Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 1/1 pp. 17-21
  • ‘Jehobah Za Ya Rama Masu’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Jehobah Za Ya Rama Masu’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gargaɗi ga Waɗanda Suke Raye Sa’anda “Ɗan Mutum Za Ya Zo”
  • Ya Kamata a “Riƙa Yin Addu’a”
  • “Ka Rama Mani”
  • “Za Ya Rama Masu”
  • ‘Za Ya Sami Wannan Imani Bisa Duniya?’
  • “Dukan Hanyoyinsa Gaskiya Ne”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Yesu “Ya Kafa Yin Gaskiya a Duniya”
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Ka Yi Adalci” Wajen Tafiya da Allah
    Ka Kusaci Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 1/1 pp. 17-21

‘Jehobah Za Ya Rama Masu’

“Allah fa ba za ya rama ma zaɓaɓunsa ba, da suke yi masa kuka dare da rana?”—LUKA 18:7.

1. Su wanene suke ƙarfafa ka, kuma me ya sa?

A DUKAN duniya Shaidun Jehobah suna more cuɗanya da Kiristoci maza da mata da suka bauta wa Jehobah cikin aminci shekaru da yawa. Ka san wasu daga cikin waɗannan? Wataƙila ka tuna da wata ’yar’uwa tsohuwa da ta yi baftisma shekaru da yawa da suka wuce kuma ba ta fasa zuwa taro a Majami’ar Mulki ba. Ko kuwa ka tuna da wani ɗan’uwa tsoho wanda yake tallafa wa shirin ikilisiya na fita hidima kowane mako, kuma ya yi haka shekaru da yawa. Hakika, yawancin waɗannan amintattu sun yi zato cewa warhaka, Armageddon ta riga ta faru. Duk da haka, ci gaban wannan duniya marar adalci bai sa tabbacinsu game da alkawarin Jehobah ko kuwa ƙudurinsu na “jimre har matuƙa” ya yi sanyi ba. (Matta 24:13) Irin wannan bangaskiya mai ƙarfi da waɗannan bayin Jehobah masu aminci suka nuna yana ƙarfafa duka ikilisiya.—Zabura 147:11.

2. Wane yanayi ne yake sa mu baƙin ciki?

2 A wani lokaci, za mu lura da wani hali dabam. Waɗansu Shaidu sun yi hidima na shekaru da yawa, amma da wucewar lokaci bangaskiyarsu ga Jehobah ta yi sanyi, kuma suka daina tarayya da ikilisiyar Kirista. Muna baƙin ciki idan waɗanda muke tarayya da su a dā suka bar Jehobah, kuma muna son mu ci gaba da taimakon kowane “ɓatacciyar tunkiya” ta komo ga garken. (Zabura 119:176; Romawa 15:1) Wannan yanayi ya jawo tambayoyi. Menene ya sa Shaidu da yawa suka ci gaba da bin bangaskiyarsu ga alkawarin Jehobah, amma wasu sun daina bi? Menene ya kamata mu yi don mu ci gaba da kasancewa da tabbaci cewa “babbar ranar Ubangiji” za ta zo? (Zephaniah 1:14) Bari mu tattauna wani kwatanci da ke cikin Linjilar Luka.

Gargaɗi ga Waɗanda Suke Raye Sa’anda “Ɗan Mutum Za Ya Zo”

3. Su wanene za su amfana daga kwatanci na gwauruwa da alƙali, kuma me ya sa?

3 A Luka sura 18, mun ga kwatancin da Yesu ya yi game da gwauruwa da wani alƙali. Yana kama da kwatanci na mai masauki da ya riƙa nacewa, da muka tattauna a talifin da ya gabata. (Luka 11:5-13) Amma, waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki da suke ɗauke da kwatanci na gwauruwa da alƙali sun nuna musamman cewa wannan ya shafi waɗanda suke raye “sa’anda Ɗan mutum ya zo” a ikon Mulki, wanda ya fara a shekara ta 1914.—Luka 18:8.a

