“Ubanku Mai-jinƙai Ne”
“Ku zama masu-jinƙai, kamar yadda Ubanku mai-jinƙai ne.”—LUKA 6:36.
1, 2. Ta yaya maganar da Yesu ya yi wa marubuta da Farisawa da kuma mabiyansa suka nuna cewa jin ƙai hali ne mai kyau?
DOKAR da aka ba da ta wurin Musa tana ɗauke da farillai da mizanai 600. Ko da yake ana bukatar a cika farillan da ke cikin Dokar Musa, nuna jin ƙai ma yana da muhimmanci. Ka yi la’akari da abin da Yesu ya gaya wa Farisawa da ba sa nuna wa mutane jin ƙai. Sau biyu ya tsauta musu, kuma ya nuna cewa Allah ya ce: “Ni, jinƙai ni ke so, ba hadaya ba.” (Matta 9:10-13; 12:1-7; Hosea 6:6) Kusan ƙarshen hidimarsa, Yesu ya ce: “Kaitonku, ku marubuta da Farisawa, masu-riya! gama kuna karɓan ushira ga ɗanɗoya da anise da algaru, amma kun ƙyale matsaloli mafiya girma na Attaurat, shari’a, da jinƙai da bangaskiya.”—Matta 23:23.
2 Babu shakka, a wajen Yesu jin ƙai hali ne mai muhimmanci. Ya gaya wa mabiyansa: “Ku zama masu-jinƙai, kamar yadda Ubanku mai-jinƙai ne.” (Luka 6:36) Amma, don mu “zama fa masu-koyi da Allah” a kan wannan batun jin ƙai, muna bukatar mu san ma’anar jin ƙai na gaskiya. (Afisawa 5:1) Buga da ƙari, fahimtar amfanin jin ƙai zai motsa mu mu nuna wannan halin sosai a rayuwarmu.
Jin Tausayin Mabukata
3. Me ya sa ya kamata mu dogara ga Jehobah don mu koyi ainihin jin ƙai?
3 Mai zabura ya rera waƙa: “Ubangiji mai-alheri ne, cike da tausai kuma; Mai-jinkirin fushi, mai-yawan jinƙai kuma. Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane; Jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.” (Zabura 145:8, 9) Jehobah ne “Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Korinthiyawa 1:3) Ana nuna jin ƙai ta wajen yi wa wani juyayi. Wannan sashe ne mai muhimmanci na halin Allah. Misalinsa da umurnin da ya ba mu za su iya koya mana ainihin ma’anar jin ƙai.
4. Menene Ishaya 49:15 ta koya mana game da jin ƙai?
4 Kamar yadda yake rubuce a Ishaya 49:15, Jehobah ya ce: “Ya yiwu mace ta manta da ɗanta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin ɗan cikinta ba?” Ana amfani da kalmomin Ibrananci da ke da nasaba da wanda aka fassara “juyayi” cikin jituwa da jin ƙai da ke Zabura 145:8, 9, da aka ambata a sama. An kwatanta sosuwar zuciya da ke motsa Jehobah ya kasance mai jin ƙai da yadda mace mai shayarwa take ji game da ɗanta. Wataƙila jaririn yana jin yunwa ko kuma yana da wasu bukatu. Juyayi ko tausayi da take ji zai motsa mamar ta biya bukatun jaririnta. Jehobah yana jin hakan game da waɗanda yake yi wa jin ƙai.
5. Ta yaya Jehobah ya nuna wa Isra’ila cewa shi “mawadaci ne cikin jinƙai”?
5 Yana da kyau a ji tausayin mutane amma ya fi kyau a aikata don amfanin mabukata. Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya aikata sa’ad da masu bauta masa suke bauta a Masar kusan shekaru 3,500 da suka shige. Ya gaya wa Musa: “Hakika na ga ƙuncin mutanena waɗanda ke cikin Masar, na kuwa ji kukarsu sabada shugabanninsu na gandu; gama na san baƙinzuciyarsu; na kuwa sabko domin in cece su daga hannun Masarawa, in fishe su daga wa can ƙasa, in kai su cikin ƙasa mai-kyau mai-faɗi, ƙasa mai-zubasda madara da zuma.” (Fitowa 3:7, 8) Kusan shekaru 500 bayan da aka ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar, Jehobah ya tuna musu: “Na fito da Isra’ila daga cikin Masar, na tsame ku daga hannun Masarawa, daga hannun dukan mulkokin da suka wulakance ku kuma.” (1 Samuila 10:18) Sau da yawa Isra’ilawa sun faɗa cikin matsala domin sun bijire wa mizanan Allah na adalci. Duk da haka, Jehobah ya ji tausayinsu kuma ya cece su a kai a kai. (Alƙalawa 2:11-16; 2 Labarbaru 36:15) Wannan ya kwatanta yadda Allah mai ƙauna yake kula da mabukata, waɗanda suke cikin haɗari, ko kuwa cikin matsala. Jehobah “mawadaci ne cikin jinƙai.”—Afisawa 2:4.
