“Waɗanda Aka Ƙadara” Suna Sauraron Bishara
“Waɗanda aka ƙadara su ga rai na har abada suka bada gaskiya.”—AYUKAN MANZANNI 13:48.
1, 2. Ta yaya ne Kiristoci na farko suka yi amfani da annabci na Yesu da ya ce za a yi shelar bishara a dukan duniya?
LITTAFIN Ayukan manzanni na Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labari mai daɗi game da yadda Kiristoci na farko suka ɗauki annabcin Yesu da ya ce za a yi bisharar Mulki a dukan duniya. (Mat. 24:14) Masu shela da himma sun nuna wa dukan waɗanda suke so su bi su misali. A sakamakon wa’azin da almajiran Yesu suka yi da himma a Urushalima, mutane da yawa har da “babban taro . . . na malamai,” suka shiga cikin ikilisiya na ƙarni na farko.—A. M. 2:41; 4:4; 6:7.
2 Masu wa’azi na ƙasashen waje na ƙarni na farko sun taimaki mutane da yawa su zama Kirista. Alal misali, Filibbus ya je Samariya, inda mutane masu yawa suka saurari kalmarsa. (A. M. 8:5-8) Bulus ya yi tafiya sosai tare da abokane dabam dabam, suna wa’azi a Kubrus, da bangaren ƙasar Asiya ƙarama, da Makidoniya, da Hellas da kuma ƙasar Italiya. Yahudawa da Helenawa masu yawa sun zama masu bi a biranen da ya yi wa’azi. (A. M. 14:1; 16:5; 17:4) Titus ya yi wa’azi a ƙasar Karita. (Tit. 1:5) Bitrus yana taƙure a Babila kuma a lokacin da ya rubuta wasiƙarsa ta farko a kusan shekara ta 62 zuwa shekara ta 64 A.Z., an riga an san game da aikin wa’azi na Kirista a ƙasar Buntus, da Galatiya, da Kappadokiya da Asiya, da Butiniya. (1 Bit. 1:1; 5:13) Waɗannan lokaci na farin ciki ne. Kiristoci na farko sun yi wa’azi da himma har maƙiyansu suka ce wai sun “birkitarda duniya.”—A. M. 17:6; 28:22.
3. Waɗanne sakamako ne masu shelar Mulki suke samu a aikin wa’azi da suke yi a yau, kuma yaya ka ke ji?
3 A zamanin nan ma, ikilisiyar Kirista tana karuwa. Kana samun ƙarfafa sa’ad da ka karanta rahoto na shekara na Shaidun Jehobah kuma ka ga sakamakon da aka samu a duka duniya? Kana farin ciki ka ji cewa masu shelar Mulki sun yi nazari na Littafi Mai Tsarki fiye da miliyan shida a shekarar hidima na shekara ta 2007? Bugu da ƙari, waɗanda suka halarci taron tuna mutuwar Yesu Kristi a shekarar da ta wuce ya nuna cewa kusan mutane miliyan goma da ba Shaidun Jehobah ba ne suna son bisharar nan shi ya sa suka halarci wannan taro mai muhimmanci. Hakan ya nuna cewa har ila akwai aiki mai yawa da za a yi.
4. Su wanene suke saurarar saƙon Mulki?
4 Kamar a ƙarni na farko, a yau, dukan “waɗanda aka ƙaddara su ga rai na har abada” suna saurarar saƙo na gaskiya. (A. M. 13:48) Jehobah yana jawo mutane zuwa ƙungiyarsa. (Ka karanta Haggai 2:7.) Wane hali ne game da hidimar Kirista ya kamata mu riƙe don mu ba da goyon baya ga wannan aikin tattarawa?
Ka Yi Wa’azi ban da Son Kai
5. Waɗanne irin mutane ne suke samun tagomashin Jehobah?
5 Kiristoci na ƙarni na farko sun fahimci cewa “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (A. M. 10:34, 35) Mutumin da ke son ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah yana bukatar ya ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu. (Yoh. 3:16, 36) Kuma nufin Jehobah ne cewa “dukan [ire-iren] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”—1 Tim. 2:3, 4.