4. Menene Yesu ya tattauna kafin ya nanata kwatancin da ke cikin Luka sura 18?

4 Kafin ya ba da kwatancin gwauruwa da alƙali, Yesu ya ce za a fahimci alamar zuwansa a cikin ikon Mulki “kamar yadda walƙiya” da ke “walkatawa daga wajen wani sashen sama, tana haskakawa har zuwa wancan sashen sama.” (Luka 17:24; 21:10, 29-33) Duk da haka, yawancin mutane da suke rayuwa a “kwanakin ƙarshe” ba za su saurari wannan tabbacin ba. (Daniel 12:4) Me ya sa? Domin irin dalilin da ya sa mutanen zamanin Nuhu da Lutu suka yi banza da gargaɗin Jehobah. A lokacin, mutane ‘suna ci, suna sha, suna saye, suna sayarwa, suna dashe, suna gini har ranar da aka hallaka su.’ (Luka 17:26-29) Sun rasa ransu saboda sun shagala a ayyukansu, ba su saurari nufin Allah ba. (Matta 24:39) A yau, mutane sun shagala da ayyukansu na yau da kullum, sun kasa fahimtar cewa ƙarshen wannan duniya marar ibada ta kusa.—Luka 17:30.

5. (a) Su wanene Yesu ya yi wa gargaɗi, kuma me ya sa? (b) Menene ya sa waɗansu suka yi rashin bangaskiyarsu?

5 Hakika, Yesu ya damu cewa wannan duniyar Shaiɗan na iya rinjayar hankalin mabiyansa, har ta sa su ‘koma gidan’ jiya. (Luka 17:22, 31) Hakika, wannan ya shafi waɗansu Kiristoci. Shekaru da yawa waɗannan suna marmarin su ga ranar da Jehobah zai hallaka wannan muguwar duniya. Amma, sun yi sanyin gwiwa domin Armageddon bai zo ba a lokacin da suke sa rai. Tabbacinsu na zuwan ranar hukunci na Jehobah ya yi sanyi. Sun yi sanyi a hidimarsu kuma a hankali suka sa hannu a neman abin duniya, sai suka yi sanyi a ayyukansu na ruhaniya. (Luka 8:11, 13, 14) Da shigewar lokaci sun ‘koma gidan’ jiya, wannan abin baƙin ciki ne!

Ya Kamata a “Riƙa Yin Addu’a”

6-8. (a) Ka ba da kwatancin gwauruwa da na alƙali. (b) Ta yaya ne Yesu ya ba da ma’anar wannan kwatanci?

6 Menene ya kamata mu yi don mu tabbata cewa tabbacinmu a cikar alkawarin Jehobah bai yi sanyi ba? (Ibraniyawa 3:14) Yesu ya amsa wannan tambayar bayan da ya gargaɗi almajiransa kada su koma wa muguwar duniya ta Shaiɗan.

7 Luka ya ce Yesu ya yi “musu misali da nufin ya kamata a riƙa yin addu’a, kada a suma.” Yesu ya ce: “A cikin wani birni akwai wani alƙali wanda ba shi da tsoron Allah ba, ba ya kuwa kula da mutum ba: a cikin wannan birni kuma akwai wata gwamruwa; ta kan riƙa zuwa wurinsa, tana cewa, Ka rama mani bisa ga maƙiyina. Sai da ya jima tukuna, yana ƙi: amma daga bisani cikin ransa ya ce, ko da shi ke ba na tsoron Allah ba, ban kuwa kula da mutum ba; duka da haka, domin macen nan gwamruwa tana damuna, sai in rama mata, kada ta ja raina da zuwanta yau da gobe.”

8 Bayan da ya ba da wannan misalin, Yesu ya faɗi ma’anar: “Ku ji abin da alƙalin nan mara-adilci ya ce. Allah fa ba za ya rama ma zaɓaɓunsa ba, da suke yi masa kuka dare da rana, yana kuwa da yawan haƙuri bisa garesu? Ina ce maku, Da sauri za ya rama masu. Duk da wannan sa’anda Ɗan mutum ya zo, za ya sami imani bisa duniya?”—Luka 18:1-9.

“Ka Rama Mani”

9. Wane jigo ne yake a bayyane sarai a kwatancin gwauruwa da alƙali?

9 Jigon wannan kwatancin a bayyane yake sarai. Yesu ya ambata abubuwa da waɗanda suke cikin wannan kwatanci suka yi. Gwauruwar ta yi roƙo: “Ka rama mani.” Alƙalin ya ce: “Sai in rama mata.” Yesu ya yi tambaya: ‘Allah ba za ya rama ba?’ Yesu ya ce game da Jehobah: “Da sauri za ya rama masu.” (Luka 18:3, 5, 7, 8) Yaushe ne ainihi Allah zai “rama masu”?

10. (a) Yaushe ne aka rama wa mutanen Allah a ƙarni na farko? (b) Yaushe ne kuma ta yaya za a rama wa bayin Allah a yau?

10 A ƙarni na farko, “kwanaki na ramawa” ya soma ne a shekara ta 70 K.Z., sa’ad da aka hallaka Urushalima da haikalinta. (Luka 21:22) A yau za a rama wa mutanen Allah a “Babbar ranar Ubangiji.” (Zephaniah 1:14; Matta 24:21) A wannan lokacin, Jehobah zai “sāka ma waɗanda ke ƙuntata” wa mutanensa sa’ad da “[Yesu yake] ɗaukan ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.”—2 Tassalunikawa 1:6-8; Romawa 12:19.

11. Ta wace hanya ce za a yi ramako “da sauri”?

11 Ta yaya, ya kamata mu fahimci tabbacin Yesu cewa Jehobah zai rama wa bayinsa “da sauri”? Kalmar Allah ta nuna cewa ko da “yake [Jehobah] yana da yawan haƙuri,” zai rama wa bayinsa nan da nan idan lokacin ya kai. (Luka 18:7, 8; 2 Bitrus 3:9, 10) A zamanin Nuhu, sa’ad da rigyawar ta soma, ba da ɓata lokaci ba aka hallaka mugayen mutane. Hakazalika, a zamanin Lutu, an halaka mugayen mutane sa’ad da wuta ta sauƙo daga sama. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan misali za ya faru kuma cikin rana da Ɗan mutum za ya bayanu.” (Luka 17:27-30) Haka kuma, mugayen mutane za su fuskanci “halaka farat.” (1 Tassalunikawa 5:2, 3) Hakika, mu tabbata cewa Jehobah ba zai bar duniyar Shaiɗan ta ci gaba fiye da yadda shari’a take bukata ba.

“Za Ya Rama Masu”

12, 13. (a) Wane darassi ne game da Allah kwatancin Yesu na gwauruwa da alƙali ya ƙunsa? (b) Me ya sa ya kamata mu tabbata cewa Jehobah zai saurari addu’o’inmu ya kuma rama mana?

12 Kwatancin Yesu game da gwauruwa da alƙali ya nanata wasu abubuwa masu muhimmanci. Ta wurin faɗin amfanin kwatancin, Yesu ya ce: “Ku ji abin da alƙali nan mara-adilci ya ce. Allah fa ba za ya rama ma zaɓaɓunsa ba?” Hakika, ba wai Yesu yana kwatanta Jehobah da alƙalin ba ne, kamar dai Allah zai bi da mabiyansa yadda alƙalin ya bi da gwauruwar. Maimakon haka, Yesu ya koya wa mabiyansa darassi game da Jehobah sa’ad da ya nanata bambancin da ke tsakanin alƙalin da Allah. A waɗanne hanyoyi ne suka bambanta?

