Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 pp. 4-8
  • “Ka Yi Lura Da Hidima Wadda Ka Karɓa Cikin Ubangiji”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Yi Lura Da Hidima Wadda Ka Karɓa Cikin Ubangiji”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dalilin da ya sa Yawancin Mutane Ba su da Bege
  • Ka Ci Gaba da Yin Wa’azi ‘Babu Fasawa’
  • ‘Ka Ci Gaba da Lura da Hidimarka’
  • Yadda Za A Magance Ƙalubale Na Hidimar Gida Gida
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Kana Cika Hidimarka ga Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Ɗokanta A Yin Shelar Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Yin Wa’azi Da Ƙarfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 pp. 4-8

“Ka Yi Lura Da Hidima Wadda Ka Karɓa Cikin Ubangiji”

“Ka yi lura da hidima wadda ka karɓa cikin Ubangiji, domin ka cika ta.”—KOL. 4:17.

1, 2. Wane hakki na mutane ne ke kan Kiristoci?

MUNA da hakki mai girma na mutanen da suke zaune kusa da mu. Shawarar da suka yanke a yanzu zai sa su sami rai ko kuma su mutu a lokacin “babban tsanani.” (R. Yoh. 7:14) Hurarren marubucin littafin Misalai ya ce: “Ka ceci waɗanda an kai su ga mutuwa, Waɗanda suna kusa ga yanka kuma, sai ka riƙe su.” Waɗannan kalamai ne masu muhimmanci! Idan muka ƙi cika hakkinmu na yi wa mutane gargaɗi game da zaɓin da ke gabansu, hakan na iya sa mu ɗauki alhakinsu. Ɗayar ayar ta ci gaba da cewa: “Idan ka ce, Ga shi, ba mu san wannan ba: Mai-auna zukata ba ya lura ba? Mai-kiwon ranka kuma, ba ya sani ba? Ba za ya saka ma kowane mutum gwalgwadon aikinsa ba?” Babu shakka, bayin Jehobah ba za su ce ‘ba su san’ haɗarin da mutane suke ciki ba.—Mis. 24:11, 12.

2 Jehobah yana ɗaukan rai da tamani. Ya umurci bayinsa su yi iya ƙoƙarinsu su taimaki mutane masu yawa su sami rai. Dole ne kowane mai yi wa Allah hidima ya sanar da saƙon da ke ba da rai da ke cikin Kalmar Allah. Aikin da aka ba mu yana kama ne da na mai tsaro wanda zai yi sanarwa idan ya ga haɗari. Ba ma son mu ɗauki alhakin mutuwarsu. (Ezek. 33:1-7) Saboda haka, yana da muhimmanci sosai mu yi iya ƙoƙarinmu a wajen “wa’azin kalma.”—Ka karanta 2 Timothawus 4:1, 2, 5.

3. Waɗanne batutuwa ne za a tattauna a wannan talifin da kuma talifofi biyu na gaba?

3 A wannan talifin za ka koyi yadda za ka sha kan tangarɗa a hidimarka ta ceton rai da kuma yadda za ka taimaka wa mutane masu yawa. Talifi na gaba zai tattauna yadda za ka iya koyar da gaskiya. Talifi na uku zai ba da rahoto ne a kan wasu sakamako masu kyau da masu shelar Mulki a dukan duniya suka samu. Kafin mu tattauna waɗannan batutuwan, zai dace mu sake bincika dalilin da ya sa zamaninmu ke da wuya sosai.

Dalilin da ya sa Yawancin Mutane Ba su da Bege

4, 5. Menene mutane suke fuskanta, kuma wane mataki ne mutane suke ɗauka?

4 Abubuwan da ke faruwa a duniya sun nuna cewa muna zaune ne a “cikar zamani” kuma ƙarshe ya kusa sosai. Mutane suna shaida aukuwa da yanayin da Yesu da almajiransa suka ce zai auku a “kwanaki na ƙarshe.” “Wahala,” har da yaƙoƙi, karancin abinci, girgizar ƙasa, da sauran bala’o’i suna addabar mutane. Taka doka, son kai, da kuma halaye marar kyau sun zama gama gari. Har ma mutanen da suke iya ƙoƙarinsu su bi mizanan Littafi Mai Tsarki suna fuskantar “miyagun zamanu.”—Mat. 24:3, 6-8, 12; 2 Tim. 3:1-5.

5 Yawancin mutane a duniya ba su san ainihin ma’anar abubuwan da ke faruwa a duniya ba. Domin haka, yawancin mutane sun damu ne kawai da yadda za su kāre kansu da kuma iyalansu. Rashin wanda ake ƙauna ko kuwa bala’i ya jefa yawancin mutane cikin matsanancin hali. Mutanen nan ba su da bege domin ba su da cikakken sani na dalilin da ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa da kuma abin da zai magance matsalolin.—Afis. 2:12.