6. Menene ya kamata masu wa’azin Mulki su guje wa, kuma me ya sa?
6 Ba zai dace ba idan masu shelar bishara suka yi watsi da mutane domin ƙasar da suka fito, matsayinsu, shigen da suka yi, irin addininsu, ko kuma domin duk wani irin halin da ya sa suka fita dabam ba. Ka ɗan yi la’akari da wannan: Ba ka godiya cewa mutumin da ya soma gaya maka gaskiyar da ke cikin Nassi bai nuna maka son kai ba? Saboda haka, me zai sa ka ƙi gaya wa duk mutumin da zai saurare ka saƙon da zai iya ceton ransa?—Ka karanta Matta 7:12.
7. Me ya sa ya kamata mu guje wa yanke hukunci a kan waɗanda muke yi wa wa’azi?
7 Jehobah ya naɗa Yesu a matsayin Mai Shari’a, saboda haka, ba mu da ikon yi wa kowa shari’a. Wannan ya dace domin mu muna yin shari’a ne “bisa ga abinda ya bayyana ga idanun [mu]” ko kuwa “bisa ga abin da kunnen [mu] ke ji,” shi kuwa Yesu yana iya sanin abin da ke zuciyar mutum.—Isha. 11:1-5; 2 Tim. 4:1.
8, 9. (a) Wane irin mutumi ne Shawulu kafin ya zama Kirista? (b) Menene ya kamata mu koya daga labarin manzo Bulus?
8 Mutane daga ko’ina sun zama bayin Jehobah. Wani fitaccen misali shi ne Shawulu na Tarsus, wanda ya zama manzo Bulus. Shawulu Bafarisi ne mai hamayya da Kiristoci sosai. Ya tabbata cewa su ba masu bauta wa Jehobah da gaskiya ba ne shi ya sa yake tsananta wa ikilisiyar Kirista. (Gal. 1:13) A ra’ayin mutane, ana iya cewa ba zai taɓa zama Kirista ba. Duk da haka, Yesu ya ga wani abu mai kyau a zuciyar Shawulu kuma ya zaɓe shi ya yi wani aiki mai muhimmanci. A sakamakon hakan, Shawulu ya zama mai ƙwazo da himma sosai a ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko.
9 Menene labarin manzo Bulus ya koya mana? A yankinmu ƙila akwai mutanen da ba sa ƙaunar saƙon da muke sanarwa. Ko da yake muna iya yin shakkar cewa ba za su zama Kiristoci na gaskiya ba, kada mu daina tattaunawa da su. A wasu lokatan mutanen da muke tunanin cewa ba sa son gaskiya suna sauraronmu. Umurnin da aka ba mu shi ne mu ci gaba da yin wa’azi ga kowa ‘babu fasawa.’—Ka Karanta Ayukan Manzanni 5:42.
Waɗanda Suke Wa’azi ‘Babu Fasawa’ Za Su Sami Albarka
10. Me ya sa bai dace ba mu ƙi yin wa’azi ga mutanen da ke da ban tsoro? Ka faɗi labarai daga yankinka.
10 Irin shigen da mutane suka yi na iya ruɗar mu. Alal misali, Ignacio,a ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah sa’ad da yake kurkuku a ƙasar Amirka ta Kudu. Mutane suna jin tsoronsa domin mugun halinsa. Saboda haka, waɗanda suke cikin kurkuku da suke sayar da abubuwa ga waɗanda suke cikin kurkukun tare, sukan yi amfani da Ignacio wajen karɓan bashi daga wajen waɗanda suka ƙi biyan bashin da ake bin su. Amma, sa’ad da Ignacio ya sami cin gaba a ruhaniya kuma ya yi amfani da abin da yake koya, wannan mugun mutumin ya zama mutumin kirki. Babu wanda ya ƙara amfani da shi wajen karɓan bashi, duk da haka, Ignacio ya gamsu cewa gaskiyar Littafi Mai Tsarki da kuma ruhun Allah ne suka sa ya canja halinsa. Kuma ya yi farin ciki sosai domin rashin son kai da masu shelar Mulki da suka yi nazari da shi suka nuna masa.