13 Alƙali na kwatancin Yesu mutum ne “mara-adilci,” amma “Allah mai-shari’a mai-adilci ne.” (Zabura 7:11; 33:5) Alƙalin ba ya ƙaunar gwauruwar ko kaɗan, amma Jehobah yana ƙaunar dukan mutane. (2 Labarbaru 6:29, 30) Alƙalin ba ya so ya taimaki gwauruwar, amma Jehobah yana so ya taimaki waɗanda suke bauta masa. (Ishaya 30:18, 19) Menene darassin? Idan har alƙali marar adalci ya saurari roƙon gwauruwar ya kuma rama mata, Jehobah zai saurari addu’o’in mutanensa ya kuma rama masu.—Misalai 15:29.

14. Me ya sa bai kamata mu yi rashin bangaskiya game da zuwan ranar hukunci na Allah ba?

14 Saboda haka, waɗanda suka yi rashin bangaskiya game da babbar ranar Allah na hukunci sun yi kuskure mai tsanani. Me ya sa? Saboda sun yi watsi da zuwan “babbar ranar Ubangiji,” da haka, suna shakka, ko Jehobah zai iya cika alkawarinsa. Amma babu wanda ya cancanta ya yi shakkar amincin Allah. (Ayuba 9:12) Tambaya mai muhimmanci da ya kamata mu yi ita ce, Za mu kasance da aminci kuwa? Wannan tambayar ne Yesu ya yi a ƙarshen kwatancin gwauruwa da alƙali.

‘Za Ya Sami Wannan Imani Bisa Duniya?’

15. (a) Wace tambaya ce Yesu ya yi, kuma me ya sa? (b) Menene ya kamata mu tambayi kanmu?

15 Yesu ya yi tambaya mai muhimmanci: “Sa’anda Ɗan mutum ya zo, za ya sami [wannan] imani bisa duniya?” (Luka 18:8, NW ) Furcin “wannan imani” yana nufin cewa ba kowane irin imani ba ne Yesu yake magana a kai ba, amma yana nuni ne ga irin imanin da gwauruwa take da shi. Yesu bai amsa tambayarsa ba. Ya yi tambayar ne saboda almajiransa su yi tunani bisa ga irin imanin da suke da shi. Imaninsu ya soma sanyi ne, da zai sa su koma ga abubuwan da suka bari? Ko kuma suna da irin bangaskiyar da gwauruwa take da shi? A yau, ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Wace irin bangaskiya ce “Ɗan mutum” zai samu a zuciyata?’

16. Wace irin bangaskiya ce gwauruwar take da shi?

16 Idan muna son Jehobah ya rama mana, ya kamata mu bi misalin wannan gwauruwar. Wace irin bangaskiya ce take da shi? Ta nuna bangaskiyarta sa’ad da ta nace “ta kan riƙa zuwa wurin [alƙali], tana cewa, ‘Ka rama mani.’ ” Idan har gwauruwar nan ta nace don mutum marar adalci ya rama mata, ya kamata bayin Allah a yau su tabbata cewa Jehobah zai rama masu, ko idan ya ɗauki lokaci fiye da yadda suke zato. Bugu da ƙari, sun nuna tabbacinsu a alkawarin Allah ta wurin nacewa a addu’o’i, da yin ‘kuka ga Jehobah dare da rana.’ (Luka 18:7) Hakika, idan Kirista ya daina yin addu’a domin a rama masa, zai nuna ya yi rashin tabbaci cewa Jehobah zai ɗauki mataki domin bayinsa.

17. Waɗanne dalilai ne muke da su don mu yi addu’a da nacewa kuma mu riƙe bangaskiyarmu bisa ga zuwan ranar hukunci na Jehobah?

