Matasa Halinku na Shafan Iyayenku
“BA NI da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji labarin ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya,” in ji manzo Yohanna tsoho. (3 Yohanna 4) Ko da yake yaran da aka ambata a cikin wannan ayar ta Littafi Mai Tsarki yana nuni ne ga almajirai Kiristoci, iyaye masu tsoron Allah za su fahimci wannan furcin da Yohanna ya yi. Yadda iyaye suke shafar rayuwar yaransu a hanya mai kyau, hakazalika, yara suna shafar rayuwar iyayensu sosai.
Sarki Sulemanu na Isra’ila ya bayyana yadda yara za su iya shafan iyayensu. Ya ce: “Ɗa mai-hikima yana faranta zuciyar ubansa: Amma jahilin ɗa yana nawaita zuciyar uwatasa.” (Misalai 10:1) Saboda haka, ya kamata dukan yara har da manya, su yi tunanin yadda abubuwan da suke yi zai shafi babansu da mamarsu. Me ya sa hakan yake da muhimmanci?
Ka yi tunanin irin kular da iyayenka masu tsoron Allah suka yi maka har ka girma! Sun soma kula da kuma yi maka addu’a tun kafin su haife ka. Bayan sun haife ka, sun so ka sosai kuma ƙila sun yi wa Allah godiya domin gata mai muhimmanci da ya ba su da kuma hakkin kula da yara. Sun haifi ɗan jaririn da ba zai iya yin komi ba don su kula da shi, kuma sun ɗauki hakan da muhimmanci da yake su masu bauta wa Jehobah ne.
Tun da iyayenka Kiristoci ne na gaskiya, suna karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littafin da ke bisa Littafi Mai Tsarki don neman ja-gora, kuma sun nemi shawara daga wurin waɗanda suka yi renon yara. Suna kuma ci gaba da faɗin damuwarsu a addu’a ga Allah. (Alƙalawa 13:8) Sa’ad da kake girma, iyayenka sun san halayenka masu kyau da kuma kurakuranka. (Ayuba 1:5) Ka fuskanci wasu matsaloli a lokacin da ka isa shekarunka na goma sha. A wasu lokatai, wataƙila ka yi rashin biyayya, kuma iyayenka suka ƙara yin addu’a, suka ƙara yin bincike, kuma suka ci gaba da yin tunani a kan yadda za su taimaka maka ka ci gaba da bauta wa Ubanka na samaniya, Jehobah.
Iyayenka sun ci gaba da zama baba da mamarka. Ko da ka girma, suna ci gaba da kula da lafiyarka, tunaninka, motsin ranka, da kuma ruhaniyarka. A duk waɗannan lokatai, iyayenka sun san cewa kana da ikon yin zaɓinka, kuma ba su san yadda rayuwarka za ta zama ba. A ƙarshe, kai ne za ka zaɓa wa kanka irin tafarkin rayuwa da za ka bi.
Kana ganin bai dace ba a ce babu “wani farinciki wanda ya fi wannan” iyaye su ji cewa yaransu “suna tafiya cikin gaskiya,” kuma idan suka ƙi iyayensu za su yi baƙin ciki? Babu shakka, yaran da suka yi abin da bai dace ba suna jawo wa iyayensu baƙin ciki. Sulemanu ya ce: “Ɗa marar-wayo abin ɓacin rai ne ga ubansa, Ɗaci ne kuma ga wadda ta haife shi.” (Misalai 17:25) Iyaye suna baƙin ciki sosai sa’ad da wani ko wata daga cikin ’ya’yansu ya ko ta daina bauta wa Allah na gaskiya!
Babu shakka, matasa suna da tasiri sosai a cikin iyali da kuma a waje. Halinku na shafan iyayenku sosai. Idan kuka juya wa Allah da mizanansa baya, iyayenku za su sha wahala. Amma, idan kuka kasance da aminci kuma kuka yi biyayya ga Jehobah, iyayenku za su ji daɗi. Ku ƙudurta cewa za ku sa iyayenku su yi farin ciki! Wace irin kyauta mai tamani ce za ku ba waɗanda suka yi renonku, suka kāre ku, kuma suka ƙaunace ku da ta wuce wannan?