Tsofaffi Albarka Ne Ga Matasa
“I, har lokacinda na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah; Sai dai na bayana zira’akka ga tsara mai-zuwa, Ƙarfinka kuma ga dukan wanda ya ke zuwa.”—ZABURA 71:18.
1, 2. Me ya kamata bayin Allah tsofaffi su fahimta, kuma menene za mu tattauna yanzu?
WANI dattijo a Afirka ta Yamma ya ziyarci wani ɗan’uwa tsoho shafaffe kuma ya tambaye shi, “Yaya kake?” Ɗan’uwan ya amsa, “Zan iya gudu, zan iya tsalle,” yana ƙoƙarin ya kwatanta abubuwa da yake faɗa. Ya daɗa, “amma ba zan iya tashiwa ba.” Dattijon ya fahimci abin da yake nufi. Yana nufin cewa ‘Zan yi iyaka ƙoƙarina, amma ba zan yi abin da ya fi ƙarfina ba.’ Dattijon da ya yi wannan ziyara yana shekararsa na tamanin yanzu, kuma yana tunawa da amincin wannan ɗan’uwan da kuma yadda yake da ban dariya.
2 Halaye na ibada da tsofaffi suke nunawa zai iya motsa mutane sosai. Hakika, shekarar rayuwa kaɗai ba ta sa mutum ya kasance da hikima da kuma halaye irin na Kristi. (Mai-Wa’azi 4:13) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Furfura rawanin daraja ce, idan an iske ta cikin hanyar adalci.” (Misalai 16:31) Idan kai tsoho ne, ka fahimci cewa kalmominka da ayyukanka suna iya shafan wasu a hanya mai kyau? Ka yi la’akari da wasu misalai na Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda tsofaffi suka kasance albarka ga matasa.
Bangaskiya da Ke da Sakamako na Dindindin
3. Ta yaya amincin Nuhu ya shafi dukan waɗanda suke rayuwa yanzu?
3 Bangaskiyar Nuhu da amincinsa sun kawo amfani da har yau muna gani. Nuhu ya kusan shekaru 600 sa’ad da ya gina jirgi, ya tattara dabbobi, kuma ya yi wa maƙwabtansa wa’azi. (Farawa 7:6; 2 Bitrus 2:5) Domin yana jin tsoron Allah, Nuhu tare da iyalinsa sun tsira wa babban Rigyawa kuma ya zama kakan dukan mutanen da suke rayuwa a duniya a yau. Gaskiya ne cewa Nuhu ya rayu a lokacin da mutane suke daɗewa sosai kafin su mutu. Duk da haka, ko a tsufansa, Nuhu ya kasance da aminci, kuma wannan ya kawo albarka mai yawa. Ta yaya?
4. Ta yaya amincin Nuhu yake amfanar da bayin Allah a yau?
4 Shekarar Nuhu ta kusan 800 sa’ad da Nimrod ya soma gina Hasumiya na Babel yana ƙin bin umurnin Jehobah na “mamaye duniya.” (Farawa 9:1; 11:1-9) Amma Nuhu bai sa hannu a tawayen Nimrod ba. Da haka, wataƙila ba a canja yarensa ba sa’ad da aka rikiɗar da yaren ’yan tawayen. Ya kamata bayin Allah yara da manya su yi koyi da bangaskiyar Nuhu da amincinsa sa’ad da ya tsufa da kuma dukan rayuwarsa.—Ibraniyawa 11:7.
Suna da Tasiri a Cikin Iyali
5, 6. (a) Menene Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya yi sa’ad da yake ɗan shekara 75? (b) Ta yaya Ibrahim ya aikata ga umurnin Allah?
5 Za iya ganin tasirin tsofaffi a bangaskiyar waɗanda ke cikin iyalinsu ta rayuwar ubanni bayan Nuhu. Ibrahim yana misalin shekara 75 sa’ad da Allah ya ce masa: “Ka fita daga ƙasarka, daga danginka kuma, da gidan ubanka, zuwa ƙasa da zan nuna maka: daga wurinka zan yi al’umma mai-girma, zan albarkace ka kuma.”—Farawa 12:1, 2.
6 A ce ka bar gidanka, abokanka, ƙasarka, da kwanciyar rai na danginka ka tafi ƙasar da ba ka sani ba. Abin da aka gaya wa Ibrahim ya yi ke nan. “Ya tafi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa” kuma duk rayuwarsa, ya zauna a cikin tanti kamar baƙo da mai ƙaura a ƙasar Kan’ana. (Farawa 12:4; Ibraniyawa 11:8, 9) Ko da Jehobah ya ce zai zama “al’umma mai-girma” Ibrahim ya mutu da daɗewa kafin zuriyarsa ta yi yawa. Matarsa, Saratu ta haifa masa ɗa tilo, Ishaƙu, bayan Ibrahim ya yi shekara 25 a ƙasar alkawari. (Farawa 21:2, 5) Duk da haka, Ibrahim bai kasala ba kuma ya koma birnin da ya fito. Lallai Ibrahim misali ne mai kyau na bangaskiya da jimiri!
7. Ta yaya jimirin Ibrahim ya shafi ɗansa Ishaƙu, menene sakamakon wannan ga ’yan adam?
7 Jimirin Ibrahim ya shafi ɗansa Ishaƙu sosai, wanda ya ba da dukan rayuwarsa na shekara 180 ya yi baƙunci a ƙasar Kan’ana. Ishaƙu ya jimre ne saboda bangaskiyar da yake da ita a alkawuran Allah, bangaskiya da iyayensa tsofaffi suka koya masa kuma kalmar Jehobah ta ƙarfafa bangaskiyar nan. (Farawa 26:2-5) Amincin Ishaƙu ya taimaka sosai wajen cika alkawarin Jehobah cewa ‘zuriya’ da za ta yi wa dukan ’yan adam albarka za ta zo ta wurin iyalin Ibrahim. Shekaru da yawa bayan haka, Yesu Kristi sashe na musamman na wannan zuriya, ya sa ya yiwu dukan waɗanda suka ba da gaskiya a gare shi su sulhunta da Allah kuma su more rai madawwami.—Galatiyawa 3:16; Yohanna 3:16.
8. Ta yaya Yakubu ya nuna bangaskiya mai ƙarfi, kuma da wane sakamako?
8 Ishaƙu kuma ya taimaki ɗansa Yakubu ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi da ya kiyaye shi har tsufansa. Yakubu yana shekara 97 sa’ad da ya yi kokawa da mala’ika dukan dare don ya samu albarka. (Farawa 32:24-28) Kafin ya mutu a shekararsa na 147, Yakubu ya yi ƙoƙari ya albarkaci kowane cikin ’ya’yansa 12. (Farawa 47:28) Kalmomin annabci da ya furta da ke rubuce a Farawa 49:1-28, sun zama gaskiya kuma suna cikawa har yanzu.
9. Menene za a iya faɗa game da tasiri da tsofaffi da suka manyanta a ruhaniya suke da shi a iyalinsu?
9 Hakika, bayin Allah tsofaffi suna da tasiri mai kyau ga waɗanda suke cikin iyalinsu. Umurni na Nassi da shawara mai kyau da kuma misali na jimiri za su taimaki matashi ya girma ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi. (Misalai 22:6) Bai kamata tsofaffi su ga ba su da amfani a iyalinsu ba.
Suna da Tasiri ga ’Yan’uwa Masu Bi
10. Wane umurni ne Yusufu ya ba da “a kan zancen ƙasussuwansa,” kuma menene sakamakon?
10 Tsofaffi suna iya zama tasiri mai kyau ga ’yan’uwa masu bi. Yusufu ɗan Yakubu ya aikata cikin bangaskiya sa’ad da ya tsufa kuma hakan ya shafi masu bauta na gaskiya da yawa da suka rayu bayansa. Yana ɗan shekara 110 sa’ad da ya “bada wasici kuma a kan zancen ƙasussuwansa” wato, cewa Isra’ilawa su ɗauki ƙasusuwansa sa’ad da suke barin Masar. (Ibraniyawa 11:22; Farawa 50:25) Wannan umurnin ya nuna cewa Isra’ila tana da bege a lokacin bautarsu bayan mutuwar Yusufu, kuma wannan ya ba da tabbaci cewa za su sami ceto.
11. Wane tasiri ne Musa tsoho yake da shi ga Joshua?
11 Musa yana cikin waɗanda bangaskiyar Yusufu ta ƙarfafa. Sa’ad da Musa yake ɗan shekara 80, ya samu gatar ɗaukan ƙasusuwan Yusufu daga ƙasar Masar. (Fitowa 13:19) A lokacin ya sadu da Joshua, matashi. Joshua ya yi wa Musa hidima ta shekara 40. (Litafin Lissafi 11:28) Ya raka Musa zuwa Dutsen Sinai kuma ya je ya tari Musa sa’ad da ya sauko daga dutsen da alluna na Shaida. (Fitowa 24:12-18; 32:15-17) Babu shakka, Musa tsoho ya ba Joshua shawara da hikima mai kyau!
12. Ta yaya Joshua ya zama tasiri mai kyau ga al’ummar Isra’ila sa’ad da yake da rai?
12 Joshua kuma ya ƙarfafa al’ummar Isra’ila sa’ad da yake da rai. Alƙalawa 2:7 ta gaya mana: “Jama’ar suka bauta ma Ubangiji dukan kwanakin Joshua, da kuma dukan kwanakin datiɓai da suka wanzu bayan zamanin Joshua, waɗanda sun ga manyan ayukan Ubangiji da ya aika domin Isra’ila.” Amma, bayan mutuwar Joshua da kuma dattawa, aka soma tantama na shekara 300 tsakanin bauta ta gaskiya da ta ƙarya, har kwanakin annabi Sama’ila.
Sama’ila ya “Aika Adalci”
13. Menene Sama’ila ya yi don ya “aika adalci”?
13 Littafi Mai Tsarki bai faɗi shekarun Sama’ila ba sa’ad da ya mutu, amma aukuwa na littafin Sama’ila na Farko ya ɗauki misalin shekaru 102 kuma Sama’ila ya ga yawancinsu. Ibraniyawa 11:32, 33 sun ce alƙalai da annabawa sun “aika adalci.” Hakika, Sama’ila ya sa wasu cikin tsaransa su guji laifi ko su daina yin hakan. (1 Samuila 7:2-4) Ta yaya? Ya kasance da aminci ga Jehobah a dukan rayuwarsa. (1 Samuila 12:2-5) Bai ji tsoron yi wa sarki gargaɗi mai tsanani ba. (1 Samuila 15:16-29) Ƙari ga haka, Sama’ila da ya ‘tsufa ya yi furfura’ ya nuna misali mai kyau wajen yin addu’a game da wasu. Ya ce ‘kada ya yi ma Ubangiji zunubi, ya dena yin addu’a’ game da ’yan’uwansa Isra’ilawa.—1 Samuila 12:2, 23.
14, 15. Ta yaya tsofaffi a yau za su yi koyi da Sama’ila a batun addu’a?
14 Dukan waɗannan sun nuna hanya mai kyau da tsofaffi za su kasance tasiri mai kyau ga bayin Jehobah. Ko da rashin lafiya ko kuma wasu yanayi suna iya jawo kasawa, tsofaffi za su iya yin addu’a game da wasu. Tsofaffi addu’o’inku na amfanar ikilisiya. Domin bangaskiyarku ga jinin da Kristi ya zubar, kuna more tagomashi a gaban Jehobah, kuma domin tarihin jimirinku an ‘gwada’ bangaskiyarku. (Yaƙub 1:3; 1 Bitrus 1:7) Kada ku manta: “Addu’ar mai-adalci tana da iko dayawa cikin aikinta.”—Yaƙub 5:16.
15 Ana bukatar addu’arku wajen tallafa wa aikin Mulkin Jehobah. Wasu cikin ’yan’uwanmu suna cikin kurkuku domin tsaka tsakinsu na Kirista. Wasu suna shan wahala domin tsarar bala’i, yaƙe-yaƙe, da yaƙin basasa. Wasu kuma cikin ikilisiyarmu suna fuskantar gwaji ko tsanantawa. (Matta 10:35, 36) Waɗanda suke shugabanci a aikin wa’azi da kuma kula da ikilisiyoyi suna bukatar addu’o’inku dominsu a kai a kai. (Afisawa 6:18, 19; Kolossiyawa 4:2, 3) Yana da kyau ku ambata ’yan’uwanku a cikin addu’arku, yadda Abafras ya yi!—Kolossiyawa 4:12.
Koyar da Tsara ta Gaba
16, 17. Menene aka annabta a Zabura 71:18, kuma ta yaya wannan ya faru?
16 Yin tarayya da masu aminci na “ƙaramin garke,” da za su je sama ya sa “waɗansu tumaki” da suke da begen zama a duniya har abada su sami koyarwa mai muhimmanci. (Luka 12:32; Yohanna 10:16) An annabta wannan a Zabura 71:18, wadda ta ce: “Har lokacinda na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah; Sai dai na bayana zira’akka ga tsara mai-zuwa, Ƙarfinka kuma ga dukan wanda ya ke zuwa.” Waɗanda aka shafa da ruhu suna ɗokin su koyar da abokansu waɗansu tumaki don ƙarin hakki kafin su bar su kuma a ɗaukaka su tare da Yesu Kristi.