6. Ta yaya ne Yesu Kristi ya yi koyi da Ubansa wajen nuna jin ƙai?
6 Yesu Kristi ya yi koyi da Ubansa sosai wajen nuna jin ƙai. Menene Yesu ya yi sa’ad da makafi biyu suka roƙe shi, suna cewa: “Ubangiji, ka yi mana jinƙai, kai dan Dawuda”? Suna roƙon Yesu ya buɗe idanunsu ta hanyar mu’ujiza. Yesu ya yi mu’ujizar saboda ya ji tausayi ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yesu . . . da yana jin juyayi, ya taɓa idanunsu: nan da nan suka sami ganin gari.” (Matta 20:30-34) Juyayi ne ya sa Yesu ya yi mu’ujizai da yawa don ya warkar da makafi, masu aljanu, masu kuturta, kuma ya sauƙaƙa wa iyaye masu yara da suke ciwo.—Matta 9:27; 15:22; 17:15; Markus 5:18, 19; Luka 17:12, 13.
7. Menene misalan Jehobah Allah da Ɗansa suka koya mana game da jin ƙai?
7 Misalan Jehobah Allah da Yesu Kristi sun nuna cewa jin ƙai yana da fannoni biyu: yin juyayi ko jin tausayin mabukata da kuma yin abin da zai kawo musu sauƙi. Don mutum ya zama mai jin ƙai ya kamata ya kasance mai nuna dukan waɗannan halayen. A cikin Nassosi, sau da yawa nuna jin ƙai na nufin yi wa mabukata alheri. To, ta yaya ake nuna jin ƙai a batun shari’a? Ya ƙunshi ƙin yin abin da ya kamata ne, kamar ƙin horanta mutum?
Nuna Jin Ƙai ga Masu Zunubi
8, 9. Menene jin ƙai da aka nuna wa Dauda bayan ya yi zunubi da Bath-sheba ya ƙunsa?
8 Ka yi la’akari da abin da ya faru bayan da annabi Natan ya je wajen Sarki Dauda na Isra’ila ta dā game da zina da ya yi da Bath-sheba. Dauda ya tuba kuma ya yi addu’a: “Ka yi mani jinƙai, ya Allah, bisa ga rahamarka: Bisa ga yawan jiyejiyenƙanka ka shafe laifofina. Ka wanke ni sarai daga kuskurena, ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina: zunubina yana gabana tuttur. Kai kaɗai na yi maka zunubi, Na yi abin da ke mugu a gabanka.”—Zabura 51:1-4.
9 Dauda ya yi nadama sosai. Jehobah ya gafarta masa zunubinsa kuma ya yi haƙuri bai yi wa Dauda da Bath-sheba horo mai tsanani ba. Bisa Dokar Musa, ya kamata a kashe Dauda da Bath-sheba. (Kubawar Shari’a 22:22) Ko da yake ba su tsira daga dukan sakamakon zunubinsu ba, ba a kashe su ba. (2 Samuila 12:13) Jin ƙai na Allah ya ƙunshi gafarta zunubai. Duk da haka, yana ba da horo da ya dace.
10. Ko da Jehobah mai jin ƙai ne wajen zartar da hukunci, me ya sa ba za mu yi abin da muka ga dama ba?
10 Tun da yake “zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu] kuma “hakkin zunubi mutuwa ne” ya dace dukan ’yan adam su mutu. (Romawa 5:12; 6:23) Ya kamata mu yi godiya cewa Jehobah yana nuna jin ƙai sa’ad da yake zartar da hukunci! Amma, ya kamata mu mai da hankali kada mu riƙa yin abin da muka ga dama domin Allah mai jin ƙai ne. Kubawar Shari’a 32:4 ta ce: “Dukan tafarkunsa [Jehobah] shari’a ne.” Idan yana nuna jin ƙai, Allah ba ya ƙyale cikakken mizanansa na shari’a.
