saƙonsa. (Mat. 15:6; Yoh. 14:10) Abin da ya kamata mu yi ke nan.
15 Akwai wani abu kuma da ya sa Yesu ya bambanta da shugabannin addinan. Ga abin da ya ce game da marubuta da Farisawa: “Dukan abu fa iyakar abin da suka umurce ku, sai ku yi, ku kiyaye kuma: amma kada ku aika bisa ga nasu ayyuka; gama su kan faɗi, ba su kuwa aikawa.” (Mat. 23:3) Yesu ya aikata abin da ya koya wa mutane. Bari mu yi la’akari da misalin da ya nuna hakan.
16. Me ya sa za ka iya cewa Yesu ya yi rayuwar da ta jitu da kalmominsa da ke rubuce a Matta 6:19-21?
16 Yesu ya aririci almajiransa su “ajiye . . . dukiya cikin sama.” (Ka karanta Matta 6:19-21.) Yesu da kansa ya bi wannan umurnin ne? Hakika, shi ya sa ya faɗi wannan gaskiyar game da kansa: “Yanyawoyi suna da ramummukansu, tsuntsayen sama kuma suna da sheƙunansu, amma Ɗan mutum ba shi da wurin da za ya sa kansa.” (Luka 9:58) Yesu ya yi rayuwa mai sauƙi. Ya shagala da aikin sanar da bisharar Mulki, kuma ya nuna ma’anar kauce wa yin alhini da ke tattare da tara dukiya a duniya. Yesu ya nuna cewa ya fi kyau a tara dukiya a sama “inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su hudawa su yi sata ba.” Kana bin umurnin Yesu na tara dukiya a sama?
Halayen da Suka sa Mutane Suka So Yesu
17. Waɗanne halaye ne suka sa Yesu ya zama mai yin bishara da babu kamarsa?
17 Waɗanne halaye ne suka sa Yesu ya zama mai yin bishara da babu kamarsa? Na ɗaya shi ne yadda ya bi da mutanen da ya taimaka musu. Wasu cikin halayen Jehobah da Yesu ya nuna su ne tawali’u, ƙauna da kuma juyayi. Ka lura da yadda waɗannan halayen suka sa mutane da yawa suka kusanci Yesu.
18. Me ya sa za a ce Yesu mai tawali’u ne?
18 Domin Yesu ya yarda cewa zai zo duniya, “ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane.” (Filib. 2:7) Ya nuna tawali’u ta wajen yin hakan. Bugu da ƙari, Yesu bai rena mutane ba. Bai nuna irin halin, ‘Na zo daga sama, saboda haka dole ne ku saurare ni.’ Akasin waɗanda suka mai da kansu almasihun ƙarya, Yesu bai yaɗa matsayinsa na Almasihu na gaskiya ba. Akwai lokatan da ya gaya wa mutane cewa kada su gaya wa wasu ko shi wanene ko kuma abin da ya yi. (Mat. 12:15-21) Yesu yana son mutane su tsai da shawarar binsa don abin da suka gani da kansu. Almajiransa sun amfana sosai domin Ubangijinsu ba ya bukatar su zama kamar kamiltattun mala’iku waɗanda ya yi tarayya da su a sama!
19, 20. Ta yaya ƙauna da juyayi suka motsa Yesu ya taimaki mutane?
19 Yesu Kristi ya kuma nuna ƙauna, hali na musamman na Ubansa na sama. (1 Yoh. 4:8) Yesu ya koyar da masu sauraronsa domin yana ƙaunarsu. Alal misali, ka yi la’akari da yadda ya ji game da wani saurayi mai sarauta. (Ka karanta Markus 10:17-22.) Yesu ya “ƙaunace shi” kuma yana son ya taimake shi, amma saurayin mai sarauta bai bar dukiyoyinsa ba domin ya zama mabiyin Kristi.
20 Nuna juyayi yana cikin halayen da ya sa mutane suke son Yesu. Kamar dukan ’yan adam ajizai, waɗanda suka saurari koyarwarsa suna da matsaloli. Tun da yake ya san da haka, Yesu ya koyar da su cikin juyayi kuma ya ji tausayinsu. Alal misali: Akwai lokacin da Yesu da manzanninsa suke aiki sosai da ba su da lokacin cin abinci. Amma, menene Yesu ya yi sa’ad da ya ga taron jama’a da suka taru? ‘Ya ji juyayinsu, gama kamar tumaki su ke waɗanda ba su da makiyayi: ya fara koya masu abu dayawa.’ (Mar. 6:34) Yesu ya lura da yanayi na ban tausayi da mutanen da ke yankinsa suke ciki kuma ya ba da kansa ya koyar da su kuma ya yi mu’ujizai da ya amfane su. Wasu sun so shi domin halayensa masu kyau, kuma maganarsa ta motsa su suka zama almajiransa.
21. Menene za mu tattauna a talifi na gaba?
21 Da akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya game da hidimar Yesu a duniya, kuma talifi na gaba zai nuna wannan. A waɗanne ƙarin hanyoyi ne za mu iya yin koyi da Yesu Kristi, Mai Wa’azi mafi girma?
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Wace koyarwa ce Yesu ya samu kafin ya zo duniya?
• Ta yaya koyarwar Yesu ta fi ta marubuta da Farisawa kyau?
• Waɗanne halaye ne suka sa mutane suke son Yesu?
[Hoto a shafi na 15]
Ta yaya ne Yesu ya koyar da taron jama’a?