17 Bisa ƙa’ida, za a iya yin amfani da abin da Zabura 71:18 ta ce game da koyar da “dukan wanda ya ke zuwa” ga waɗansu tumaki, da shafaffu na Allah suka koyar da su. Jehobah ya ɗanka wa tsofaffi gatar ba da shaida game da shi ga waɗanda yanzu suna bin bauta ta gaskiya. (Joel 1:2, 3) An albarkaci waɗansu tumaki don abin da suka koya daga shafaffu kuma dole ne har ila su koyar da waɗanda suke son su bauta wa Jehobah.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10.
18, 19. (a) Wace koyarwa ce mai tamani bayin Jehobah da suka tsufa suke yi? (b) Wane tabbaci ya kamata tsofaffi Kiristoci su kasance da shi?
18 Bayin Jehobah da suka tsufa, duk da shafaffu da waɗansu tumaki tabbaci ne na aukuwa na tarihi mai muhimmanci. Wasu da har ila suke da rai suna nan sa’ad da aka nuna bidiyon “Photo-Drama of Creation (Hoton Wasan Kwaikwayo na Halitta).” Wasu sun san ’yan’uwa maza da suke shugabanci da aka sa su cikin kurkuku a shekara ta 1918. Wasu sun watsa labarai a tashan rediyo na Watchtower da ake kira WBBR. Da yawa a cikinsu sun tuna batun da ya shafi ’yancin addini na Shaidun Jehobah da aka kai babban kotu. Wasu sun yi tsayin daka don bauta ta gaskiya yayin da suke zama a ƙarƙashin mulkin kama karya. Hakika, tsofaffi suna iya ba da labarin yadda aka ci gaba da bayyana fahimi na gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu amfana daga irin wannan labarin.—Kubawar Shari’a 32:7.
19 An aririce Kiristoci tsofaffi su zama misalai masu kyau ga matasa. (Titus 2:2-4) Wataƙila a yanzu ba ku ga yadda jimirinku, da addu’arku da gargaɗinku suke shafan wasu ba. Mai yiwuwa, Nuhu, Ibrahim, Yusufu, Musa, da kuma wasu ba su san yadda amincinsu zai shafi tsara ta gaba ba. Duk da haka, tarihi na bangaskiya da aminci da suka bar mana yana da muhimmanci; shi ya sa misalinku zai iya kasance hakan ga matasa.
20. Wace albarka ce ke jiran waɗanda suka kasance da bege har ƙarshe?
20 Ko an cece ka a lokacin “ƙunci mai-girma” ko kuma an dawo da kai daga tashin matattu, zai zama abin farin ciki ka ga “hakikanin rai”! (Matta 24:21; 1 Timothawus 6:19) Ka yi tunanin lokacin Sarautar Shekara Dubu na Kristi sa’ad da Jehobah zai canja sakamakon tsufa. Maimakon fuskantar sukukucewar jikinmu, za mu tashi kowace rana da kyautatawar jiki, za mu ƙara samun ƙarfi, idanu mafi kyau, za mu ji magana da kyau, da jiki mafi kyau! (Ayuba 33:25; Ishaya 35:5, 6) Waɗanda aka albarkace su su zauna a sabuwar duniya ta Allah za su ci gaba da zama matasa idan aka gwada da rayuwa ta har abada da za su samu. (Ishaya 65:22) Saboda haka, bari dukanmu mu kasance da bege har ƙarshe kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai cika dukan abin da ya yi alkawarinsa kuma abin da zai yi zai wuce dukan abubuwa da muke tsammani.—Zabura 37:4; 145:16.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya amincin Nuhu da ya tsufa ya kawo albarka ga dukan ’yan adam?
• Ta yaya bangaskiyar ubanni ya shafi tsararsu?
• A tsufansu, ta yaya Yusufu, Musa, Joshua, da kuma Sama’ila suka ƙarfafa ’yan’uwa masu bi?
• Menene tsofaffi suke bar wa ’yan’uwa?
[Hoto a shafi na 26]
Jimirin Ibrahim ya shafi Ishaƙu sosai
[Hoto a shafi na 28]
Gargaɗi mai kyau na Musa ya ƙarfafa Joshua
[Hoto a shafi na 29]
Addu’o’inku domin wasu zai amfane su sosai
[Hoto a shafi na 30]
Matasa suna amfana ta wajen saurarar tsofaffi masu aminci