11. Me ya sa muke sake ziyarar mutane?
11 Ɗaya cikin dalilan da ya sa muke ci gaba da komawa wajen mutanen da muka gaya wa bishara shi ne yanayinsu da halayensu yana iya canjawa kuma yana canjawa. Tun ziyararmu na ƙarshe, wataƙila wasu sun yi mugun rashin lafiya, sun rasa aikinsu, ko kuma sun yi rashin wani wanda suke ƙauna. (Ka karanta Mai Wa’azi 9:11.) Abubuwan da ke faruwa a duniya suna iya sa mutane su yi tunani sosai game da rayuwarsu ta nan gaba. Irin waɗannan abubuwan suna iya sa mutumin da a dā ba ya son ya saurare mu ko kuwa yana hamayya da mu, ya soma sauraronmu. Saboda haka, kada mu ƙi gaya wa mutane bishara a duk lokacin da ya dace.
12. Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi game da mutanen da muke yi wa wa’azi, kuma me ya sa?
12 Halin ’yan adam ne su haɗa mutane kuma su yanke hukunci a kansu. Duk da haka, Jehobah ba ya haɗa wani da wani. Yana ganin halaye masu kyau na kowannenmu. (Ka karanta 1 Samuila 16:7.) Ya kamata mu ma mu yi hakan a hidimarmu. Labarai masu yawa sun nuna cewa ana samun sakamako mai kyau idan muka kasance da ra’ayin da ya dace ga mutanen da muke yi wa wa’azi.
13, 14. (a) Me ya sa wata majagaba ta ƙi kula da wata matar da ta sadu da ita a hidima? (b) Menene za mu iya koya daga wannan labarin?
13 Sandra, wata ’yar’uwa majagaba tana wa’azi na gida-gida a wani tsibiri a ƙasar Karibiya a inda ta sadu da Ruth wadda ta shagala da wani irin bikin da ake yi na yin rawa da wasa iri-iri a ƙasashen Turai. An naɗa Ruth sau biyu a matsayin sarauniyar bikin. Ta nuna tana son abin da Sandra ke cewa, sai suka shirya yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Sandra ta ce: “A lokacin da na shiga ɗakinta, na ga babban hoton Ruth inda take sanye da rigar yin rawa, da kuma lambar yabon da ta samu. Na yi zaton cewa irin wannan mutumiyar da ta yi suna kuma wadda ta shagala a irin waɗannan bukukuwan ba za ta so gaskiya ba. Sai na daina zuwa wurinta.”
14 Bayan wasu lokatai, sai Ruth ta bayyana a Majami’ar Mulki, kuma bayan an tashi taron, sai ta tambayi Sandra, “Me ya sa ki ka daina zuwa yin nazari da ni?” Sandra ta ba ta haƙuri kuma sai suka soma yin nazarin. Ruth ta sami cin gaba sosai, ta cire hotunanta na bikin, ta soma saka hannu a cikin dukan ayyukan ikilisiya, kuma ta keɓe rayuwarta ga Jehobah. Daga baya, Sandra ta fahimci cewa matakin da ta ɗauka a farko bai dace ba.
15, 16. (a) Menene ya faru sa’ad da wani mai shela ya yi wa danginsa wa’azi? (b) Me ya sa bai kamata halin wani danginmu ya hana mu yi masa ko mata wa’azi ba?
15 Yawancin mutanen da suka yi wa ’yan’uwansu marasa bi wa’azi sun sami sakamako mai kyau, har da ma waɗanda suke tunanin cewa ba za su saurara ba. Yi la’akari da misalin Joyce, wata ’yar’uwa Kirista da ke zaune a ƙasar Amirka. Ƙanin tsohon mijin ƙanwarta ya sha shiga da fita kurkuku tun yana matashi. “Mutane sun ce rayuwarsa ba ta da amfani,” in ji Joyce, “domin shi ɗan ƙwaya ne, yana sata, kuma ya yi abubuwa marar kyau da dama. Duk da waɗannan maganganun, na ci gaba da gaya masa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki har tsawun shekaru talatin da bakwai.” Haƙurin da ta yi don ta taimaka wa ɗan’uwanta ya zama abin farin ciki sa’ad da ya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare da Shaidun Jehobah kuma ya canja salon rayuwarsa. Kwanakin baya, sa’ad da yake ɗan shekara 50, ƙanin tsohon mijin ƙanwar Joyce ya yi baftisma a taron gunduma a garin Kalifoniya, a ƙasar Amirka. Joyce ta ce: “Na yi kukan murna. Ina farin ciki sosai cewa ban ƙyale shi ba!”