17 Ainihin yanayin wannan gwauruwa ya nuna mana cewa muna da ƙarin dalilai na nacewa a yin addu’a. Ka yi la’akari da wasu bambancin da ke tsakanin yanayinta da namu. Gwauruwar ta ci gaba da zuwa wurin alƙalin ko da yake babu wanda ya ƙarfafata ta yi hakan, amma Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu “lizima cikin addu’a.” (Romawa 12:12) Gwauruwar ba ta tabbata ko za a biya mata bukatarta ba, amma Jehobah ya ba mu tabbaci cewa zai rama mana. Ta wurin annabinsa, Jehobah ya ce: “Ko ta jima, dakanta mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.” (Habakkuk 2:3; Zabura 97:10) Gwauruwar ba ta da wanda zai taimake ta roƙo, amma muna da babban mataimaki, Yesu, “yana hannun dama na Allah, yana yin roƙo kuma sabili da mu.” (Romawa 8:34; Ibraniyawa 7:25) Hakika, idan har duk da matsalar da gwauruwar take ciki, ta ci gaba da roƙon alƙalin da begen cewa zai rama mata, mai zai hana mu mu riƙe bangaskiyarmu da tabbacin cewa ranar Jehobah na hukunci za ta zo!

18. Ta yaya ne addu’a za ta ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ta taimakemu mu samu adalci?

18 Kwatancin gwauruwa ya koya mana cewa akwai nasaba tsakanin addu’a da bangaskiya kuma idan muka nace a addu’armu hakan zai sa mu kawar da abin da zai sa bangaskiyarmu ta yi sanyi. Amma, wannan ba ya nufin cewa yin addu’a shi ne maganin rashin bangaskiya ba. (Matta 6:7, 8) Idan muka yi addu’a saboda mun fahimci cewa mun dogara ga Allah, sa’annan addu’a za ta jawo mu kusa da Allah kuma ta ƙarfafa bangaskiyarmu. Tun da muna bukatar bangaskiya don mu tsira, shi ya sa Yesu ya ga ya dace ya ƙarfafa almajiransa cewa “ya kamata a riƙa yin addu’a, kada a suma.” (Luka 18:1; 2 Tassalunikawa 3:13) Hakika, zuwan “babbar ranar Jehobah” bai dangana ga addu’o’inmu ba, zai zo ko mun yi addu’a ko ba mu yi ba. Amma idan za mu sami adalci kuma mu tsira daga yaƙin Allah ya dangana ga bangaskiyarmu da kuma addu’ar da muke yi.

19. Ta yaya za mu nuna cewa mun tabbata Allah zai “rama masu”?

19 Idan mun tuna, Yesu ya yi tambaya: “Sa’anda Ɗan mutum ya zo, za ya sami imani bisa duniya?” Menene amsar wannan tambayar mai ban sha’awa? Muna farin ciki cewa bayin Jehobah da yawa masu aminci a duka duniya a yau suna nuna cewa sun yi na’am da tambayar da Yesu ya yi ta wurin addu’o’insu, haƙuri, da kuma nacewa. Hakika, duk da rashin adalci da duniyar Shaiɗan take jawo mana, mun tabbata cewa Allah “za ya rama ma zaɓaɓunsa.”

[Hasiya]

a Don ka fahimci muhimmancin wannan kwatancin, don Allah ka karanta Luka 17:22-33. Ka lura da yadda misalin “Ɗan mutum” a Luka 17:22, 24, 30 ya ba mu ƙarin bayani da zai taimake mu mu amsa tambayar da ke cikin Luka 18:8.

Ka Tuna?

• Menene ya sa waɗansu Kiristoci suka rasa bangaskiyarsu?

• Me ya sa muke da tabbatacciyar bangaskiya a zuwan ranar hukunci na Jehobah?

• Wane dalili ne muke da shi don mu nace a addu’a?

• Ta yaya ne nacewa a addu’a zai taimaka mana mu guje wa yin rashin bangaskiyarmu?

[Hoto a shafi na 18]

Menene aka nanata a kwatanci na gwauruwa da alƙali?

[Hotuna a shafi na 21]

Miliyoyin mutane sun tabbata cewa Allah zai “rama masu”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba