Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 12/1 pp. 20-24
  • Ka Koyi Halayen Da Za Su Taimake Ka Ka Yi Almajirai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koyi Halayen Da Za Su Taimake Ka Ka Yi Almajirai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ƙaunaci Allah Sosai
  • Ka Nuna Kulawa ga Mutane
  • Ka Nuna Halin Saɗaukar da Kai
  • Ka Kasance Mai Haƙuri Amma Kada ka Ɓata Lokaci
  • Ka Koyi Yadda Ake Koyarwa Sosai
  • Ka Nuna Ƙwazo Sosai a Yin Almajirantarwa
  • ‘Ku Koya Musu Su Kiyaye Duk Iyakar Abin Da Na Umarce Ku’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Koyarwa Da Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • ‘Ku Je . . . Ku Sa A Zama Almajiraina’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Taimaka wa Mutane Su Zama Almajiran Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 12/1 pp. 20-24

Ka Koyi Halayen Da Za Su Taimake Ka Ka Yi Almajirai

“Ku tafi . . . ku almajirtadda dukan al’ummai.”—MATTA 28:19.

1. Waɗanne iyawa da kuma halaye ne ake bukata daga wajen wasu bayin Allah a dā?

A WASU lokatai, bayin Jehobah suna bukatar su zama gwanaye kuma su koyi halayen da za su taimake su su yi nufin Allah. Alal misali, bisa umurnin Allah, Ibrahim da Saratu sun bar birnin Ur mai arziki kuma suna bukatar iyawa da kuma halayen da ake bukata wajen masu zaman tanti. (Ibraniyawa 11:8, 9, 15) Yi wa Isra’ilawa ja-gora zuwa Ƙasar Alkawari ya bukaci Joshuwa ya kasance da gaba gaɗi, tabbaci ga Jehobah, da kuma sanin Dokarsa. (Joshua 1:7-9) Duk da cewa Bezalel da Oholiab ƙwararru ne a dā, ruhun Allah ne ya sa suka ƙware sosai domin su saka hannu kuma su kula da mazaunin da ake ginawa da kuma sauran ayyukan da suka shafi ginin.—Fitowa 31:1-11.

2. Waɗanne tambayoyi da suka shafi aikin almajirantarwa ne za mu tattauna?

2 Bayan wasu ƙarnuka, Yesu Kristi ya ba mabiyansa wannan umurnin: “Ku tafi . . . ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Ba a taɓa ba mutane irin wannan gatan ba a dā. Waɗanne halaye ne ake bukata don a almajirantar da mutane? Ta yaya za mu iya samun su?

Ka Ƙaunaci Allah Sosai

3. Wace dama ce umurnin yin almajirantarwa ta ba mu?

3 Tattaunawa da mutane da kuma rinjayarsu su bauta wa Allah na gaskiya yana bukatar mu ƙaunaci Jehobah sosai. Isra’ilawa za su iya nuna ƙaunarsu ga Allah ta wajen yin biyayya ga dokokinsa da dukan zuciyarsu, yin hadayun da suka dace, da kuma yaba masa da waƙa. (Kubawar Shari’a 10:12, 13; 30:19, 20; Zabura 21:13; 96:1, 2; 138:5) Mu masu almajirantarwa muna bin dokokin Allah, amma muna nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen gaya wa mutane game da shi da kuma nufe-nufensa. Muna bukatar mu yi magana da gaba gaɗi, ta wajen yin amfani da kalmomin da suka dace wajen faɗin yadda muke ji game da begen da Allah ya ba mu.—1 Tassalunikawa 1:5; 1 Bitrus 3:15.

4. Menene ya sa Yesu ya ji daɗin koya wa mutane game da Jehobah?

4 Domin yana ƙaunar Jehobah sosai, Yesu ya ji daɗin gaya wa mutane nufe-nufen Allah, Mulkinsa, da kuma bauta ta gaskiya. (Luka 8:1; Yohanna 4:23, 24, 31) Shi ya sa Yesu ya ce: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” (Yohanna 4:34) Waɗannan kalaman na mai zabura sun shafi Yesu: “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata. Na yi shelar bishara ta adilci a cikin babban taron jama’a; Ga shi, ba zan hana bakin ba, Ya Ubangiji, ka sani.”—Zabura 40:8, 9; Ibraniyawa 10:7-10.