16 Kana iya jinkirin yi wa wasu danginka magana game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki domin imaninsu na addini. Amma, wannan bai hana Joyce yi wa ƙanin tsohon mijin ƙanwarta magana ba. Ballantana ma, ta yaya mutum zai san abin da ke zuciyar wani? Wataƙila wannan mutum da gaske yana neman gaskiyar addini. Saboda haka, kada ka hana shi ko ita zarafin samun addinin.—Ka Karanta Misalai 3:27.
Littafi Mai Kyau na Nazarin Littafi Mai Tsarki
17, 18. (a) Menene rahotanni daga dukan duniya suka nuna game da tamanin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? (b) Waɗanne abubuwa masu kyau ne ka shaida ta wajen yin amfani da wannan littafin?
17 Rahotannin da ake samu daga ƙasashe a dukan duniya sun nuna cewa mutane da yawa masu zuciyar kirki suna yin amfani da abin da suke koya a cikin littafin nan na nazarin Littafi Mai Tsarki mai suna Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Penni, wata majagaba a ƙasar Amirka ta soma yin nazari da mutane masu yawa da wannan littafin. Biyu a cikinsu tsofaffi ne kuma suna da ƙwazon zuwa cocinsu. Penni ba ta san yadda za su ɗauki gaskiyar Nassi da ke cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Duk da haka ta rubuta, “Domin yadda aka gabatar da bayanin da ke ciki a hanya mai sauƙi, kuma taƙaitacce, sun yarda cewa abin da suke koya gaskiya ne, babu gardama ko ɓacin rai.”
18 Pat, wata mai shela a ƙasar Britaniya, ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata wadda ’yar gudun hijira ce daga ƙasar Asiya. An tilasta wa matar ta gudu daga ƙasarsu bayan sojojin ’yan tawaye sun ɗauke mijinta da ’ya’yanta kuma ba ta ƙara ganinsu ba. An yi mata barazana, an ƙona gidanta, kuma an taru an yi mata fyaɗe. Dukan waɗannan abubuwan sun sa take jin cewa ba ta da wani manufa a rayuwa, kuma sau da yawa ta so ta kashe kanta. Amma nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa ta kasance da bege. Pat ta rubuta: “Domin bayanai da kuma kwatancen da ke cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? suna da sauƙi, hakan ya shafi rayuwarta sosai.” Ɗalibar ta samu cin gaba sosai, ta zama mai shelar da ba ta yi baftisma ba, kuma ta nuna tana son ta yi baftisma a babban taro na gaba. Abin farin ciki ne mu taimaka wa mutanen da suke son gaskiya su fahimci kuma su so begen da ke cikin Nassosi!
“Kada Mu Yi Kasala Kuma Cikin Aikin Nagarta”
19. Me ya sa yin wa’azi aiki ne na gaggawa?
19 Da shigewar kowace rana, aikinmu na yin wa’azi da almajirantarwa yana ƙara gaggautawa. A kowace shekara, dubban masu zuciyar kirki suna yin na’am ga aikinmu na yin wa’azi. Duk da haka, “babbar ranar Ubangiji ta kusa,” hakan na nufin cewa sauran waɗanda suke cikin duhu na ruhaniya “suna kusa ga yanka.”—Zeph. 1:14; Mis. 24:11.
20. Menene ya kamata dukanmu mu ƙudurta yi?
20 Duk da haka muna iya taimaka wa irin waɗannan mutanen. Amma idan muna son mu yi hakan, dole ne mu yi koyi da Kiristoci na ƙarni na farko, waɗanda ‘ba su fāsa koyaswa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.’ (A. M. 5:42) Ka bi misalinsu ta wajen nacewa duk da wahala, ta wajen mai da hankali ga ‘iya koyarwarka,’ da kuma yin wa’azi ga dukan mutane babu son kai! “Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta,” domin idan muka nace, za mu sami amincewar Allah.—2 Tim. 4:2; ka karanta Galatiyawa 6:9.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.
Mecece Amsarka?
• Su waye ne suke sauraron bishara?
• Me ya sa bai kamata mu yi watsi da mutanen da muke yi wa wa’azi ba?
• Waɗanne sakamako ne aka samu ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
[Hotuna a shafi na 13]
Dubban masu zukatan kirki suna sauraron bishara
[Hotuna a shafi na 15]
Menene za mu iya koya daga canje-canjen da manzo Bulus ya yi?
[Hoto a shafi na 16]
Masu yin bishara ba sa yin watsi da mutane