11. Ta yaya Jehobah ya nuna adalci wajen bi da Dauda don zunubinsa da Bath-sheba?
11 Kafin a sauƙaƙa hukuncin mutuwa a kan Dauda da Bath-sheba, za a gafarta musu zunubansu. Ba a ba alƙalai na Isra’ilawa ikon yin hakan ba. Idan aka bar su su yi wannan shari’a, da yake ba su da wani mataki dabam, za su ce a kashe masu laifin. Haka ne doka ta ce a yi. Amma domin alkawarinsa da Dauda, Jehobah yana son ya gani ko akwai dalilin gafarta wa Dauda zunubinsa. (2 Samuila 7:12-16) Saboda haka, Jehobah Allah, “mai-shari’an dukan duniya” wanda yake “auna zukata,” ya zaɓi ya yi shari’ar da kansa. (Farawa 18:25; 1 Labarbaru 29:17) Allah ya san zuciyar Dauda, ya auna tabbacin tubansa, kuma ya gafarta masa.
12. Ta yaya ne mutane masu zunubi za su iya samun jin ƙan Allah?
12 Jin ƙai da Jehobah ya nuna mana ta wajen sa ya yiwu a sake mu daga hukuncin zunubi da muka gada ya jitu da adalcinsa. Domin ya gafarta zunubi ba tare da taka mizanansa na adalci ba, Jehobah ya yi tanadin Ɗansa Yesu Kristi, ya yi hadayar fansa, wannan shi ne jin ƙai mafi girma da aka taɓa yi. (Matta 20:28; Romawa 6:22, 23) Don mu amfana daga jin ƙan Allah wanda zai iya cetonmu daga hukuncin zunubi da muka gada, dole ne mu “bada gaskiya ga Ɗan.”—Yohanna 3:16, 36.
Allah Mai Jin Ƙai da Hukunci
13, 14. Jin ƙan Allah yana sauƙaƙa hukuncinsa ne? Ka ba da bayani.
13 Ko da yake Jehobah ba ya taka mizanansa na shari’a wajen nuna jin ƙai, hakan yana shafan hukuncinsa ne? Jin ƙai na rage hukuncin Allah ne? A’a.
14 Ta wurin annabi Hosea, Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa: “Zan ɗaura alkawarin aure da ke har abada; i, cikin adalci, da cikin shari’a, da rahama, da jinƙai, zan yi alkawari da ke.” (Hosea 2:19) Waɗannan kalmomi sun nuna sarai cewa jin ƙai da Jehobah yake nunawa ya jitu da sauran halayensa har da adalci. Jehobah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, . . . yana gafarta laifi da saɓo da zunubi: ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.” (Fitowa 34:6, 7) Jehobah Allah ne mai jin ƙai da adalci. Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi: “Fa ne shi, aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne.” (Kubawar Shari’a 32:4) Adalcin Allah cikakke ne, kamar jin ƙansa. Ba wanda ya fi wani, ba wanda ke bukatar taimakon wani don ya sauƙaƙa sakamakonsa. Maimakon haka, dukan halaye na aiki cikin jituwa da juna.
15, 16. (a) Menene ya nuna cewa hukuncin Allah ba mai azabtarwa ba ne? (b) Sa’ad da Jehobah zai zartar da hukuncinsa a kan wannan mugun zamani, wane tabbaci ne masu bauta masa za su kasance da shi?
15 Hukuncin Jehobah ba mai azabtarwa ba ne. Hukunci yana da ma’ana ta doka, kuma koyaushe ana bukatar a ba da horo da ya dace ga waɗanda suka yi laifi. Amma, hukuncin Allah na iya sa waɗanda suka cancanta su sami ceto. Alal misali, sa’ad da aka halaka miyagu da ke cikin biranen Saduma da Gwamrata, uban iyali Lutu da ’ya’yansa mata biyu sun tsira.—Farawa 19:12-26.
