Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 6/1 p. 3
  • Za a Iya Kawar da Mugunta Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za a Iya Kawar da Mugunta Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Nagarta Za Ta Yi Nasara Bisa Mugunta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • An Fallasa Tushen Mugunta!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • “Kada Ku Sāka Ma Kowane Mutum Mugunta Da Mugunta”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Cikakken Sani Game da Allah na Yi Mana Ta’aziyya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 6/1 p. 3

Za a Iya Kawar da Mugunta Kuwa?

Wani ɗan ƙaramin yaro ya tsinci wani abu a wani fili, wato, bom da ake binnewa a ƙasa, kuma ya makance ya naƙasa. Wata uwa ta jefar da jaririnta, ta ajiye shi a cikin shara a gefen hanya. Wani ma’aikaci da aka kore shi daga wajen aikinsa ya koma wajen ya harbi dukan mutanen da ya gani kuma ya kashe kansa. Wani ɗan ƙasa da ake ba wa daraja ya yi lalata da yara.

ABIN baƙin ciki ne cewa irin waɗannan rahotonni na miyagun ayyuka ya zama ruwan dare a zamaninmu. Mafi muni ma, sau da yawa an fi ba da rahoto na kisan ƙare dangi, da ta’adanci. “Wannan ƙarni na 20 na Shaiɗan ne,” in ji wani labari da aka wallafa a shekara ta 1995. “Ba lokacin da mutane suka nuna iyawa sosai da son kashe mutane da yawa don ƙabilanci, addini ko rukunoninsu kamar a wannan zamanin.”

Sa’an nan, ’yan adam suna gurɓata iska, ɓata duniya, ƙarar da arzikin ƙasa, da kuma kashe dabbobi da yawa. ’Yan adam za su iya daina dukan waɗannan mugunta kuma su mai da duniya ta zama wurin zama mafi kyau? Ko kuwa ƙoƙarin yin hakan zai yi kama da canja yanayin ne? Wani farfesa da ya yi rubutu sosai a kan batun mugunta ya ce: “Ina da bukata na gaggawa don in kawo canji na musamman a duniya, in kuma kyautata duniya. Amma duniya ba ta gyaruwa.” Wataƙila kai ma kana jin haka.

Ana iya kamanta inda duniya ta nufa da jirgin ruwa da ke tafiya cikin teku da haɗarinta yake ƙaruwa kowace rana. Duk da cewa babu wanda yake so ya bi wannan hanyar, amma dukan ƙoƙarce-ƙoƙarce da aka yi don a canja yanayin ya kasa. Jirgin ya ci gaba da tafiya har ya faɗa cikin haɗarin da ba za a iya hanawa ba.

Za a iya cewa ajizancin ’yan adam ne ke sa wannan duniya tana daɗa suƙunƙucewa. (Romawa 3:23) Duk da haka mugunta ta yi yawa sosai, kuma tana wuce gona da iri da ya nuna cewa matsalar ba daga ’yan adam kaɗai ba ne. Yana yiwuwa a ce wani iko ne da ba a gani amma mai ƙarfi ne yake ja-gorar ’yan adam? Idan haka ne, wanene kuma yaya za mu iya kāre kanmu? Talifi na gaba zai amsa waɗannan tambayoyin.

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 3]

© Hotunan Heldur Netocny/Panos

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba