Manufar Talifofin Nazari
Talifofin Nazari na 1-3 SHAFUFFUKA NA 4-17
Waɗannan talifofin nazari guda uku za su ƙarfafa ƙudurinka na ci gaba da saka hannu a hidimar Kirista. Za su tuna maka dalilin da ya sa ka ke bukatar ka kasance da ƙwazo, za su nuna maka yadda za ka kyautata ‘iyawarka ta koyarwa,’ kuma za su ƙarfafa ka ta wajen nuna maka cewa mutane da yawa suna yin na’am ga aikin wa’azi.
Talifofin Nazari na 4, 5 SHAFUFFUKA NA 20-28
Waɗannan talifofin nazari guda biyu sun bayyana dalla-dalla begen da Kiristoci na gaskiya suke da shi. Ko da kana da begen kasancewa da Kristi a sama ko kuwa kana son ka rayu har abada a duniya a ƙarƙashin sarautar Mulki, waɗannan talifofin za su ƙarfafa godiyarka domin alherin Jehobah da kuma hikimarsa marar iyaka.