16 Muna da tabbacin cewa sa’ad da Jehobah zai zartar da hukuncinsa a kan wannan zamanin, “taro mai-girma” na masu bauta ta gaskiya, waɗanda “suka wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon kuma,” za su tsira. Saboda haka, za su “fito daga cikin babban tsananin.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9-14.
Me Ya Sa Ya Kamata Mu Zama Masu Jin Ƙai?
17. Menene dalili na musamman na zama masu jin ƙai?
17 Misalan Jehobah da Yesu Kristi sun koya mana jin ƙai na gaskiya. Da yake muna da dalili na musamman na zama masu jin ƙai, Misalai 19:17 ta ce: “Mai-jin tausayin fakirai yana bada rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka yi koyi da shi da kuma Ɗansa ta wurin nuna jin ƙai sa’ad da muke sha’ani da juna. (1 Korinthiyawa 11:1) An ƙarfafa mutane su zama masu jin ƙai, don idan muna nuna wa mutane jin ƙai su ma za su yi mana jin ƙai.—Luka 6:38.
18. Me ya sa ya kamata mu yi ƙoƙari mu zama masu jin ƙai?
18 Jin ƙai ya ƙunshi halaye da yawa masu kyau. Ya haɗa da alheri, ƙauna, da nagarta. Juyayi ko kuma tausayi ne ke motsa mu mu yi jin ƙai. Ko da cewa jin ƙai na Allah ba ya hana shi hukunci, Jehobah na jinkirin fushi kuma cikin haƙuri yana ba masu aika laifi isashen lokaci su tuba. (2 Bitrus 3:9, 10) Da haka jin ƙai ya ƙunshi yin haƙuri da tsawon jimrewa. Da yake ya ƙunshi halaye da yawa masu kyau, har da fannoni dabam dabam na ɗiyar ruhu na Allah, jin ƙai ya zama zarafi na nuna waɗannan halaye. (Galatiyawa 5:22, 23) Yana da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu zama masu jin ƙai!
“Masu-Albarka ne Masu-Jinƙai”
19, 20. A wace hanya ce jin ƙai yake yin nasara bisa shari’a?
19 Almajiri Yaƙub ya gaya mana abin da ya sa za mu sa jin ƙai ya zama hali mai muhimmanci a rayuwarmu. Ya rubuta: “Jinƙai kuma yana fahariya bisa shari’a.” (Yaƙub 2:13b) Yaƙub yana maganar jin ƙai da mai bauta wa Jehobah yake nuna wa mutane. Jin ƙai yana nasara bisa shari’a domin idan lokaci ya zo da mutum zai “kawo lissafin kansa ga Allah,” Jehobah yana la’akari da yadda mutumin ya nuna jin ƙai ga wasu kuma ya gafarta masa domin hadayar fansa na Ɗansa. (Romawa 14:12) Babu shakka, dalili ɗaya da ya sa aka nuna wa Dauda jin ƙai don zunubinsa da Bath-sheba shi ne cewa yana nuna wa mutane jin ƙai. (1 Samuila 24:4-7) A wani ɓangare kuma, “shari’a mara-jin ƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai ba.” (Yaƙub 2:13a) Shi ya sa “marasa-jinƙai” suke cikin waɗanda Allah yake gani “sun isa mutuwa”!—Romawa 1:31, 32.
20 A cikin Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-jinƙai: gama su za su sami jinƙai.” (Matta 5:7) Waɗannan kalmomi sun nuna cewa ya kamata waɗanda suke son Allah ya nuna musu jin ƙai su ma su zama masu jin ƙai! Talifi na gaba zai nuna yadda za mu nuna jin ƙai a rayuwarmu ta yau da kullum.
Menene Ka Koya?
• Menene jin ƙai?
• A waɗanne hanyoyi ne ake nuna jin ƙai?
• A wace hanya ce Jehobah Allah mai jin ƙai da shari’a ne?
• Me ya sa ya kamata mu zama masu jin ƙai?
[Hoto a shafi na 3]
Yadda Jehobah yake ji game da mabukata yana kamar yadda uwa take ji game da jaririnta
[Hoto a shafi na 5]
Menene muka koya game da jin ƙai daga mu’ujizan Yesu?
[Hoto a shafi na 6]
Jehobah ya taka shari’arsa ta wajen nuna wa Dauda jin ƙai ne?
[Hoto a shafi na 7]
Jin ƙan Allah game da masu zunubi yana cikin jituwa da shari’arsa