5, 6. Menene ainihin halin da ake bukata a wajen masu almajirantarwa?

5 Domin suna ƙaunar Allah, a wani lokaci, sababbin da suka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki suna tattaunawa game da Jehobah da kuma Mulkinsa da irin tabbacin da ke motsa wasu su bincika Nassosi. (Yohanna 1:41) Ƙaunar Allah ita ce ainihin abin da ke motsa mu mu yi aikin almajirantarwa. Bari mu ci gaba da kasancewa da irin wannan ƙaunar ta wajen karanta da kuma yin bimbinin Kalmarsa a kowane lokaci.—1 Timothawus 4:6, 15; Ru’ya ta Yohanna 2:4.

6 Ƙaunar Jehobah babu shakka ta taimaka wa Yesu Kristi ya zama malami mai ƙwazo. Amma ba wannan kaɗai ba ce dalilin da ya sa ya zama ƙwararren mai wa’azin Mulki ba. To, menene kuma wani halin da ya sa Yesu ya yi nasara wajen almajirantarwa?

Ka Nuna Kulawa ga Mutane

7, 8. Menene ra’ayin Yesu game da mutane?

7 Yesu ya kula da mutane kuma ya nuna cewa ya damu da su. A lokacin da yake sama a matsayinsa na “gwanin mai-aiki” na Allah, ya so abubuwan da suka shafi mutane. (Misalai 8:30, 31) Sa’ad da yake duniya, Yesu ya yi juyayin mutane, kuma ya wartsakar da waɗanda suka zo wurinsa. (Matta 11:28-30) Yesu ya nuna ƙauna da juyayin da Jehobah yake da shi, kuma hakan ya jawo mutane su bauta wa Allah na gaskiya. Mutane iri-iri sun saurari Yesu domin ya nuna cewa ya damu da su da kuma yanayin da suke ciki.—Luka 7:36-50; 18:15-17; 19:1-10.

8 Sa’ad da wani mutumi ya tambaye shi abin da yake bukatar ya yi don ya sami rai na har abada, “Yesu da dubansa ya ƙaunace shi.” (Markus 10:17-21) Mun karanta game da wasu mutanen da Yesu ya koyar da su a Bait’anya cewa: “Yesu dai yana ƙamnar Martha, da yar-uwatta, da Li’azaru.” (Yohanna 11:1, 5) Yesu ya kula da mutane sosai wanda hakan ya sa ya ƙi hutawa a lokacin da ya kamata don ya koyar da su. (Markus 6:30-34) Irin wannan ƙaunar da kula da ya nuna wa mutane ne ya sa Yesu ya fi kowa ƙwarewa wajen jawo mutane zuwa bauta ta gaskiya.

9. Wane irin hali ne Bulus ke da shi a matsayinsa na mai almajirantarwa?

9 Manzo Bulus ma ya kula da mutanen da ya yi wa wa’azi. Alal misali, ya gaya wa waɗanda suka zama Kiristoci a Tassalunika: “Domin muna marmarinku da soyayya, muka ji daɗin ba ku, ba bisharar Allah kaɗai ba, amma har da rayukanmu, gama kun zama abin ƙauna ƙwarai garemu.” A sakamakon ƙaunar da Bulus ya nuna masu, wasu a Tassalunika ‘sun bar gumaka sun juya zuwa ga Allah.’ (1 Tassalunikawa 1:9; 2:8) Idan da gaske ne muna kula da mutane kamar yadda Yesu da Bulus suka yi, mu ma muna iya shaida murnar ganin yadda bishara za ta motsa zuciyar waɗanda “aka ƙadara su ga rai na har abada.”—Ayukan Manzanni 13:48.

Ka Nuna Halin Saɗaukar da Kai

10, 11. Me ya sa muke bukatar halin sadaukar da kai sa’ad da muke almajirantarwa?

10 Ƙwararrun masu almajirantarwa suna nuna halin saɗaukar da kai. Ba su ɗauki tara dukiya a matsayin abin da ya fi muhimmanci ba. Shi ya sa Yesu ya gaya wa almajiransa: “Da ƙyar kamar me masu-dukiya za su shiga cikin mulkin Allah!” Almajiran sun yi mamakin jin haka, amma Yesu ya daɗa: “Yayana, da ƙyar kamar mi masu-dogara ga dukiya za su shiga cikin mulkin Allah! Da mawadaci ya shiga cikin mulkin Allah, ya fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura.” (Markus 10:24, 25) Yesu ya shawarci mabiyansa su yi rayuwa mai sauƙi domin su mai da hankali a kan yin almajirantarwa. (Matta 6:22-24, 33) Me ya sa halin sadaukar da kai yake taimaka mana mu almajirtar?

11 Koyar da dukan abubuwan da Yesu ya umurta yana bukatar ƙoƙari sosai. Mai yin almajirai yana ƙoƙarin ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutumin da ke son gaskiya a kowane mako. Domin su ƙara damarsu na samun masu son gaskiya, wasu masu shelar Mulki sun canja aikinsu daga cikakken lokaci zuwa na ɗan lokaci. Dubban Kiristoci sun koyi wani yare domin su yi wa mutanen da ke wani yare da suke zaune a yankinsu wa’azi. Wasu masu almajirantarwa sun bar gidajensu kuma sun koma wani yankin ko wata ƙasa don su saka hannu sosai a girbin. (Matta 9:37, 38) Dukan waɗannan abubuwan suna bukatar halin sadaukar da kai. Amma, ana bukatar fiye da haka don a zama ƙwararrun masu almajirantarwa.

Ka Kasance Mai Haƙuri Amma Kada ka Ɓata Lokaci

12, 13. Me ya sa haƙuri yake da muhimmanci wajen almajirantarwa?

12 Wani halin da zai taimaka mana mu almajirantar da mutane shi ne haƙuri. Saƙonmu na Kirista yana bukatar ɗaukan mataki nan da nan, amma, a yawancin lokaci yin almajirai yana ɗaukan dogon lokaci kuma yana bukatar haƙuri. (1 Korinthiyawa 7:29) Yesu bai nuna rashin haƙuri da Yaƙub ɗan’uwansa ba. Ko da yake Yaƙub yana sane da ayyukan wa’azin da Yesu yake yi, wani abu ya ɗan riƙe shi daga zama almajirin Yesu. (Yohanna 7:5) Amma, tsakanin lokacin da Kristi ya mutu da kuma Fentakos na shekara ta 33 A.Z., Yaƙub ya zama almajiri, domin Nassosi ya nuna cewa shi da mamarsa, da ’yan’uwansa, da kuma manzanni sun taru don su yi addu’a tare. (Ayukan Manzanni 1:13, 14) Yaƙub ya sami cin gaba sosai a ruhaniya, kuma daga baya, ya sami gata mai yawa a cikin ikilisiyar Kirista.—Ayukan Manzanni 15:13; 1 Korinthiyawa 15:7.

13 Kamar manoma, Kiristoci suna girbe abubuwan da suke girma a hankali, wato, fahimtar Kalmar Allah, ƙaunar Jehobah, da kuma kasancewa da irin halin Kristi. Hakan na bukatar haƙuri. Yaƙub ya rubuta: “Ku yi haƙuri . . . , ’yan’uwa, har zuwan Ubangiji. Duba, mai-gona ya kan jira amfanin ƙasa mai-tamani, yana haƙuri da shi, har ya sami ruwa na fari da na baya. Ku kuma sai ku yi haƙuri; ku tsaida zukatanku; gama zuwan Ubangiji ya kusa.” (Yaƙub 5:7, 8) Yaƙub yana ariritar ’yan’uwa masu bi ne su ‘yi haƙuri har sai Ubangiji ya bayyana.’ Idan almajiran ba su fahimci wani abu ba, Yesu cikin haƙuri ya bayyana ko kuma ya yi amfani da kwatanci. (Matta 13:10-23; Luka 19:11; 21:7; Ayukan Manzanni 1:6-8) A yanzu da Ubangiji ya riga ya bayyana, muna bukatar mu yi haƙuri yayin da muke ƙoƙarin mu almajirantar da mutane. Waɗanda suka zama mabiyan Yesu a zamaninmu suna bukatar a koyar da su cikin haƙuri.—Yohanna 14:9.

14. Ko da yake muna da haƙuri, a matsayin mu na masu almajirantarwa, ta yaya za mu yi amfani da lokaci yadda ya dace?

14 Ko da yake muna da haƙuri, kalmar ba ta motsa zuciyar yawancin mutanen da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su. (Matta 13:18-23) Bayan mun yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka masu, cikin dabara muna iya daina ɓata lokaci da irin waɗannan mutanen kuma mu nemi waɗanda suke ɗaukan gaskiyar Littafi Mai Tsarki da tamani. (Mai-Wa’azi 3:1, 6) Babu shakka, mutanen da suke son gaskiyar Littafi Mai Tsarki wataƙila suna bukatar ƙarin taimako don su canja ra’ayoyinsu, halayensu, da kuma abubuwan da suka fi so a rayuwa. Saboda haka, muna bukatar mu kasance masu haƙuri, kamar yadda Yesu ya yi haƙuri da almajiransa waɗanda kasancewa da hali mai kyau ya yi wa wuya.—Markus 9:33-37; 10:35-45.

Ka Koyi Yadda Ake Koyarwa Sosai

15, 16. Me ya sa koyarwa mai sauƙi da kuma shiri mai kyau suke da muhimmanci sa’ad da muke yin almajirantarwa?

15 Ƙaunar Allah, kula da mutane, halin sadaukar da kai, da kuma haƙuri, suna da muhimmanci idan muna son mu yi nasara a yin almajirantarwa. Muna bukatar mu koyi yadda ake koyarwa sosai, domin hakan zai taimaka mana mu bayyana batutuwa a hanya mai sauƙi. Alal misali, yawancin abubuwan da Babban Malami, Yesu Kristi, ya faɗa sun motsa mutane ne sosai domin suna da sauƙin fahimta. Wataƙila ka tuna da irin waɗannan furcin na Yesu: “Ku ajiye wa kanku dukiya cikin sama.” “Kada ku ba karnuka abin da ke mai-tsarki.” “Hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.” “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.” (Matta 6:20; 7:6; 11:19; 22:21) Hakika, Yesu bai yi gajerun furci ba kaɗai. Koyarwarsa ta fita sarai kuma ya bayyana abubuwa sa’ad da yin hakan ke da muhimmanci. Ta yaya za ka iya yin koyi da salon koyarwa na Yesu?

16 Shiri mai kyau shi ne ainihin abin da zai sa koyarwarmu ta fita sarai kuma ta zama mai sauƙin fahimta. Mai shelan da bai yi shiri ba yakan yi magana mai yawa. Yana iya faɗin ainihin bayanan ta wajen yin magana mai yawa, wato, faɗin dukan abubuwan da ya sani a kan batun. Akasin haka, mai shelan da ya yi shiri sosai yana yin tunani game da mutumin da yake koya wa, yana yin bimbini a kan batun, kuma yana faɗin ainihin abin da ake bukata. (Misalai 15:28; 1 Korinthiyawa 2:1, 2) Yana yin tunanin abubuwan da ɗalibin ya riga ya sani da kuma ainihin bayanan da ya kamata ya nanata a lokacin nazari. Mai shelan yana iya sanin abubuwa masu yawa game da batun, amma faɗin ainihin abubuwan da ake bukata ne kawai zai sa a fahimce shi.

17. Ta yaya za mu iya taimaka wa mutane su yi tunani a kan abin da ke cikin Nassosi?

17 Maimakon ya gaya masu gaskiya kawai, Yesu ya taimaka wa mutane su yi tunani. Alal misali, akwai lokacin da Yesu ya yi wannan tambayar: “Ƙaƙa ka aza a ranka, Siman? daga wurin wa sarakunan duniya su ke karɓan garama ko gandu? daga wurin ’ya’yansu, ko kuwa daga wurin baƙi?” (Matta 17:25) Muna iya jin daɗin bayyana Littafi Mai Tsarki sosai, amma muna bukatar mu nuna kamun kai domin mu ƙyale ɗalibin ya faɗi ra’ayinsa ko kuma ya bayyana abin da aka tattauna a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida. Bai kamata mu cika mutane da tambayoyi ba. Maimakon haka, cikin dabara, yin amfani da misalai masu kyau, da kuma tambayoyi masu sa tunani, muna iya taimaka masu su fahimci bayanan da ke cikin Nassi waɗanda suke cikin littattafanmu da ke bayyana Littafi Mai Tsarki.

18. Menene kasancewa da “sahihiyar koyarwa” ta ƙunsa?

18 Nassosi ya ambata “sahihiyar koyarwa.” (2 Timothawus 4:2; Titus 1:9) Irin wannan koyarwar ta fi taimaka wa mutum ya haddace gaskiya kawai. Muna bukatar mu taimaka wa ɗalibi na Littafi Mai Tsarki ya fahimci bambancin da ke tsakanin gaskiya da kuskure, abin da ke da kyau da marar kyau, hikima da kuma wawanci. (Matta 6:5, 6) Yayin da muke yin haka kuma muke ƙoƙarin mu taimaka wa mutumin ya ƙaunaci Jehobah a zuciyarsa, yana iya ganin dalilin da ya sa ya kamata ya yi wa Allah biyayya.

Ka Nuna Ƙwazo Sosai a Yin Almajirantarwa

19. Ta yaya ne dukan Kiristoci suke saka hannu wajen yin almajirai?

19 Ikilisiyar Kirista ƙungiya ce ta yin almajirantarwa. Sa’ad da mutum ya zama almajiri, ba Mashaidin Jehobah da ya sadu da shi kuma ya taimaka masa ya san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ba ne kaɗai zai yi farin ciki. Idan aka ce mutane su je su nemi yaron da ya ɓace, wataƙila mutum ɗaya ne kawai a cikinsu zai gano yaron. Amma, a lokacin da yaron ya sake saduwa da iyayensa, duka waɗanda suka tafi nemansa ne za su yi farin ciki. (Luka 15:6, 7) Hakazalika, yin almajirantarwa ba aikin mutum ɗaya ba ne kawai. Dukan Kiristoci ne suke fita neman waɗanda za su zama almajiran Yesu. Kuma sa’ad da mutum ya soma halartan taro a Majami’ar Mulki, dukan Kiristocin da ke wurin ne za su taimaka wajen faɗaɗa son da yake yi wa bauta ta gaskiya. (1 Korinthiyawa 14:24, 25) Saboda haka, dukan Kiristoci za su iya yin farin ciki cewa ana samun dubban sababbin almajirai a kowace shekara.

20. Menene kake bukatar ka yi idan kana son ka koya wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki?

20 Yawancin Kiristoci masu aminci za su yi farin cikin koyar da wani game da Jehobah da kuma bauta ta gaskiya. Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcensu, wataƙila ba su sami yin hakan ba. Idan haka ne, ka ci gaba da ƙarfafa ƙaunar da kake yi wa Jehobah, ka kula da mutane, ka ci gaba da sadaukar da kai, ka nuna haƙuri, kuma ka kyautata yadda kake koya wa mutane. Mafi muhimmanci, ka yi addu’a game da muradinka na son koyar da gaskiya. (Mai-Wa’azi 11:1) Ka ƙarfafa da sanin cewa dukan abin da ka yi a hidimar Jehobah yana cika gurbi wajen aikin almajirantarwa da ke ɗaukaka Allah.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Me ya sa almajirantarwa yake gwada ƙaunarmu ga Allah?

• Waɗanne halaye ne ake bukata a wajen masu almajirantarwa?

• Menene “sahihiyar koyarwa” ta ƙunsa?

[Hoto a shafi na 20]

Ta wajen almajirantarwa, Kiristoci suna nuna cewa suna ƙaunar Allah sosai

[Hoto a shafi na 22]

Me ya sa masu almajirantarwa suke bukatar su kula da mutane?

[Hoto a shafi na 23]

Menene wasu halayen da masu almajirantarwa suke bukatar su nuna?

[Hoto a shafi na 24]

Dukan Kiristoci suna farin cikin ganin sakamako mai kyau na almajirantarwa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba