Kana Amfani da Zarafi Ka Sanar da Bangaskiyarka?
“SHIN da akwai tabbatacciyar gaskiya kuwa?” Wannan shine jigon gasar wani rubutu da aka yi a Poland. Umurni da aka bayar don rubutun ya ce: “Ba ma bukatar tabbatacciyar gaskiya. Babu wanda yake bukatarta. Babu ma tabbatacciyar gaskiya.” Agata ’yar shekara 15 ’yar makaranta ce kuma Mashaidiyar Jehobah, ta yi amfani da wannan zarafin domin ta sanar da wasu abin da ta yi imani da shi.
Domin ta yi shiri don rubutun, Agata da farko ta yi addu’a ta nemi ja-gorar Jehobah sai ta fara tara abin da za ta yi rubutu a kai. Ta sami bayani a kan wannan butu a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 1995 na Turanci. Ta yi ƙaulin tambayar da Bilatus Ba-Bunti ya yi wa Yesu: “Menene gaskiya?” (Yohanna 18:38) Wannan tambaya da ta yi ƙaulinsa ya nuna wani irin hali na rashin yarda da gaskiya, kamar dai yana cewa ne: ‘Gaskiya? Menene kuma wannan? Babu wani abu kamar wannan!’ Agata ta rubuta: “Tambayar da Bilatus ya yi, ya tuna mini da umurnin rubuta wannan rubutu.”
Sai ta tattauna yadda ra’ayin cewa abu yana iya kasance gaskiya ga wani mutum kuma ya kasance ba gaskiya ba ga wani kuma dukan su su kasance “daidai.”Ta yi tambaya kamar haka, “Wanene a tsakaninmu zai yarda ya shiga jirgin sama idan bai yi imani ba da cewa dokar da take ta da jirgin sama gaskiya ce?” Sai ta ambata Littafi Mai Tsarki, ta ce: “Dogara ga Littafi Mai Tsarki yana da jijiya cikin abin da za a iya ba da tabbaci da shi.” Ta yi begen cewa waɗanda suke nemen tabbatacciyar gaskiya za su kasance suna da haƙuri su same ta.
Agata ta sami difiloma na musamman kuma ta sami zarafin ba da gabatarwanta a gaban dukan aji. ’Yan ajinta masu yawa suka yarda ta yi nazarin Littifi Mai Tsarki da su. Agata ta yi godiya da ta yi amfani da zarafi da ta samu ta sanar da abin da ta yi imani da shi ga wasu. Hakika, kasancewa a faɗake ka yi amfani da zarafi ka yi magana bisa bangaskiyarka na ba da amfani. Wane zarafi ne za ka yi amfani da shi?