6. Me ya sa “Babila Babba” ta kasa taimaka wa mabiyanta?

6 “Babila Babba,” daular duniya na addinin ƙarya ba ta taimaka wa mutane. Akasin haka, ta wajen “ruwan anab na fasikancinta,” ta ruɗi mutane da yawa a ruhaniya. Bugu da ƙari, ta wajen yi kamar karuwa, addinin ƙarya ta ruɗi kuma ta mulki “sarakunan duniya,” ta yin amfani da koyarwar ƙarya da kuma sihiri don ta sa yawancin mutane su yi duk abin da gwamnati ta ce su yi. Addinin ƙarya ta sami iko kuma ta yi suna, amma, ta yi watsi gabaki ɗaya da addini ta gaskiya.—R. Yoh. 17:1, 2, 5; 18:23.

7. Wane bege ne yawancin ’yan adam suke da shi, kuma ta yaya za a iya taimaka wa wasu?

7 Yesu ya koyar da cewa yawancin mutane suna tafiya ne a kan hanya mai faɗi da ke kai ga halaka. (Mat. 7:13, 14) Wasu mutane suna kan wannan hanyar domin sun zaɓi su ƙi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ne, amma yawancin mutane suna kan ta ne domin an ruɗe su, ko kuwa suna cikin duhu, game da ainihin abin da Jehobah yake bukata a gare su. Wataƙila wasu za su canja salon rayuwarsu idan suka ji dalilai masu kyau na yin hakan daga Nassi. Amma waɗanda suka ci gaba da kasancewa a cikin Babila Babba kuma suka ci gaba da ƙin mizanan Littafi Mai Tsarki ba za su tsira ba a lokacin “babban tsanani.”—R. Yoh. 7:14.

Ka Ci Gaba da Yin Wa’azi ‘Babu Fasawa’

8, 9. Menene Kiristoci na ƙarni na farko suka yi sa’ad da suka fuskanci hamayya, kuma me ya sa?

8 Yesu ya ce almajiransa za su yi wa’azin bisharar Mulki kuma za su almajirantar da mutane. (Mat. 28:19, 20) Saboda haka, Kiristoci na gaskiya a kowane lokaci sun ɗauki yin wa’azi a matsayin nuna aminci ga Allah da kuma ainihin abin da ake bukata daga gare su saboda bangaskiyarsu. Shi ya sa mabiyan Yesu na farko suka dage har ma a lokacin hamayya. Sun dogara ga Jehobah don samun ƙarfi, kuma sun roƙe shi ya sa su ci gaba da ‘faɗin maganarsa da ƙarfinzuciya duka.’ Ta wajen amsa addu’arsu, Jehobah ya cika su da ruhu mai tsarki, kuma suka faɗi kalmar Allah da gaba gaɗi.—A. M. 4:18, 29, 31.

9 Sa’ad da hamayya ta zama mugunta, mabiyan Yesu sun daina yin wa’azin bishara ne? Ko kaɗan. Domin wa’azin da manzannin suke yi yana ba su haushi, shugabannin addinan Yahudawa suka kama manzannin, suka yi masu barazana, kuma suka yi masu bulala. Duk da haka, manzannin “ba su fāsa koyaswa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.” Sun ga cewa suna bukatar su “fi biyayya ga Allah da mutane.”—A. M. 5:28, 29, 40-42.

10. Waɗanne ƙalubale ne Kiristoci suke fuskanta a yau, duk da haka, menene zai iya faruwa domin halinsu mai kyau?

10 Yawancin bayin Allah a yau ba su taɓa fuskantar bugu ko shiga kurkuku domin ayyukan wa’azin da suke yi ba. Amma, dukan Kiristoci na gaskiya suna fuskantar jarraba dabam dabam. Alal misali, lamirinka da Littafi Mai Tsarki ya koyar zai iya sa ka bi tafarkin da ba sananne ba ne ko kuwa wanda zai sa ka bambanta da sauran mutane. Abokan aiki, abokan makaranta, ko kuwa maƙwabta suna iya tunanin cewa kai wani irin mutumi ne domin kana bin mizanan Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, kada ka yarda maganganun banzan da suke yi ya sa ka ja da baya. Wannan duniyar tana cikin duhu na ruhaniya, amma Kiristoci suna bukatar su kasance da ‘haske.’ (Filib. 2:15) Wataƙila wasu masu son gaskiya da suke kallon ku za su ga kuma su yi sha’awar ayyukanku masu kyau kuma su ɗaukaka Jehobah.—Ka karanta Matta 5:16.

11. (a) Menene wasu za su iya yi domin aikin wa’azi? (b) Wane irin hamayya ne manzo Bulus ya fuskanta, kuma menene ya ce?

11 Muna bukatar gaba gaɗi don mu ci gaba da yin wa’azin saƙon Mulki. Wasu mutane, har da ’yan’uwanka suna iya yi maka ba’a ko kuwa su nemi su sa ka karaya. (Mat. 10:36) Sau da yawa an bugi manzo Bulus domin ya ci gaba da yin hidimarsa da aminci. Ka lura da abin da ya ce game da wannan hamayyar: “Mu da muka rigaya muka sha wuya, har da wulakanci, . . . muka yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah cikin husuma mai-yawa.” (1 Tas. 2:2) Hakika, ya zama ƙalubale ga Bulus ya ci gaba da faɗin bishara bayan an kama shi, an cire tufafinsa, aka buge shi, kuma aka jefa shi a cikin kurkuku. (A. M. 16:19-24) Menene ya ba shi gaba gaɗin ci gaba da wa’azi? Muradinsa ne na cika aikin wa’azi da Allah ya ba shi.—1 Kor. 9:16.

12, 13. Waɗanne matsaloli ne wasu suke fuskanta, kuma ta yaya suka yi ƙoƙarin magance su?

12 Yana iya yi mana wuya mu ci gaba da kasancewa da ƙwazo a yankunan da ba a yawan samun mutane a gida ko kuwa a inda mutane ba sa sauraron saƙon Mulki. Menene za mu iya yi a irin waɗannan yanayin? Wataƙila muna bukatar mu ƙara nuna gaba gaɗi don yi wa mutane wa’azi a kowane yanayi. Ƙila kuma muna bukatar canja tsarinmu ko kuwa mu mai da hankali a kan yin wa’azi a wuraren da za mu iya samun mutane da yawa.—Ka gwada Yohanna 4:7-15; Ayukan Manzanni 16:13; 17:17.

13 Wasu matsalolin da yawanci suke fama da su su ne tsufa da rashin lafiya, kuma hakan na iya rage abin da za su iya yi a aikin wa’azi. Idan abin da ka ke fama da shi ke nan, kada ka karaya. Jehobah yana sane da yanayinka kuma yana farin ciki da abin da za ka iya yi. (Ka karanta 2 Korinthiyawa 8:12.) Duk irin wahalar da ka ke sha, hala hamayya, wariya, ko rashin lafiya, ka yi iya abin da za ka iya wajen gaya wa mutane bishara.—Mis. 3:27; ka gwada Markus 12:41-44.

‘Ka Ci Gaba da Lura da Hidimarka’

14. Wane misali ne manzo Bulus ya kafa wa ’yan’uwa Kiristoci, kuma wace shawara ce ya ba su?

14 Manzo Bulus ya ɗauki hidimarsa da muhimmanci sosai, kuma ya ƙarfafa ’yan’uwansa masu bi su yi hakan. (A. M. 20:20, 21; 1 Kor. 11:1) Wani mutumin da Bulus ya ƙarfafa sosai shi ne wani Kirista na ƙarni na farko mai suna Arkibbus. A cikin wasiƙarsa ga Kolosiyawa, Bulus ya rubuta: “Ku ce ma Arkibbus kuma, Ka yi lura da hidima wadda ka karɓa cikin Ubangiji, domin ka cika ta.” (Kol. 4:17) Ba mu san ko wanene Arkibbus ba da kuma yanayinsa, amma babu shakka yana wa’azi. Idan kai Kirista ne wanda ya keɓe kansa, kai ma kana da hidima. Kana ci gaba da lura da hidimarka don ka cika ta?

15. Menene keɓe kai na Kirista ya ƙunsa, waɗanne tambayoyi ne ya ta da?

15 Kafin mu yi baftisma, mun keɓe rayuwarmu ga Jehobah a cikin addu’a. Hakan yana nufin cewa mun ƙuduri aniyar yin nufinsa. Zai dace mu tambayi kanmu a yanzu, ‘Yin nufin Allah ne ainihin abin da ya fi muhimmanci a rayuwata?’ Wataƙila muna da hakki dabam dabam da Jehobah yake son mu cika, kamar su yi wa iyalinmu tanadi. (1 Tim. 5:8) Amma yaya muke amfani da sauran lokacinmu da kuma ƙarfinmu? Menene ya fi muhimmanci a rayuwarmu?—Ka karanta 2 Korinthiyawa 5:14, 15.

16, 17. Waɗanne zarafi ne Kiristoci matasa ko kuwa waɗanda ba su da hakki sosai za su iya yin tunani a kai?

16 Kai Kirista ne matashi wanda ya keɓe kansa kuma ya kammala ko kuwa yake gab da kammala makarantar sakandare? Wataƙila ba ka da hakkin da za ka ɗauka na iyali. Saboda haka, menene ka ke shirin yi da rayuwarka? Waɗanne shawarwari ne za su sa ka cika alkawarinka na yin nufin Jehobah? Yawanci sun daidaita al’amuransu domin su zama majagaba, kuma sun sami farin ciki sosai da gamsuwa.—Zab. 110:3; M. Wa. 12:1.

17 Wataƙila kai saurayi ne. Kana da aiki na cikakken lokaci amma ba ka da hakki mai yawa a kanka sai dai kawai na kula da kanka. Babu shakka kana more saka hannu a ayyukan ikilisiya yadda za ka iya. Za ka so ka sami ƙarin farin ciki? Ka taɓa tunanin faɗaɗa hidimarka? (Zab. 34:8; Mis. 10:22) A wasu yankuna ana bukatar yin ayyuka masu yawa don gaya wa kowa saƙon gaskiya mai ba da rai. Za ka iya yin gyara a rayuwarka, wataƙila yin hidima a wuraren da ake bukatar masu yin wa’azin Mulki sosai?—Ka karanta 1 Timothawus 6:6-8.

18. Waɗanne canje-canje ne wasu ma’aurata matasa suka yi, kuma menene sakamakon?

18 Yi la’akari da misalin Kevin da Elena, da ke zaune Amirka.a Kamar yadda sababbin ma’aurata suke yi a yankinsu, sun ga cewa suna bukatar su sayi gida. Su biyun suna aiki na cikakken lokaci saboda haka za su iya ci gaba da more rayuwarsu. Duk da haka, aikin da suke yi da kuma ayyukan gida sun sa ba su da isashen lokacin yin wa’azi. Sun ga cewa suna ba da dukan lokacinsu da kuzarinsu ga dukiyoyinsu. Amma, sa’ad da suka ga irin rayuwa mai sauƙi da wasu majagaba ma’aurata masu farin ciki suke yi, Kevin da Elena sun yanke shawarar salon rayuwarsu. Bayan sun nemi ja-gorar Jehobah a addu’a, sai suka sayar da gidansu kuma suka tare cikin wani ƙaramin gida. Elena ta rage lokacin aikin da take yi kuma ta zama majagaba. Domin abubuwan da matarsa take shaidawa sun ƙarfafa shi, Kevin ya ajiye aikinsa na cikakken lokaci kuma ya zama majagaba. Bayan wani lokaci, sun ƙaura zuwa ƙasar Amirka ta Kudu don su yi hidima a inda ake bukatar masu wa’azin Mulki. “Muna farin ciki tun lokacin da muka yi aure,” in ji Kevin, “amma sa’ad da muka faɗaɗa hidimarmu, farin cikinmu ya ƙaru sosai.”—Ka karanta Matta 6:19-22.

19, 20. Me ya sa yin wa’azin bishara shi ne aiki mafi muhimmanci a yau?

19 Yin wa’azin bishara shi ne aiki mafi muhimmanci da ake yi a duniya a yau. (R. Yoh. 14:6, 7) Yana taimaka mana mu tsarkake sunan Jehobah. (Mat. 6:9) Saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana kyautata rayuwar dubban da suke sauraronsa a kowace shekara, kuma hakan na iya kai ga cetonsu. Duk da haka, “ƙaƙa za su ji . . . in ba mai-yin wa’azi?” in ji manzo Bulus. (Rom. 10:14, 15) Hakan zai yi wuya. Me ya sa ba za ka ƙudurta yin iya ƙoƙarinka ka cika hidimarka ba?

20 Wata hanyar kuma da za ka iya taimaka wa mutane su fahimci muhimmancin wannan zamani na ƙarshe da kuma sakamakon shawarar da suka yanke ita ce kyautata yadda ka ke koyarwa. Za a tattauna yadda za ka iya yin hakan a talifi na gaba.

[Hasiya]

a An canja sunayen.

Yaya Za Ka Amsa?

• Wane hakki ne na mutane yake kan Kiristoci?

• Ta yaya za mu jimre da tangarɗa a aikinmu na wa’azi?

• Ta yaya za mu iya cika hidimar da muka karɓa?

[Hoto a shafi na 5]

Muna bukatar gaba gaɗi don mu yi wa’azi a lokacin hamayya

[Hoto a shafi na 7]

Menene za ka iya yi idan kana wa’azi a yankunan da ba a yawan samun mutane a gida?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba